← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 312

Sashe 53

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yadda take tafiya a hankli kamar bazata karaso ba yasashi dauke kansa lumshe idanunsa kawai yay yana kiran Allah cikin zuciyar sa yake rokon Allah ya kawar masa da wannan yanayin daya samu kansa aciki cikin dan kankanin lokci najin feeling akanta wanda baisan ko feeling din na soyayya bane ko na burgewa .

kan table mat din room dinsa ta wuce direct ta ajiye abincin din snn ta juyo, Can tsakar kansa ya tsinkayo muryar ta mai mugun dadi da shiga jiki tana tambayar sa ko can zata kawo mishi abincin?

Ba ta ji amsar da ya ba ta ba, saboda ya yi nisa cikin wata duniya mai hasaso masa abubuwa kala-kala masu tsauri a kanta.

mikewa yay lokci daya fuskn nan nasa babu yabo babu fallasa ya ƙaraso wajen cikin yanayin tafiyar shi mai cike da nitsuwa da kuma daukar hankli.

yana karasowa wajen yaga har ta gyara mai wajen zama.

wata karamar smirk mai taushi ne ya kufce ata gefen bakinshi yana dan kirkikiran murmushi akan fuskrsa ya zauna awajen data gyara masa din cikin yanyin nitsuwa

baice uffan ba ya shiga satan kallonta yaga komin ta a nitse takeyin shi cikin yanayin kyaun tarbiya da saukakenn hali.

Shirune ya ratsa wajen ta shiga bude warmers din, wani irin dadin qamshin abincin yaji yana ratsa shi har kwakwala, gamutse da kamshin turaren jikinta daya doki ramin hancin sa game da hanashi jan kyakkwar numfashi.

cikin lumshe ido da budewa yaga wai harta fara zuba mishi abincin acikin plate. Spagehti jollof din dayaji kayan lambu yay green colour so yummy ta fara dauƙa maize_corn din dayake kai an watsa su a sama sunyi yellow yellow kamar chesse balls abincin yay matukar kyan gani serving spoon ta dauka ta deba dan daidai ta saka a plate na daban

sannan ta dauko wani ta zuba masa ferfesun naman dayaji kayan yaji tafarnuwa da spices komi dan daidai..

clean spoon ta aje mishi daidai inda zai dauka snnn ta koma ta dauko cold watar bootle da orange juice mai sanyi
..ruwan ta dan zuba masa kadan a kofi..snn ta nemi waje ta zauna awajen tana jiran shi ya gama kafin ta tashi ta tafi.

".hakan hajy binta tace mata tanayi acewarta ita matarsa ce yana da kyau tana tsayawa awajen har saiya kammala cin abincinsa, domin maza suna son matan dasuke daraja su, anasu tarbiyan ma da wuya mace zata kawo abincin snn ta bar wajen haka kawai batare da wanda ta kawo mishi abincn ya gama ci ba,

Tun data zauna agefe baice mata komi ba

a hnkli yake kai kowani spoon bakinshi,har ya gama cin abincin wanda yakecin shi a hnkli kamar bazai kai cikin sa ba,
komin shi cikin jan aji da nitsuwa yake yi hafsat din sai satan kallonsa takeyi abinka da yaranta duk sai taji yana burgeta

dan kadan ya rage abincin a plate din wnda baifi loma daya ba, snn ya ajiye spoon yay sipping ruwan sanyin kurbi daya yy snn yay hamdala, miƙewa yay yanacewa ta kawo masa juice din sa falonsa ta waje.

ganin inda yabi yasa tayi saurin tashi domin ta tattara wajen tana kaiwa kitchen dinsu ta ajiye su agaban sink ta dauki cup mai dan marufi ta zuba juice din kusan rabi aciki snn tasaka akan plate tabi inda taga ya bin dashi.

A sashen nasa private palon nasa yake anyishi da kujeru madaidata komi na wajen dan dede bamai tarkace ba.

kai tsaye ta turo kofar tagansa yana zaune kan kujera game da taƙure kafafunshi da sukaji gyaran manicure sukayi wani haske sosai akan chair din, wayarsa yake latsawa batare da ya dago kansa yaga ko waye ya shigo ba dan yasan itadin ce kawai zata shigo.

da sallama abkinta ta karaso ta ajiye juice din akan table din gaban sa tana shirin juyawa da sauri yace " hafsat ina son magana dake"

juyowa tayi kirjinta na bugawa,ganin bama kallonta yakey ba yasata ta zauna kan kujerar dake gefen shi a takure tana zama ta hade kanta da gwiuwarta jin nauyin shi ya rufeta.

Itadai daurewa takeyi tana dukkan wannn abubuwan amma harga Allah ranta acikke yake da tsinannen fargaba da tsoro.

wani shirune ya gifta wajen jin kanshi yay a mugun daure,aranshi babu abunda yake tufkawa face tunanin yadda zai fara tursasa kanshi izuwa fidda wasu magangnun dake cikin bakinshi..he mean to be soo cool nd soft with her amma wani abu nadaban kuma yakeji akantan mai balain ƙarfi wanda ya kejin aransa kamar yarinyar ce kawai take mugun burge shi.

atake xciyarshi tayi nitso cikin zullumin kalar shige mata daya dace yay gashi bayason suyi nisa bare ma aje ga batun raini yasan dai bazai iya bata matsayin na daban aransa na aure ynzu ba

itama shiru tayi da tulin tunanin sa aranta boyayyar shauki,tausayi game da son kasancewa tare dashi dayake neman ginuwa aranta Wadanda ita kanta ta kasa sanin abin da yake janyo mata hakan ko dalilin afkowar su cikin tunaninta.

wani iska mai mugun sanyi ne ya kada ya ratsa jikinsu duka atare suka lumshe idanunsu duk suna sauƙe boyayyar numfashi.

Mahmud yana bude idonshi ya kuma saukesu akan gashin kanta data kama ta ciki iska yana dan zarar tsillin gashin izuwa kan idonta, kantan yabi da kallo snn ya kyabe bakin sa ahanlkli yanamai tuna yawan gashinta daya zuba ahannunsa ranar a airpot a idanunsa daya daukota ahnnunsa.

ita kam wasa da tsohon zoben hannun ta ta shigayi zuciyanta na bugawa sosai sam taki ta dago bare ta kalleshi

kyabe bakinshi ya kuma yi ya dauke idonshi daga kallonta yana dan bin bakinta da kallo cike da dauriya yace" hajy ta sanar dake zaki fara karatu ko toh yaushe ne kikeson ke kifara karatun?

cikin sanyin murya batare da ta kallesa ba tace mishi " eh ta fada min amma bani da wani zabin lkci duk abunda suka ce shine zanyi..".

baice komi ba saida yadan ja snn yace" mene kike sha'awar karantawa toh ina saurararki ko shima baki da zabi

..kanta taji ya sara batace mishi komai ba kuma bata dago kanta ba.

sipping juice dinshi yay ahnkli snn yace mata "To shikn ni bacci nakeji.

daga nan ya tashi yay kamar zai fita gabanta ne ya fadi tuna ko tunanin makarntar datake so din bata taba yi ba, kuma dama bawai su hjya sun gaya mata komi da komi bane kawai de sunce mata zata fara karatu.

ita dai all she wants now is a peaceful life bata sako wani dogon buri aranta cos evrthing thats happening to her now feels like a privilage.

tunani tayi koma tace asata a islamiya ne kawai toh intaje bokon ma mezata karanta?her dream was to be a doctor..tana son ta zama likita dan ta cikawa mahaifinta burinsa amma sai take ganin kamar bazai yu da aka mata auren nan ba

ji tayi kamar ta rusa ihu cikin kasa tsaida tunanin ta waje daya. daf yana shirin daukar wayar sa zai bar wajen yajiyo sautin muryanta
cikin langwabar da wuyar da batasan tayi shi ba "tace..uhmmmm nifa ko gama jss banyi ba
Shiyasa ban yi tunanin komi ba

komawa wajen zamansa yay da mamaki yace ban fahimce ki ba..

kasa ta maida kanta a hankli cikin sanyin yanayi tace.."dama lokcin da zan fara ne..sai sai..
maganan ne ya toƙare mata wuya sakamakon tuno da rayuwanta datayi abaya da mahaifinta ya rasu kawunnan ta suka tozartasu suka hanata makarntar kwata kwata.

a take idanunta suka ciko da ruwan hawaye masu zafin tsiya sai kuma tayi shiru ta bata awajen.

gyara zamansa yay cikin karantar yanayin ta ahnkli cikin taushin murya yace hafsat inajinki sai me ya faru?

girgiza kan datayi araunane ne yasa maƙudan hawayen ta da suka maƙale akwayar idanunta saukowa kasa da uban yawa suna diddiga,wani tuƙikin zafi da hargagin radadi taji yana mamayar zuciyarta tuno da yadda kannen mahaifinta suka datse mata karatunta alokcin daya dace tayi, suka ruguza mata mafarkinta na zamowa babban likita suka walaknta mahafyar ta da karfin ikonsu na ubanni basuko ji tausayin su ba, suka kuma jefa rayuwarta a cikin wata mummunan qaddara ta bauta da aikace aikace agidan mutane da bazata taba iya mancewa da shi ba.

tafin hannunta ta matse akan saman idanunta sosai snn ta saki wani raunatacce kuma sassanyar kuka mai tsuma da kuma ban tausayi wanda kallo daya zaka mata kasan bada son ranta takeyin kukan ba saidan yaci karfin zuciyarta duk sadda ta tuna wahalar da mahafyarta tasha akanta sai taji ta tsane komi.

binta yay da idanun shi da sukayi rikirkicewn bazata aranshi yanajin zafin hawayen tan da yake sauƙa.

She is soo innocent and fragile.

sautin kukan nata dayake fitowa ahankli kuma araunane yake ƙarawa kirjinshi tukikin fargaba,ji yay kamar zugin sheshhkta na ratsawa harta cikin zuciyarshi da kwakwwaln shi yana konashi kamar wuta.
.
daurewa yay ya dauƙe kansa ya da tsime kamar abun bai wani darashi ba.

juice dinshi ya dauka ya dinga kurba a hankli
harta gaji da kukan tayi shiru..can dayaga ta samu nitsuwa snn ya sace kallonta da sanyin murya yace mata i just want to know how u intend to move futher kingane menake nufi..?

Hawayenta take sharewa Bata amsashi ba cikin sautin lallami yace kinga ynzu da akwai hakkinki akaina na aure, dolene in san abunda kike so domin komi ya zama mana da sauki inhar kinason karatun sai kije ko?

lkcin kanta na can kasa dan ita kadai tasan metakeji aranta ayanzu, but insha Allah ta qudira she will over come it.

ajiyar zcya ta sauƙe
snn tace "umm
ummm..nan tafara gaya masa yadda suka fara tun lkcin maahaifinta na raye sede kan ta kawo labarin izuwa ynxu har wasu sabbin hawayen sun sauko sun wanke fuskarta gaba daya suna sauka kasa kamar ana zubosu daga sama

..hannunta tasa tana famar gogewa.

wani shiruuuu yayi idanun sa na kallan gaban sa kamar ma baijin metake cewa
boyayyuyar ajiyan zciya ya sauƙe game da kkrin boye radadin abunda yakejii na tsananin jin tausayinta ata cikin zciyarshi dayaji ya mamaye ranshi yanzu..

juyowa yay yana kallonta yaga yadda ta dage tana korar hawayentan da ƙarfi amma sunki dena turtulowa,hannun shi ya cusa a aljihun wandonshi ya miƙa mata sabuwar handkchief dinsa.
Chapter 53 · 0% Book details