← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 312

Sashe 16

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uztaz bai musanta masa ba hakan ba duk dama baida niyyar binsa office din sedei yanayin yadda khaleel din ya katsesa da idanuna yasakashi kawai ya bishi abaya sukaje.....
#SURAYYAHMS
08060712446 IS NOT A FREE BOOK
9️⃣▶️
#SURAYYAHMS
NOT A FREE BOOK
500 VIA 08060712446 CHATS ONLY.

Suna isa cikin offishin khaleel yy ma uztaz nuni da wajen zama akan wata lallausar couch dake cikin office din nan uztaz ya zauna bisakai a dofane yanamai sauke wata boyayyar ajiyan zuciya..

Daga ganin yanayinsa zakasan da cewa hanklinsa yadan fi kwanciya da Dr khaleeel fiyeda da Dr khalid da tun farkon haduwarsun sam hanklinsa bai kwanta akansa ba.

Satar Kallon khaleel din yake ayayinda ya bude wata sculpted locker mai kama da mini kitchen cabinet dagata ciki ya fidda wata hadaddiyar royal water flask, dark brown colour da set din cups dinsa aciki ya dauki kananan kopuna biyu daya fito dashi ya dora bisa saman cabinet din snn ya fito da sauran kayan hada shayi ya bude water flask din Batare da ya dago ba cikin sassanar muryansa mai sanyi yace masa..
"Tea or coffe?..ahankli uztaz yace tea sir. ya gyada kai snn yahau hadawa, within few minutes ya kammala ya miƙa masa shayin,Uztaz Yasaka hannu ya amsa yace thank you ahankli,

baisha ba ya rike cup din a hannunsa yay shiru kamar wanda ya bata acikin tunani har khaleel din ya kammala hada coffe nasa ya taho ya zauna kusa da kujerar dake fuskntar nasa bai motsa ba, shiru ne yadan dauka a tsakaninsu, sai can cikin gyaran murya khaleel yace bismillah mana mallam..?? Cikin sauke ajiyan zuciya uztaz Yace sunana Edress.

Khaleel yace Masha Allah. mallam Edress
"I am Khaleel khasheem.

Uztaz yace .."Im pleased to meet you sir. Cikin gyadamai kai Khaleel yay murmushi baice komi ba ya dan kai coffe dinsa baki ya kurba. Sai can ya kalle uztaz din fuskansa bayabo ba fallasa snn yace are you her family?
..kai tsaye uztaz yace no sir,...she is my boss..

Sounding suprised khaleel ya kalle sa suka dan hade ido snn yace mmmmm.. sorry i tot ure family. Uztaz baice komi ba yay murmushi. cikin sauke karamar ajiyan zucya khaleel yace karka damu zata warke amma kafin nan muna dan yin wasu tambayoyi wa mutanen da sukafi kusanci da ita sabida zai taimaka mana wajen bata taimakon daya dace.

Uztz yace eh haka dayan likitan ya gaya min a wancan asibitin. ba wata matsala u can ask me for anything inhar zai taimaka..

khaleel yanitsu yanata kallon uztaz kafin nan yace ka jima kana mata aikin ko?..Yace eh najima i think for like 15yrs..
khaleel yace wow, toh Me zaka iya cewa akan abunda tay kkrin aikatawa has she ever done it before..???? Kai tsaye uztz yace masa NO..ko acikin wasa bata taɓa tunanin zata kashe kanta ba..
....Cikin datsar numfashin sa khaleel yace "why? Bcos, i mean she have every reason to do that ko ba haka bane, dan a Farko, Her weding broke and then all the media breakdown on her. Kasan Ita mace ce, dolene tafara tunanin aikata hakan ko baka ganin hakan zai iya yuwa ata fanninta?

Uztaz yace gaskiya Bana tunanin cewa matsalar kenan, dan miss Halisa ba haka take ba she is the most emotionally strong woman ive ever knwn in my life, she will neva try to end her life bcos of a man. Kowaye shi, na fahimce abunda yasa mutane suke ganin kamar rabuwa da mijin aurentan ne matsalarta sabida bakowace mace bace zata iya daurewa, saidai mutane dayawa basu san da cewa harma ta aje abunda ya faru aranr aurenta abayan keyanta ba,..And She was moving on fine kafin nan wann abun yazo ya faru.

Ahnkli khaleel yace hmmm malam idrees u seems soo sure of ur boss. ya jinjina kansa batare da wani nuna amincewa a yanayinsa sosai ba, cikin nitsuwa yace toh ba matsala
Naji wannan...amma toh meyasa mutane dayawa suke cewa dan yay replacing dinta ne da wata yasaka ta shiga wann halin and you knw dat girl too is a model ryt? Dolene hala akwai kishi...And others think kawai kishi da frustrtion dinnne and some say is bcos of his money.

Tare da sauke ajiyar zuciya ustz yace Duk abunda ake fada a media is not her reality sir. I knw she was sad da suka rabu amma she is not frustrated to this extent, batun kudi kuma i think for a woman like her who build her self frm ashes zai wuya kudin wani ɗa namiji ya dameta,.when she left him she was recovring, infact shine yake hunting dinta daga baya.

Da mamaki Khaleel yace "he was hunting?..

uztaz ya gyada mai kai.

Shiru yay na dan wani lokci snn yace "bayan matsalarta da shi tana da wani matsalane da iyayenta ko yan uwanta ko business nata...

uztaz yace "a'a. Da dadewa ta rasa iyayenta wann duk ya wuce mata dan tun tana karama ne abun ya faru, and her business is doing fine i think i'm the best person to tell u that.

Khaleel na kkrin yin masa wani tambayar sai kawai aka bude kofar office din garas babu sallama aka wani wantsalo ciki kamar filin dambe.

kusn atare hanklinsu ya koma kofar, security suka soma gani kafin nan Meenal talba ta bangaje shi ta hantsalo ciki tana jajjan tsaki agefenta mahaifyarta ne tasha hijabi har kasa sunzo asibitin sassafe kamar ankorrosu daga gida.

Security na kkrin yi masa bayani khaleel din yace masa "its okay..darajar surkuwansa yace abarsu
kawai sai scruty ya juya ya fita..

Khaleel Baice musu komi ba ya daga ido ya kalle agogon bango ganin karfe shida da rabi na safiya abun ya basa mamaki sosai.

Tun akan maganan da su hadiza sukayi akan zach yasaka meenal bata samu sukuni aranta jiya da daren ba, Asubahin fari nayi ta zame tabaro gidan shema'u ta taho ta sako uwarta agaba don suzo asibiti wajen halisa sasaafe domin su tarusu rufe mata baki akan zach dan kar sauran kawayen suce zasu dauki fansa ko suyi bincike akansa asirinta yaje ya tono.

Sanin kanta ne koda ace hadiza maitamace kadai zatayi binciken zai iya jawowa zach ya fallasa komi bare ajega shemau wanda tasan in har suka soma bincikar sa babu abunda zai hanashi gaya musu Abubuwan data fada masa akan halisa mansa tun na kafin aure.

Shiyasa gabakidaya ta kasa samun nitsuwa aganinta dolene su riga kowa isowa ga halisa domin dakile wann babbn matsalar dake shirin bullo mata.

Mikewa tsaye khaleel yy snn Yace ma hajya nadiya ga wajen zama

..Hajya tazo ta zauna fuskrta babu alaman rahama dan haryanxu haushi lamarin halisan yake bata aranta, ji take kamr dauriyane halisan bata dashi kwata kwata shiyasa take neman ta saka yarta acikin damuwa.

Tun basu gaisa ba Meenal tazo kan uztaz tahau binshi da kallon kallon..baice mata uffan ba tajamai tsaki akai.
"Oga are u waiting for me to ask u to move out????
..kawani kame waje ka zauna harkana shan shayi? why wont halisa put her self in harm bayan tana zagaye da kazamai dolaye irinku wanda basusan muhimncin aikinsu ba mtssss bunch of useless workers,..bai mata ba ta Saka hannu t ta kwace cup din a hannunsa da karfi snn ta dangwala shi akasa. Uztaz ya miƙe tsaye yana dan kallonta

Sede kaskantaccen kallon datakemai yasaka saida ya sauke kansa can kasa ya kasa motsi

."Move out i said. Kaje ka wajjje kacigaba da aikinka na gadinta or else i wll fire u today. Ko kana ganin bazan iya bane?? Did u knw dat im closest person to halisa?u want to dare me ko .

...Ahankli uztaz yace am sorry ma. Yay sauri har zai fice kenan khaleel ya dakatar dashi rai abace yanamai cewa'...Dats very rude of you Amina. U met him here first. Kuma Magana me muhimmanci mukeyi u cant send him out like dat...

Tace oh please..Toh Dan kuna magana akan halisan shine bazai fita yabani waje ba ni sa'ar shine? Mema zai gaya maka akanta, meyasani you shud ask me am here . ni zan iya gaya maka komi da komi akanta bashi ba sabida nine nayi asalin zama da ita shi meyasani in banda zuwa aika?Daga bola ma fa ta tsinto shi,.

Cikin katseta khaleel yace okay dats enough ya isa haka.

Da wani irin cika da batsewaa ta maida mai maganan cikin jiji dakai.

'"..Khaleel dont shout at me mana..akanme zakana min tsawa agaban ire iren wayann kucakan..aiko dan idon uwata ma yaci ace ka koresa tuntuni amma dake baka san darajar....

....cikin katseta hajya nadiya tace ya isa haka Amina. We all knw ure worried akan jikin halisa bai kamata ace kina sauke fushinki akan kowa ba...

Tana magann ne tana Kallon cikin kwayar idon yarta direct danta gane wayancewar datay domin ta lura kmr jira kawai khaleel yake ta ambace uwarsa cikin maganan nata snn ya wanka mata mari agaban uwartata ganin yadda ransa already ya lalace...

Meenal na dago hakan taja bakinta tay shiru tare da turo musu baki.

Adan fixge Khaleel ya dauke kansa akanta snn ya dube uztaz cikin sassaauto da voice nashi kasa kasa yace malam edrees kadan jirani awaje pls ina zuwa.

Uztz baice komi ba ya fice yay waje Yana dan lekawa kuwa ya samu halisa harta dan kwanta tana bacci. Daga jikin madubin windon ya tsaya yanata kallon yanayinta dan sosai ta dukunkune kanta waje guda kamar wata maijin sanyi...

Khaleel ya nemi waje ya zauna, ko budan bakinsa bata barsa yay ba ta dora kafarta daya bisa daya snn tace " so meyene kake tambayarsa akan halisa .was she awake tay maka wani magana ne? Fuskarsa ba a sake ba yce "nop. Just asking dan ta hakane za'a san irin maganin da za'a bata.

Tace ohhh.. suka kalle juna da mum dinta suka kyabe baki cikin samun relive danso suke duk tsaya ya zamto suna nan awajen idan zata farka akarona na farko.

Daganan khaleel bai karace musu uffan ba ya hade ransa sosai ya jawo wani file gabansa yanata rubuce rubuce akai.

Zuba kawai meenal tafara masa hankalinta kwance kamr an kunnata sabida tasan koda su shemau sun iso securitu bazai barsu su iso cikin wajen batare da izinin khaleel ba.
Chapter 16 · 0% Book details