← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 312

Sashe 141

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ta kalle Ahmad da cute smiles tace cuties me zakuci ne?...

Da murnan su suka ce "sallah chicken and rice anty...And bobo..

Tace alryt. Ina zuwa toh.

Khaleel kam se kallonta yake kamar wani lost sheep harta bace ma ganinshi Hakama maryam suke binta da kallo..

tana bacewa suka sakosa agaba da son jin wacece wannan din?

Sai da ya mugun ja musu rai kafin ma ya gaya musu sunanta, bayan nan yaki sam ya gaya musu ita wacece sabida baisan ya zai fassara musu su gane batare da sun canko yaren dake zuciyarsa ba

Babu irin quesing din da basuyi ba amma haka yaki sam ya kulasu.

Halisa nakaiwa kitchen ta kunna four head na gas dan girkinta yay sauri

kafin wani 40 mints me kyau har ta tsara fried rice me cike da kayan su karas green beans green prpr da neatly sliced liver ta zuba a warmers, tay hadadden ppr chicken da babbaan one and half broiler chicken, Hade da samosas guda takwas da cup cake guda shida, datay kadan akan faranti snn tazo ta jera musu akan dinning da drink, da cup of milk na yara, snn ta karaso falon tace musu suzo ta gama.

Banda kallon kallo babu abunda ke wanzuwa tsakaninsu su ukun..

yaran ne suka fara gaba ssn khaleel ya tashi ya bisu izuwa kan table din

aka bar Aliyu da maryam dashan mamaki dan sai abun ya musu kamar a mafarki yau gasu nan dai sunzo gidan khaleel an karbe su hannu biyu agidan koda shike dama angaya musu cewa meenal bata nan dan haka ne ma sukadan sake ransu game da zuwan.

Satar kallonta khaleel yake amma ko sau daya bata kalleshi ba .

Haka tayi serving din kowa bandashi tagama da sauri ta juya zata bar wajen maryam tace "Halisa?? Da mamakin jin sunanta a bakinta ta juyo ta kalle maryam din sai taga tana murmushi wani irin mugun kama da khaleel din take mata har na fitan hankli, tace bismillah mana ina zakije kuma?

..fuska ba yabo ba fallasa tace no thanks i am okay...i wll just be in my room if u need anything.

nan da nan Aliyu ya juyo ya zuba mata kyawawan idanunsa, hannu taga ya mika mata snn yace" ni sunana Aliyu hasheem,.

Halisa tayi murmushi ta mika mai hannunta slighty snn tace nice meting u Aliyu.

Kin sake mata hannun yay yana binta da charming looks dinsa dannkuwa ta masa kyaune na fitar hankli.

yace pls have a seat..Sit down mana..Inba haka ba bazamu ci bafa

Maryam tace kamar ka sani..

babu musu halisa taja chair ta zauna, maryam tayi saurin serving dinta abincin amma kadan kadan take ci sabida kunyar idanun su duba da cewa dukan su idanunsa nakanta ne.

Hirarsu suke me shegen ban dariya, aciki ta gane cewa maryam twin sis din khaleel ce sai abun be wani bata mamaki sosai ba.

Kusan ma attitude dinsu dayane dan indirectly take mashi magana akan issure din family musmn nasu da dad dinsa yana amsata daddaya inbaka fahince shi zaka dauka tsabar girman kaine yay masa yawa da son girma.

Daga yadda kowa kecin abincin za kasan girkin tayi dadi yara yaran har labarin santi suke ma halisa duk dama yau suka soma ganin ta arayuwarsu.

..Hira aliyu suke jefowa tsakanin su suna dan yima halisa tambyoyi akan yadda akayi ta iya girki me dadi kuma adan kanknin lokci ganinta ajebo jiki duk madara sunata tsokanan junansu sunata dariya.

Kafin kace wani abu har sun dan jawota cikin surutunsu shide khaleel baiya tsoma musu baki

Maryam is totally and deeply mesmerized da kyaun halisa da kuma saukin kanta sede halisan ce akwaita da zurfin ciki da jan aji me sanyi.

nan Maryam ta fara gaya mata yadda ta taso a maiduguiri wajen kakansu da yadda ta tsani girki, har aka fara tursata koyan abinci da yake mata matukar wuya da yadda aka kashe dunbin kudade wajen kaita wajejen koyan girki da kyar harta zo ta iya,

Hirar sosai ya dago ma halisa tunanin yadda ita tafara koyan nata girkin a hannun mama grace acikin azaba da duka da cin mutunci da kunci ana ruwa ko iska tun bata mallake hanklin kanta ba

total opposite of what maryam went tru, it seems like cikin gata da soyayya kowa yay yarintarsa ita kam duk batasan wann ba.

Ahnkli tunanin past dinta yasoma dawowa mata kanta sai taji kirjinta na mata ciwo taciki cos he neva had a family time in her life batasan ma dadin iyaye ba bare kuma yan uwan jini.

Itako maryam ta gama daukawa yadda taga kyau, hutu da dukiya ya ratsa fata da jikin halisa atunaninta halisan yar wani biloniyace ma azaune.

Abun ma mamaki ya basu dasuka ga ta kwara ce haka a iya girki so she tot they maybe sum kind of special labari behind it
tanason halisa ta basu labari kodan taji wani catering schl taje a kasar waje.

yanayin yadda halisa take murmushi tana doje wasu talks din yasaka khaleel yay saurin katse hirar me gabaki daya tare da janye hanklinsu da wata maganan na daban, ai kuwa yana yin haka Halisa tay excusing dinsu ta haura sama dan bataso a dawo da hiran akwai abubuwan da inta tuna har ji take kamar zatay hawaye.

Tun bata gama wucewa sama ba tajiyo muryansa tun daga step yana ce musu time up suje gida zai fita sai gobe zaizo gidan ya samesu suyi hira.

Batasan meyasa ya koresu ba, amma hakan dayay sai ya bata mugun haushi, aganinta shine dai kawai baison jan su ajiki, tanaji maryam tana mita cikin masifa haba khaleel kaifa dama badama azo gidanka sai ka kore mutane, muma maganin mayu da mukace dai munzo maka yawon sallah. Aliyu mu tafi kaji,.. atleast we r lucky today har mun samu miss strnger an karbe da mutunci.

Halisa na karsa shiga room dinta ta fada kan gado hade da tuna baqin cikin Mama g data tuno yasata ta kwanta akan gadon nata rungume da filo tana sauke hawaye masu sanyi sosai....

Har waje ya rakasu tare da bawa yara yaran goron sallah yana dawowa cikin gidan ya hau tattara inda suka ci abincin yakai kitchen snn ya wanke hannunsa bai tsaya ko ina ba sai kofar dakin halisan
....THANK YOU ALL FOR THE COMENTS AND LOVE....❤️❤️❤️❤️

Ayanayin ruf da ciki take kwance zafafan Silent tears masu tsananin sanyi tare da karsashi ke saukowa ahankli daga cikin rufaffun idanuwan ta data lumshesu tareda tantamesu da wani irin shaukakiyar karfi wanda kallo daya zaka mata kasan cewa rayuwarta na yarinta kawai take kkrin tunawa sosai ta Tantame pillown bisa kirjinta hannunta yanamai yamutsashi cikin nisan tunani she just want to rember if she had any good memry at all, sai da tay nisa cikin tunani kafin nan fuskan iyayenta ya soma mata yawo cikin idanunta da kwakwalwar ta, shekaru shida izuwa bakwai kawai tay dasu, awan lkcin bata taba tsamnin rayuwarta zai kasance a yadda ya kasance bayan ransu ba.

Dan kuwa Bata taba ganin mutum me yawan ilimi da sanyin zuciya kmr mahaifnta ba, snn duk duniya babu abunda yafi kauna aransa kamar ita, lkcin dayake shan giyan ma tana karama amma batasan cewa giya yake sha ba sabida baya cutar dasu saidai ya bugu ya dawo cikin dare snn ya kwanta bacci shi baya aikin komi, yawanci saidai taga mahaifyarta tana wahalar kulawa da komi nasu, kuma basu taba yin wata cacar baki ko fada ba duk dama yawanci takan gansu cikin kunci da damuwa.

Baban nata ke taje mata kanta duk sanda zataje schl,zai kaita snn ya jira a bakin kofar schl din har atashi snn su dawo gida tare.

mamanta ke neman musu kudi da abinci da duk sauran abubuwan da suke bukata, ita ahaka kawai tasan rayuwarsu yana tafiya batare da wani hatsaniya ba face saida mahaifinta ya rasu
da mota ya bugeshi.

sun shiga wani hali,dan Da can ko taje suman kanta bata iyayi batare da tatuno irin soyayyar dayake nuna mata ba hakama intaje schl ta dinga kallon inda yake zama yana jiranta kenan
wani bin Haka zata zauna a wajen tun safe tay ta kuka har atashi da tunanin ko zai dawo ya dauketa

maman ta tazo tafara ciwo, tun alkcin gatan ta ya kare kwata kwata, ta koyi hakuri, da halayyar tausayi snn ta koyi kulawa da marar lafya. Kafin nan Allah ya dauke abarsa ta koma hannun kawu. Those few yrs datay da iyayenta was the only good part of her childhood memry duk dama ta jima bata kaunar tunawa dashi dan baiya haifar mata komi face kewar iyayenta da suka rasu.

Wani bin sassanyar hawayen Nata sai ya sauka da murmushi wani bin sai kaji taja zuciyarta can can sama har kamar zuciyar tata zai balle ya fita daga kirjinta.

Cikin wann yanayin taji kamar ana buga mata kofarta tsam tay batare da ta bude lunsashun idanutan ba, tun tana jin bugun ahankli harta soma jinshi da dan karfi

Ahankli tay juyi snn ta saka hannu akan lallausar fuskarta ta share hawayenta, jiki a sanyaye ta sauko kasa batare da tunanin komi aranta ba ta bude kofar Dakin, khaleel tagani a tsaye Hannunsa rike da cup din ruwa me sanyi yanamai bin jirwayen hawayen nata da kallo.

Takaitaccen kallo tabishi dashi komi na jikinshi is intact kusan ma hularsa ce kawai bata kansa hannunsa daya na cikin aljhu yay mata sallama yay batace mai uffan ba ta juya abunta ta koma kan gadonta taja pillow ta daura kanta akai.

Lumshe idonta tay kadan sann ta bude jin ya zauna daga gefe daf da ita.

Batace mai komi ba shima be ce mata komi ba ya dan tapping gadon ta daga ido ta kallesa nn taga ya mika mata ruwan tare da kwayar magani ta amsa ta sha batare da tacemai komi ba

Shiru ne ya gifta tsakanin su, halisa ta harde ranta sosai ta dauke kai cikin murtake fuska alaman she just want to be alone dan haushi ma taji yake bata, shikuwa cikin ransa he is hoping yay mata godiya snn ya mata bayani akan yan wasu abubuwan dayasan zai daure mata kai game dashi,sede sanin halinta yasaka baisan ta ina zai fara ba.
Chapter 141 · 0% Book details