← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 185 OF 312

Sashe 185

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yadda yace mata su bude zuciyoyinsu su shinfida sabuwar cafta na rayuwar aurensu tana ganin kamar hakan ne mafita, she just smile sabida inna hajiya tasha gaya mata haka lkcin a turkey intana mata nasiha akan aurenta kamr tasan wnn lkcin zaizo, she alwys says dat her marriage is her marriage inta tsaya yin doguwr tunani akan lamarin Allah shaidan zai rinjayeta ta butulce ma niimar Allah and eida She make it or break it all is his in her decisions.

tana murmushi me sanyi Chan Ta dan daga kai ta duba agogo its almost 5.30am ta kallesa cikin ranta tana ji kamar ita kadaice mace acikin ransa da zucyarsa.. shikam Baccinsa yake hankali kwance bai ko motsawa, ta kallesa a hankali numfashi yake saukewa soo calmly fusaknsa yayi sanyi with full serenity kamar dan karamin yaro, kallon shi take har bata san time din data yi murmushi me yawa ba...

kokarin kwace kanta tayi daga jikinshi sai taji ya sake kamota cikin kasala da sanyin murya tace its morning yaa, yau baza kayi sallah ba ko ?Bai bude ido bare ya amsa ba, saketan kawai yay ya juya mata baya tasake matsowa takamosa ta dan lafe kadan a bayan sa tareda kwantar daa kanta abayansa jinta anan yasaka ya dada lumshe idonsa sosai kusan minti 3 ya dauka yanakan saita tafiyar numfashinsa daga bisani yajuyo ahankli da fuskar sa medauke da wata sassnyar murmushi yanamai fuskantarta muryansa a kasale sosai yace good morning my beautuful wify..ya fada da disasshen muryansa idonsa a kasale kamar wanda ba yanzun a bacci ya tashi ba, lumshe ido tay ta bude batace komai ba tasa hannu tadan shafa fuskansa mai cike da tsaban hasken kyau da kwarjini wani ajiyar zcya taji ya sauke mata snn ya kama hannun ta cikin salo zai yi kissing ta kwace abunta firgit ta mike tsaye tana kallonsa yana dariya, a kunyace ta turomai baki dan tasan karshen wasan marmaza ta shige wajen alwala.

..shikam kasa tashi yayi saboda bata san dan kwanciyar da tayi jikinsa jiya yasaka da kyar ya samu bacci ba sosai yake fama da fitinnanen shawa'ar ta amma baison yayishi anytime soon har sai ta sake ranta dashi sosai...

yanaa iwance cikin tunanin abunda zasuyi yau Har ta fito ta shirya Tana tada sallah yayi saurin shiga shima ya kimtsa kansa ko da ya fito ya samu har ta idar tadan kwanta nan shima ya gabatar da sallah Yayi zamansa yayi adua sosai kusan 1hr bai tashi ba har bacci ya sake tafiya da ita shima gajiyan ke damunsa ya mirgina kadan a dan gefenta tuni ya jonata wajajen 12 hasken rana dake shigowa ya daga shi.

Ya bude idonsa ahankli ganin bata gefensa yana waigawa daga can ya hangota akan chair ta tafito daga wanka kenan farin towel dore abisa kirjinta tana famar taje sumanta dake da wani irin duhu da cika da tsawo tanayi tana sauke hannunta agijiye dan tsabar cika da yawan suman yasaka she is alwys struggling tawajen kamashi ita kadai, gyaran muryansa yasaka tajuyo suka hade ido cikin sakar ma juna murmushi ta gaisheshi da sanyin murya ya amsa tare da karasowa wajenta, suman nata ya kama yana shafawa ta lumshe ido sosai yace can i?
Tagyada masa kai baice komi ba yakama suman snn ya taje mata gently ya kulla mata da ribbon ya tufkesa tsaf tana dan tayashi gyarawa har suka kammallashi tsaf snn ya shiga wankan shima dan yunwa ya fara damunsa

Kayanta ta bude zata saka taga duk sun kare daga nayau shikenan..
Tana zaune cikin tunanin yadda zatay ta tambaye sa ranar da zasu koma gida saigashi nan ya fito Daga shi sai farin towel daure akan kugunshi ganinta ahakan jikinshi ya dan basa ya zauna daf da ita Tun bata budi baki ba yajawo shping bag dinsa na jiya daya shigo dashi snn ya aje mata agabanta yace kinga na manta ashe jiya na kawo miki kayan sawa yanxu de ki shirya sai muje muci abinci mu wuce inda zamu in mun dawo zan baki wayar ki kirata sai ku gaisa, kanta akasa tace mishi toh, ya mike tsaye yana tsantsane jikin sho dats so fresh and smooth tabisa da kallo a sadade,"Pack evrything bbyna in muka fita bazamu dawo nan ba..nan ma tace toh din ahnkli, Kanta na kasa ganin yadda ya sullebe towel agabanta yana shafa mai ko ajikinshi duk takasa daga kai ta kalleshi kirjinta na bugawa da tsanani dan kamar tanitse kasa dan kunya haka ta dingaji, ba awani cikin hayyacinta ba tabude kayan taga abaya ce maroon colour da wedge shoe da side bag da komi da komi na sawanta aciki, abayar ba'a cikamai tarkacen kwalliya ba so simple and classy tasaka riga da wando ta ciki snn tay rolling kanta sanin cewa tafiya zasuyi yasa ta dan shafa powder ta saka kwalli da man baki sosai fuskan nata yay haske.

Sharp sharp ya tattara musu kayansu duka har da nata snn ya shirya kansa cikin kananan kaya casual me aji black white shirt din data kama dirinsa cass cass ya hada da sneaker black da face cap ya saka cool white eye glasses a idonsa. Satar kallonsa ta dingaji tanajin farin ciki aranta. yana tsaye daga gaban madubi yay mata hannu ta taho Suka tsaya daganan suna kallon kansu tare a taciki suna murmushi ahnkli taji hannunshi akan waist dinta tareda lafewa jikinta kadan ya dauka musu wata cute picture da wayarsa ayayinda take sakin wata iriyar smiles cikin jin kunya fuskanta bai wani nuna sosai ba amma bakramin dacewarsu hoton ya bayyana a fili ba, suna kallon pic din suna murmushi tace woww "kiss me sanyi yadora mata akai yace i am lucky ko? Dariya tay me sanyi, shima yanayi har ya kama hannunta suka fice waje lkcin cab dinsa is waiting ya bude mata tashiga ta zauna saiga wasu mutane na fitowa da kayansu ana zubawa a booth cab din yakaisu wani restaurant suka ci abinci nan ma yay mata pictures masu kyau sosai basu wani jima ba taga ankaisu filin jirgi..

Itade bata tambayesa komi ba, dan tana da kunya sosai. After like 1hr suka sauka a wata karamar gari irin nearby county din nan me tarin provincial islands na shakatawa.

Wani karamin morden village suka sauka wajen is very quiet and peaceful dadin karawa wajen gaba daya albarkatacciya ce da niimomin Allah tare da kawatatun natural enviroments masu dauke ido da furanne masu dauke idanu, gidan hutu da suka kama is not too far from the town kusa da wani haddaden island ne a tsakiyar tekun great lake of britain In banda shuke shuke da flowers babu abunda ke zagaye da su, suna isa room dinsu sallah kawai sukayi suka sha hot chokokate coffe, wani yaje sukaje inda akwai mountain swing na flowers hannunsu sarkafe sa juna yake ce mata, "i just want u relax ko nan din bai miki bane.? Ta tabe baki cikin murmusho ta juya tana kallon wajen is so beautiful kam amma abun tsoro ne ko ina yayi dan dark dark tsaban forest trees da suke rufe su but it soo soothing musmmn da shine agefenta yanxu, ta kalle sa tace "but u need it more than me..yace maybe..but i cant relaz witou u..tace i am here alwys and forever, ya mika mata hi five yana smiling dariya tayi ta bashi suka dan tafa ..ya kamo waist dinta suka karasa wajen mountains

tana yi tana kame jikinsa saboda tsoro gashi tana so ta dan daure ta sake jikinta amma ena kunya kamar ajininta yake shiko abun burgesa yake, kunyar ya zamo masa kamar wani ado ne me daraja agareta da kuma idanunsa, dan har ransa yake kallonta da cikkekn kima da mutunci.

Suna holewarsu daf ta koma bayansa ta lafe tare da chukiuyosa da hannayenta duka
tana maida numfashi....

lumshe ido yayi yana jin cool breath dinta a bayan sa suna hirarsu with each minute they spnt soyayyarsu na kara tsimuwa aransu bana wasa ba.

Rayuwa duka duka naa tafiyane da yadda ka daukesa, inhar kay hakuri ka zabar makanka sauki da kwanciyar hankli toh babu shakka shi zaka samu ,hakama inka rike gaba, fushi, bacin rai, da son daukar fansa wani abu waishi jin dadi da kwanciyar hankli bazai taba ya sameka ba.

Bayan sun gama yayi kokarin Jawo ta amma ta turje sam ta takure shi baki daya ta manne masa abaya, yana dariya yace ok fine hakanan ya hakura suka sauko atare suka kama hanya tare hannunsa acikin nata suke tafiya yana mata bayanin wajen suna hirar su me sanyi da saka nitsuwa.

Bangaren shemau kusan yau din ma ahaka ta farka da neman alhaj shafiu yau kwana ukug dagama progrm amma bata ji duriyarsa a ko ina ba. Tun abun be darata ba har tafarajin haushin shirun nasa, Evrthing is now boring msmn ma da batasan me ake ciki ba, gashi apart frm her cloth har jeweries nata duk ta kyautar da wasu, and her
acct balance is almost empty zai wuya ya ciyar da ita abinci na kwana biyu a hotel din dan me tsada sosai ta saba ci anan din dake asalin rayuwar karyan kawai ya sabar mata dashi.

Tun safe data farka ziriya kawai take frm one end to another da waya gashi tana mugun tsoron ta fita nemansa a gari duk ta rasa wa zata kira taji labarin alhaj shafiu since duk abunda takeyi bata taba ganinsa da wani aboki ko PA ba komi zai saidai waya ko drivers haka. Sosai ta soma shiga tashin hankli ta rasa nitsuwarta sam gashi yaudin ta tashi da mutuwar jiki da ciwon kai sam bata wani iya cin abinci.

Hirarsu meenal da vicky da hadiza a grp ke dan debe mata kewa dan bakaramin drama akeyi a grp din yanxu ba.

Irin silent war din nan ke going on yar kasa kasa na ciki duk na ciki amma kowa yasan da wanda yakeyi..

Kullum hadiza ta kawo musu hirar wani abu nata na cigaba shemau sai taji hawan jininta ya haura can sama sau tamanin.

babban dramar aynxu shine wanda ke gudana atsakanin halisa da meenal.
Chapter 185 · 0% Book details