← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 312

Sashe 166

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayayinda mahmud din ke shirinsa a birnin london da zimman kawo karshe ma matsalolin rayuwar aurensa dana iyayensa

Shema'u anan kuma yan kudaden cikin acct dinta take ta kashewa tana zuwa wajajen bude ido da siyayyan kayan duniya da sukafi karfin arzikin ta, yo babban arziki zaizo musu ita da saurayinta kwanan nan shiyasa bata damu da yawan wanda take kashewa ynxu ba.

Tun daya shiga hidima ta zamo bata da aiki sai daukar wanka da yawo acikin motocinsa tana zuwa shoping agari

kayayyakinta dana nan dana gida duk tay kasafi wanda zata kyautar dasu sabida tsarin rayuwarta gabaki daya zata sauya ya dawo irinna hadiza maitama koma fiye dashi

She made a long list of the cars, the houses and the luxury datake son ta mallaka ita kanta dan rayuwar hadiza maitama kusan shine mata tamkar madubin dubawa.

** Ata daya bangaren Bugun Sautin Wakar sa'adu bori aka kunna wata hamshakiyar dattijuwa tana tikar rawa cikin hayagaga tana kuma rausaya kanta dake kaduwa kamar tsohowar kadangariya.

chan ta kunna hayakin tsadadden tabar nan na marlboro ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki da gayya tana hura hancinta ita kadai tana huci tana kuma yatsinawa ...

Wani katoton Samsung laptp ne agabansu ta dauki pen dinsa tana rubutu aciki da alaman tracking ranakun da za'a gabatar da hidiman project din nan itama takeyi..

Tun daga ranar da za'a gabatar da bikin project din ma wanda suka ci nasara har izuwa sati guda dake bayansa ta ja ma ranakun jan layi da pen din hannunta. Tana yi tana busa hayakin tabarta ajiki daga ganin fuskarta kasan babu mutunci a lamarinta kwata kwata.

Dayan hamshakiyar matar dake gefentan ma kusan abunda takey kenan da alama abun ya shige ta giya mai zafi ta kwalkwala a wine glass shima ta masa zuka daya sanda taji tayi nak.

suna cikin hirar abubuwan dake gabansu aka kira babban cikin sun a awaya, dacan kamar bazata dauka ba sai can snn ta dauka muryanta a mugun dake tace fadi abunda yake tafe da kai ina jinka. Snn ta jefa wayar a handsfre ta aje musu ita da yar uwarta sunajin muryan me magana.

bayani aka hau yi mata dalla dalla cewa tun data tafi kasar dubai business ake ganin mijinta Alhaj shafiu ta da wata mata a hotel.

Daga nan aka fara fayyace mata Gabaki daya tarihin shemau da komi da komi har labarin motocinsa datake hawa tana yawo agari da shoping din data tsira zuwa kullum kullum kai hatta hotonan shema'u tana chilling da hoton su tare da alhaj shafiun kaf an tura musu.

A haukace matar Ta mike tsaye axafafar yanayi ta dafe kirjinta tace ban ci ta zama ba shafi'u ashe har ya samu sararin da zai soma bibiyar mata da basukan kudina akansa?to wallhy wallh daga shi har ita sai na ci uban su..yar iskan matar kuma senaga gatan ta a duniyan, sena...ta jero ashariya yafi sau a kirga

Basuyi wata wata ba suka shirya a wnn ranan suka bar dubai cikin dare suka iso UK da shirin yin operation check out dinsu ma shema'u

Tun dawowar matar cikin gidanta take masifa tana buga manya manyan zage zage Shi shafiun har isa ya debi kudaden da banashi ba yakama wata sheqiyar karuwa daki a hotel??.

Uwar gidan sa me suna hajiya turai ana mata lakabi da turai ture kaga tsiya wanda tsabar balbalin masifarta yau kusan duka masu aikin gidan sanda ta cuna musu bakin ciki da tashin hankli akan maganan shemau dataji.

koda ta ji labarin bata damu da neman mijinta alhaj shafiun ba har se Washe gari da sassafe wajen misalin karfe 9.30 am da yar uwanta ta iso

Saida suka tabbatar da inda zasu samu shema'u ayau snn suka hau shirinsu a ahujajan.

Wata iriyar buba ta saka ta kafe daurin ture kaga tsiya tana wani irin huci

Tana fitowa sarari tace kanwata muje wani yuuu suka fito Manyan tinted jeeps suka dauka kowa da nata tana ja ba su ko tsaya a ko ina ba sai gaban babban filin finsbury daf da gaban hotel din inda mutane ke tururuwan zuwa cikin moorgate station ke yawan wulgawa.

Lekawa suke koxasu ga tahowar shema dan ance musu sassafe taje gucci store siyan kayan da zata tafi dasu london wajen hidima.

dan haka a dede zasu sha kwanar shiga moorgate din din suka bi taron yan mata da cunkuson masu wucewa tashar, mata da maxa wasu ma sauri suke zasu je su karya su dawo station.

Aikuwa dada rage speed sukayi suka kafa idanun su suna bin hanya da ido daya bayan daya can kamar a wasa charaf sai ga motar alhj shafiun ya kunno kai wata ferari sport ce ba shakka mace ce ajiki tana tukawa...

wani ihun hauka hajiya turai ta fasa daga cikin motar ta a masife tace ehhhhhh kam babu shakka samun waje karuwa da baccin rana.
wani wawar juya kan motar tayi ta nufo kan shema'u a guje ai tuni yar uwanta tabiyo bayanta
Aikuwa atake suka janye hankalin ilahirin jama'an da suke wajen tare da muguwar yanayin yadda suke murza kan stering suna tahowa atare ..

A mugun rude shema ta tsaya cak acikin motar ta kasa motsi ganin yadda motoci biu manya suke sawo kai kamar zasu zo su taka ta batama san wai ta taka burki ba, kkrin fitowa a motar take sede tunkan ta sami nitsuwar hakan tace zata bude mota yar uwan hajya turai tayi saurin bude mata motar ta fito cikin sauri kuma a masife

wani irin buga gabar motar tay da ruwan balai tace obbbubbbbububbbu prossssstitude...duk wata ballagazar jakar dake jikin motar nan tayi maza ta fito kafin na fito da ita waje.

Wani irin tsit wajen ya dauka kowa yana jajja da baya abunka da turawa sai scene din ya zamo abun kallo habamana kowa ya daga camera zai samu nasakawa a media

jikin shemau kuwa atake yahau wani irin kyarma ta warware dankwalin kanta ta rufe fuskanta dashi kamar wata ninja acikin tsananin rudani take ɓari tana cewa na shiga uku na shiga uku cikin tsananin tsoro da razana take sake maimaiwatawa tana neman wayarta zata kira alhaj shafiu ko polisawa

aikuwa batayi aune ba ta ji an banke kofar motar din an wanI finciko wata waje kamar yar kaza aka fyetta da kasa hajya turai tuni ta saka hannu ta kwace key din motar snn tabita da wani gigitaccen mari saida abunda ta rufe fuskan nata dashi ya kusa kuncewa kasa

A tsomare suka taru suka cakwamota suka mikar ta tsaye, ta mata irin rikon nan na mahaukata, cikin diri da tsawa mai kada hanji hajya turai take cewa shemau kike kowa?? jibeki fa? look at u..ke har kin isa kici kudi na? Wani Tauu takai mata mari shema ta fashe da kuka
Sukuma suka saka dariya Hahahaha bura uban can jita kazama ma lallai shafiu bai da idon kallon mace yo ke din meye ajikin banda ruwan man bleaching da karnin talauci mhmmm

shema ta rude sosai sabida bata taba kawo batun matarsa a hidimarta ba dan ce mata yake ai matarsa ba komi bace yama fi karfinta dama hadin gida aka musu akanta ne zaiy auren soyayya, wani Kukan baxata da mugun firgita shiya kufce ma shemau ganin su tantiran shedanun mata wanda ko ahanya kagansu sai dai ka basu hanya su wuce, murya ta na rawa rawa tace kuyi hakuri dan Allah waye mijin naki? Ni ban san shi ba,let me go, or i wll call the police...

wani wawan dago ta matar tayi hade da sake mata maruka zafafa kamar ta kama yar cikin ta..

"ohh baki san waye miji na ba ko?..to me wannan motar..ko motar mijinki ne? Yar iska karuwa kina matar wani kato kina bin maza kina kwana da su tufffffff wallh badon kudina dake hannun shafiu ba da saina tuna miki asiri duk duniya sai sun san ke wacece jaka, ke ga uban ki chan yana fama da kansa yay retire yana zaune kamar kayan wanki uwarki tana can tana daga jijiyar wuya wai ita yar hisba me kawo gyara, wani irin dungureta tay a mugun masife tana cewa uwar me sukeyi da basu gyara maki naki tarbiyan ba tambatsaiyar shashaha ta dada shakureta cikin kai mata mari me zafi snn tace bude idonki
Ki kalle ni dakyau shemau nidin dakike gani na cikkayar bakatsiniya ce, sai na hadiyeki anan nahadiye banza babu abunda hukuma zasumin anan kasar bare kuma a nigeria inda kika saba aikin law na karya.

Rasa na cewa shemau tayi tsaban kuka da firgicin kunyar ganin idanun mutane a kansu duk kare fuskanta datay jikinta rawa yake kamar mazari duk tsoronta kar asata a media kowa yagani

aikuwa anan babu mutuncinta da basu ci ba sai jajjan ta suke in a very bad public disgrace manner suna dungurar kanta cikin yanayin yanka mata warning Masu ban tsoro.

iya tsoro da Kunya ma kawai shine ya xautar da shemau ya ladabtar da ita gashi ko a ido tasan wayannan ba sa'oin ta bane bare tayi wani fada da su masifan su da alama ya wuce karfin iskan cin ta..

Haka suka tsinka mata tijara me zafi a tsakiyar fili sannan suka kwace motar su kuma suka shige nasu motar suka barta anan.

Kuka ta dingayi karshe securty suka kaita cikin room dinta na hotel duk ta rasa abunda ke mata dadi tattara kayanta tay tanata kuka gashi nata da ko sisi yanxu duk ta kashe su, banda kiran layinsa da turamai sakoni babu abunda takeyi tunda kubce tay kusan awa tane nemansa ganin bai dauka ba yasaka ta dan kwanta baccin wahala yay awon gaba da ita

Bayan awanni biu alhaj shafiu na xaune akan lallausan lush cushion na home office dinsa Duk damuwar sa baifi dayaga sakonnin shema'u ba

tsabar ya gama tsurewa da abunda matsarsan tayi ko iya amsa kirar shema'u baiyi ba bare ya dauki call dinta.
Chapter 166 · 0% Book details