← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 312

Sashe 88

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Doguwar corridor ne me yalwataccen kwayayen wuta ga wani irin sanyin Ac dake busawa..

Wajen babu motsin kowa face karar Acn Isarsu kofa ke da wuya khaleel ya juyo a nitse snn ya dubi uztaz tareda nuna masa wajen zama a wani cushion dake waje daf da kofar, yace masa su zauna anan, he will send for them in few mins.

Babu musu uztaz ya amsa masa snn ya nuna ma halisa seat ta zauna

Tana zama aka bude kofar waje, nan sai ga Dr khalid bankole ya taho yana sauri sauri daga ganinsa kasan yan gulma ne suka sanar dashi cewa Halisa ta shigo asibiti.

aiki yakeyi ya bari marmaza yazo dan yaga yaya take dan kuwa saka idon zach akan harkokin sa da kasancewarta agidan magiyinsa khaleel bakaramin takamai burki yay ba.

Khaleel harya bude kofar office din De Aseem zai shiga caraf ya hango dr khalid nata sauri yana na zuwa kuwa ya tsaya yana kallonshi daga gefe...

Halisan batama lura ba tana zaune, caraf taji mutum ya fado gabanta da wani irin rawan jiki dr khalid din ta gani ya taho yanamai rike mata hannu casually da wani irin murnan ganinta a face nashi yace hi miss Halisa...oh my god its good to see u..

Murmushin bazata tay cos His happy gesture is almost infectious, duk da takwace hannunta anashi da dan sauri amma bai hana tay masa magana da tarba me kyau ba, da dan sakin fuska sosai tace..hi DR..?
Whts that ur name again

Dariyar kirji yay ganin harta mance sunanshi Yace khalid..tace ohhh Dr khalid..wani janta yay ta mike tsaye yadan yi hugging dinta lighly yana cewa is soo good to see you pretygirl ya jiki?

Ta dan sake jikinta kadan snn Tace fine..

Wani jajjan ta Dr khalid din ya fara da wani irin dan iskan kallo yanata shishhige mata kamr zai cinyeta, wanda atake hakan yay annoying din khaleel to the core ahnkli ya firzan da zazzafar iskar dake bakinshi cikin kyabe baki ya wuce cikin office din Dr aseem kai tsaye.

Fannin vicky kuwa tun da ta kammalla waya da hadiza taji kirjinta na bugawa driving din ma a daddafe takeyinshi dan Allah Allah take ta isa office dinta ta zauna ta bude computerta danta turawa kayden sakon wasu files nata da gaggawa.

Hadiza ta gaya mata cewa thers been alot of competitions, mutane dayawa kuma na kai hari a wajen data samu, dadin karawa har da tawagar babban business rival dinta wato Mrs chimamanda onyeka chuku datake son taga bayanta a duniyar business din gaba daya.

Ata dayan bangaren kuwa dede gaban hadadden gate din pan athlantic unniversity
Hadaddun Yan mata da samari sukayi cincirondo
Tun daga gate din waje kansu nata kallon wani waje..

Vicky da already ta doso ta bakin gate da white mercedez benz dinta zata shiga sai taga student sunata kallon bayanta tun abun be darata ba harta fara tsarguwa daga bisani sai ta soma gane cewa ashe ba itadin ake kallo ba..

Wani hadadden koeniseg aqueira fancy sport car ce baka kirin irin matte black din nan daya kusa cin karo da ita tun a gate na farko aka tsaya anata kalla abayan ta, tsaki taja da tunanin cewa bazai wuce sabbin zuwan nan bane da kansu ke rawa a makaranta.

Ita haushi ma taji da motar yake jawo mata trfic duba da irin saurin datakeyi ta isa office..

Ahnkli motar ke tafiya akan titin schl duk inda ya wuce sai gayu sun ce "dammmnn" mata kuma suhau sumewar tsaye ana "wow wow" gashi tinted ce ba aganin kowaye ne aciki ba.

Wasu kywawan mata ne su ukunsu a tsaye kamar su suka kera kansu dan kyau dayan ta dafa dayan tace...

"Janis, Who ever is in that car must be the son of the president..

Ta biyun tace "No way nicole, he must be the son of a mafia.

Ta ukun tace I dont care, duk muninsa wallh saiya kulani. Cos damn he is soo wealthy duk schl din nan babu mai exotic cars kamarsa.

Hadaddun yan mata uku da ake mugun ji dasu a makrntar ke wann hirar agaban motocinsu suna tsaye daga cikin filin parking.Da karfi suke fadin hakan dan haka vicky take jiyosu tun kan ta iso..Kusan daf da gabansu tay parking Tana parking motar tan kuwa sai gashi nan ya doso yana biye da ita.

He is smooth and soo fast sabida sport car ce tunkan vicky ta gyara nata motar har cimmata
Yay kamar ma tare suka iso.

Yadda yay parking nashi motar roughly daf da nata yasaka yan matan suka karajin ya mugun burgesu.

Ran vicky ya sosu bana wasa ba amma Tsabar aji daya gama ratsa jikinta yasaka ta kame kanta bata bude motar ta fito ba tana zaune a car din tana son taga wani isashen yarinya ko Yaron ne zai Fito aciki.

Nicole dija da janis sai rawan jiki suke kowacce tana famar gyara zaman nonowarta da matsatsen bombom dinta da hair dinta ana rigima ana kar kadasu..

Kusan five mint yaci snn motar tay blinking red light kafin nan murfinta ta budu, tun daga kan kafafunsa dake sakale cikin wata grey colour balenciaga booth da ya soma dorawa akasa suke kalla har izuwa kan hadadden fuskarsa data sha gyara sajen sa ta kwanfa luf, he is tall and dark shi ba fari bane but he is god damn young and handsome, asalin yanayin samari masu jini ajika yan gata yayan masu kudin gaske kuma sakaltattu wanda ake ji dasu sosai kayden yake dashi, wani irin shiga yay ta kamala, not the boyish swag u will expect to see frm a fresh young boy kamarsa yasaka white shirt me buttoran gaban adan bude da wata grey trouser me laushi ta kamfanin calvin klein.

manyan idanunsa har maiko maiko suke idan ya juyasu wani irin Sanyin nitsuwa da kamiyarsa tamkar ya hada jini da jinin sarauta. Kominshi a nitse He is so calm and collected.

Itakanta vickyn saida ta dau lokci tanata kallon sanyin kasaitar dake tafe da yanayin kayden duk dana bayau ta soma lura da hakan ba, yaron de haushi yke bata for no reason at all cos she feel like they are connected by heart sumhow..

Janis da dija kuwa atake suka yi sumewar tsaye ajikin nicole kusan atare suke cewa wowwww.. vicky ta kalle su tana jan tsaki jin takaicin su ya shakureta.

Daga zaune tafara mita tana cewa "Henry yana bawa yaron nan dama yay yawa, why wud he let him drive these fancy cars karatu yazo yi ko burge yan mata?

Kwarjininsa da wnn Calmness dinsan da nitsuwar tasa ya hana yan matan nan zuwa jikinsa dan sam baiyi kama da irin mazajen da suka saba cin karo dasu ba.

Allah Allah vicky take ya bar wajen sabida ta fito tawuce office dinta duk takaicin su nicole yasaka ki fitowa, daga zaunen ta dan lumshe idonta da zimman tana budewa zataga basu wajen dukansu, bata sani ba Kai tsaye wajenta ya doso ya tsaya ya zuba mata mayun idonsa daga cikin glass yanata kallon lumsashen idanunta yana murmushi me sanyi jin kaunarta yana me kara huda masa zuciya.

Ko minti biyu da lumshe idon batay ba taji tsikar jikinta na tashi kamr kuma ana kwankwasa mata motarta, adan firgit ta bude ido, suna hade ido taji kirjinta ya bada sauti me karfi ganib irin kallon so karara dayake mata. Atake ta bata ranta tay kamar bata san shi ba.

Ahnkli ta sauke glass din tana hararsa snn tace ehen what is it young man? murmushi ya sauke mata me sanyi da muryansa me taushi yace."good morning..

Tace "morning.

Kai tsaye yace I have an assigment i want to summit to u ma'am.

"Tace okay. See me at the office now.. Babu tantama ya gyada kansa.

Daga nan ta bude motar ta fito qamshin turaren sa data shaka yasa taji gabanta na faduwa sosai dan irinsa ne aka turo mata kyauta daga kamfani, Gaba tay tanamai mancewa da jakarta a motar.

Daukar jakar yay ya riko mata hade da tarkacen files dinta snn ya fara binta abaya dashi duk inda suka wuce sai anjuyo ana kallonsu musmn ganin yadda yake binta da jakartan respectfully and calmy.

Office dintan kai tsaye suka shiga tana zama akan chair dinta ta dago kai ta kallesa snn ta jawo computerta tace let me see ur work...

Wayarsa ya ciro ya tura mata file ta bude ta gani daga ganin fuskarta zakasan she is so pissed and annoyed and soo unhappy da yadda taga perfomancw dinsa ahaka

atunaninta zata ga ya iya komi ne sai taga wani shirmen kawai ya turo..

After some time ta daga ido ta kallesa snn tace "what is ur name again?

Ahnkli Yace "kayden"..

Tace okay mr kayden,
Im sory to annouced to u that ure so unserious.. na baku isashen lokaci dan kuyi aikin nan amma just see ur work, This is all rubbish ..cancelled.
Nan da nan Ta danna cross akai gabaki daya.

Na baka nan zuwa kafin atashi kaje kayi solving questions din nan maza ka kawomin. Kanaji na?

Bai bata ransa da masifar datamai ba yace mata okay,..kallonshi ta dingai tana mamaki dan record dinsa na baya da aka turo musu daga kasar waje ya nuna cewa kayden is infact a genious topper in his previous studies.

Tsaki tay aranta tace Kodan daya zo nigeria zaice zai sakankance yay wasa ? I will deal with him cos dats not gonna hapen under my watch!!

harya juya zai bar wajen saikuma taga ya juyo baya, saiyanzu taga jakarta da tarkacenta a hannunsa. Koda ya aje mata batace mai komi ba ta harde ranta dan qamshin turarensa yana motsata bana wasa ba.
Chapter 88 · 0% Book details