← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 312

Sashe 96

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani tay duk bata da wani lokci me yawa da zata sallame fadila kuma babu wanda zata iya masa yardan datay wa uztaz akan case din ynxu dakema ta riga ta aiki agents akan anemo mata mahaifyr fadilan dansu fahimce juna sosai.

Umartansa tay akan daya kira mata shuaib omar suyi magana nan take yay dialing lambar snn ya mika matashi....

Daga dayan bangaren Meenal ta fito daga dakin halisan kenan tana baza takunta daya bisa kan daya daf zata sauka akan matakalar knn suka ci karo da khaleel sanye da kananan kaya da suka masa kyau da alama yau dakansa yaje gari ya siyo Abincin karyawa bai tura uztaz ba..

Idanuwanta masu cike da ruwan kishi ta tsura masa tare da Dakewa daga inda ta tsaya cak din tanamai dada kure kyakkwar fuskansa da kallo jin wani abu mai mugun zafi a zcyarta na mamayeta ahankli...

Meenal tana masifar son mijinta kodaga cikin kwayar idanunta zaka iya zakwalo hakan cikin sauki fiyeda yadda dabiunta suke nunawa kamar bata damu dashi ba kwata kwata, ita dai Son duniya da girman kai shine kawai yasaka ta kasa gane cewa tana masa wani irin nannaniyar so tare da wani irin mummunan zafin kishi akansa da ita kanta bata san tana dashi ba..

Maganganu ta kumtsa aranta tare da Kankance ido akan ledojin shoping din dake hannunsa tana kan jiranshi ya karaso ya sameta ta balbaleshi

Badan bata kaunar yay hidima wa halisa amma wnn kishi da Haushin dolene takejinshi musmn datake ganinsa yana kulawa sosai, dan tasan Inda itace tace yana ficewa da safe yana saya mata abun karyawa da bazai taba amincewa..

Aranta cewa take Tasan jinya suke da halisa and he is just doing his job amma this has to stop today tunda bazai mata ba bai isa yay ma wata ƴa macen ba.

Fuskansa babu yabo babu fallasa ya tinkarota dake yasan ba gaishesa zatay ba dan haka kallo daya yay mata yataho zai wuce ta gefenta dadddar qamshin turarensa dake binsa ya dada hatsalata da ruwan kishi, tay rau da ido cikin giggiwa da ji da kai tace "khaleeel..

Juyowa yay anitse yace "what?...

Da raini a yanayinta Tace what fa kace? Akan Baka ganni bane da zaka wuce ni kamar ka wuce banza khaleel banason irin wann abun fa..

Girarsa na sama a dage Cikin katseta yace ke nagaya maki idan baki dena min magana yadda kikaga dama ba ranki zai baci..are u mad??? Ya fada with no nonsense tune.

Yadda yay maganan da dakewa yasaka Take ta saukar da murynta kasa kasa babu shiri tahau murguda mai baki, toh gani nayi ai bamu gaisa yau ba amma Shine zaka ganni kawani dauke kanka kamar kaga kashi haba khaleel kodan abunda ya faru jiya shine zaka doramin dika lefin..

Fuskarsa ba asake ba yaja tsiririyar tsaki snn Yace .."Let it rest Amina.
Dama can Baki saba gaisheni ba so why shud i expect it frm u today kefa babu ranan da baki neman fitina dani a gidan nan.

Khaleel inde maganan expectations akeyi then i also dint expect to see u buying food in this house I tot is againts ur law...

Ya juyo da mamaki yana kallon bakinta ta what do u mean..wani law?

Tana kallon idonshi cikin yin maganan da karfi yadda su halisa zasuji tafara kakalo zantuka akan batun girki agidan da kuma siyen abinci, kai kace bakason wokers, bakason cooks agidan nan, but u shud atleast hire one for halisa's sake if not saidai fa kahada mu duka kana siyamana abincin agidan nan bangane wann cin fuskar ba.

Looking emotionless and calm yace can you Go straight to the point pls ban fahimceki ba fa..

Gaba ta turo baki tana kumbura fuska cikin sautin shagwaba tace aikasan menake nufi....
or, am i not ur responsibility too, inde zaka cigaba da hakan toh nima dolene kana siya min abincin kawai ainima nayi desrving ka kula dani..

Zai magana kenan sai ga nan halisa na saukowa tare da uztaz a bayanta suna dan sauri dan tun daga sama sukejin muryan meenal da abinda take cewa amma tayi kamr batajisu bama har zata fice waje kenan ta amshi sakonta wajen drivern zach taji meenal din na masa ihu akai..

Tsaki tay kasar wuyarta cikin ranta tace waynn kullum basa da wani aiki ne face hayaniya, Gashi babu halin komawa dan transaction report ne na duka abinda suka kashe akan harkan companynta which is a very important file shikansa zach din sai jiya yake samunshi daga hannun managern bankin sa dama kuma shika daine abunta daya rage awajenshi da bai bata ba.

Meenal din ce ta fara hangota shiyasa tunda ta katse khaleel tahau daga murya tana kawo makirci me yawa acikin zancen abincin har tana ciko ruwan hawaye a idonta dan ace itace ake zalunta

...dan ni ba patient dinka bace shiyasa Baka damu da naci ko banci ba so i shud starve ryt? Toh ka bari mana in kawo mana cook agidan i swear to u i will pay for evrythiing.

A mamakance Yake kallon yadda ta sauya kamar chameleon ta maida maganar wani babba dake shi baima lura da fitowarsu halisan ba...yace kin fara hauka ne Amina...all this while da nake siyan abinci agidan nan sai yaune abun ya fara damunki..
Toh ai ba wani abu bane in bakison asiyo sai ki fara shiga kitchen kina mata girkin...listen, duk randa kika kawo wata wai cook gidan nan ki shirya zaban ko ita ko ni..

Yana gama furta hakan sai ganan halisa sun sauko, hade ransa yay baice mata komi ba har suka kammala gaisawa da uztaz, da wani sigar makirci meenal ta fado jikin halisa tana sauke ajiyan zucya tare da matse hawayen karya dan kawai ace shine mai zafin rai din. Ganin abunda meenal takeyi awajen ya mugun dore masa kai ya tsura mata idanunshi ganin sai wani shishhigewa jikin halisan take tana kananan maganganu, yarasa me yasa ta dago da wann maganan, me kuma ya mata da har take hawaye agaban mutane, takaici ya hanashi iya tsayuwa mikawa uztaz abincin yay snn ya kama hanyar waje dan yasha iska.

Halisa ta rikota suka zauna akan chairtun bata tambayeta meya faru ba tahau complain tanamai murda maganan cikin juyashi upside down tanamai zuzzubawa halisa zancen karya

irin ta nuna cewa ai khaleel yana siyo abincin ne kawai ba dan Allah ba saidan ya horata, mene menenta..tace ai mugunta kawai yake mata dan yasan bata wani iya abinci ba shiyasa ma ya ki sam su kawo me aiki agidan, ta dinga hawaye me ban tausayi tana cewa ai threathning dinta yakeyi da zancen zai bar gidan sabida dan yaga gidan nata ne in ya bar mata itace zata damu.

As usual halisa batace mata komi ba banda rarrashinta datayi dan bazata iya sake yadda da maganan bakin meenal talba ba....

Kamar wacce take karantar zuciyar meenal din atake ta raya aranta cewa zata dena amsar abincin khaleel tunda dama ba ita ta sakashi ba...

Meenal ta gama kukan makrcintan Sun mike zasu fita waje kenan meenal tana hango khaleel tafara kakalo wata sabuwar makricin tanamai cewa halisa itafa bawai hanashi takeson yi kawo mata abu take sonyi ba she just want to be included.
Tanason mijinta ya nuna kulawarsa akanta ko da sanadiyar ciwon halisan ne...

Daga inda yake yana ji halisan tace mata Koma yaya ne yaune dama na karshe,in sha Allah she will take care of that by herself musmmn ma da abun ya soma dawowa musu sabani...

Kafin kace wani abu meenal ta sake sauya salon makricinta izuwa wani siffa ta daban..

Tay rau da ido jin halisa tace zata katse hakan, Nan take Tafara rokon halisa musmmn ma data san yanajinsu tafara daga muryanta sama sama kamar bata san tanayi ba..

Halisa pls don't say this wallh khaleel zaiy fushi dani inna jawo masa wani tsaiko akan lamarin treatment dinki...he have already told me jiya bazai dauka ba...halisa pls can u not make it any worse?
Zaiji haushi what if he decide to leave me..

Fuska ba yabo ba fallasa Halisa tace "Amina he wont.. kawai Dama dan diet routine ne yasaka in uztaz bai iso da wuri ba yake min but ure his responsibilty not me in zai baki kulawa ya baki kawai amma ba sai kinyi amfani da ni ba.

I knw i knw amma ai inkika dena karban nashi kuma kika dena cin abincin gidab nan wani abu yaje ya faru da lfyar ki wallah zaice nina jawo masa..so, why dont u just do it here by uself
Halsy, gidana fa gidanki ne, and You can use our store babu abunda bamu dashi aciki na Abinci khaleel ya siya mana komi, kuma i knw u love cooking.. wont u be happpy eating ur own food..ko ciwon naki bazai barki kiyi girki ba?
Nide wallh banason ace kina gidana kuma kina sayan abinci awaje..

Take ta marairaice fuska dana san cewa danayi khaleel ya hada dani zai jawo har kice haka da bance ba, halisa plssss dont say no to me pls pls pls...consider !

Wani abu akasar ran halisa nagaya mata cewa da biyu meenal take duk wann abun sede bata Nuna hakan akan fuskanta ba.

Okay fine ..i will think about it inna ga zan iya to..but am not promising u anything.

Cikin sassauto da murya kmr mutuniyar arziki meenal din tace okay to shikenan.. ranta yay fari fat dan tasan muddin halisa tay girki khaleel bazai taba ci ba, snn ta rabashi da fita siya mata abinci agidan kamr wata sarauniya. Wata shuumar Murmushi tay acikin ranta da tunanin ta kashe tsuntsu biyi da dutsi daya.

Agaggauce halisa tace ana jira na awaje see u latr..

Meenal tay murmushi tace okay

Dukan wani abunda suka zanta khaleel na jinsu yarasa mesa Duk sanda yaji meenal na magana da halisa Kansa sai ya daure ya kasa fahintar inda meenal din ta dosa dashi cos it alwys feeels like she is painting him red irin shine mugu din nan itace kuma me hankli..
Chapter 96 · 0% Book details