← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 312

Sashe 119

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

halisa tay nisa cikin ji mamakin yadda abincin ta ya bace bat a tukunya idanunsa masu sanyi daya zubo mata akai sauyin bugun zuciyarta yasaka tafara tunanin ko aljanu ne ma agidan tana ta imagining abubuwan tsoro kala kala aranta hmmmm amma kuma aljanun satar abincin ne zata zauna dasu a gida daya?

Babu zato babu tsammani taji sautin kakkaurar gyaran murya abayanta wani irin dam kirjinta ya buga a firgit ta sake plate din datake wankewar ya fada cikin ruwan kumfa ta juyo a mugun tsorace wufff tay setin kofa zata arce da gudu yay saurin fixgota tafada jikinshi jikinta na rawa rawa dan tana tsaka da yin tunanin aljanu kenan wani irin rungumeta taji yay duminta da qamshin turaren su daya gamutsu waje guda suna masu saukar mai jarabbaiyar kasala a sassan jikinshi
Da Damshin ruwan dayake hannunta ta kankame farar singlet dinsa tare da cukuikye masa gadon baya motsin sanyin hannun nata kan fatar bayanshi yasaaka yakejin kamar ya saki fitsari ajikinshi dan bai san sau nawa ya sauke ajiyan zuciya aransa ba bai saketa ba kuwa har saida tsoron ya saketa

tana dawowa hayyacinta taji kunya me yawa ya lullumeta, kusan kallo daya ta ma hadadden dirin jikinshin cikin sauri ta sauke kanta kasa bata sake iya daga ido ta kalle shi ba tsabar yadda xcyarta ke bugawa da karfi, Ahnkali ta kwace jikinta anashi tay saurin juyamai baya jin zuciyar ta nabugawa da tsananin karfi kamar zai ballo waje ..

Smirks dinshi taji adede setin wuyarta yana cewa "ina zakije aguje dama?

Bata juyo ba bare ya amsashi har saida ta dedeta notsuwarta da hanlknta waje guda snn ta juyo ta kallesa cikin jan aji da basarwa..

tace Babu inda zanje ni wanke wanke kawai nakeyi

Ya tabe baki yana gumse dariyarsa taciki yace i see,..so, Did i scare u??

Dakewa tay Tace 'me? Scared?? Of what...hmm Allah ya sawwake, akai kasuwa.

zai yi magana cikin katseshi tace i am working, wai meya kawoka nan..

Baice komi ba ya mika mata empty plate da spoon da glass cup..

Baki bude take kallonshi ganin ko ajikinshi Ahnkli tace so its u who ate my food.. rau da idonsa yay akanta alaman eh yaci din, a kufule tace bazan karba ba..keep it over der and leave karka sake cinye mun abinci na..
"..understand.???

yatsar data nunamai ya dora hannunsa akai ya karyashi softly ahnkli yace wani abincin naki ma da babu dadi duk gishiri ya cika ma mutum ciki. Gobe karki cika masa gishiri..use ur brain

Harara tabishi dashi kamar idonta zai fado kasa Ta kalle empty plate din kafin ta kalleshi tace "toh ina bolarsa da ka zubar tunda be maka dadi ba'..karka cemin Gishirin ne ka lashe haka

Ta dau plate din ta nuna mai fuska.. "look..u ate and left no crumbs.

Cikin tsokana da shan qamshi yace toh ya na iya dake I can't let the food go to waste, bamai hanaki koyan girkinki kawai de gobe kar asake saka mana gishiri yay yawa aciki.

takaicinshi ya cikata aranta tace Hmm kaci na karshe kenan stupid Snn ta juyo tabashi baya cikin jan kufulallen tsaki ta cigaba da wanke wankenta.

Hakanan yay keeping inta busy da tsokanansa tana shiru tun abun na bata haushi harya dena saidai in ya fadi wanda ta kasa hakura saita juyo ta harare shi sama da kasa

yana tsaye harta gama ta tsaftace wajen kusan kominta da jikinta takeyi cikin kwarewa bakaramin burgeshi yaji take dadayi ba. Dan a fili in ka gan yanayin daular datake ciki da irin gayun data keyi kai tsaye zaka dauka ko ruwan zafi batasan ya ake tafasawa bama.

Bayan ta kammala tsaftace koina tay mopping ta juyo da niyyar ficewa sai kuma ta fasa ta dawo ta tsaya agabansa da wani irin kallon masifa dayake mata mugun kyau tace "toh ai saika fita zan kashe wuta kaje waje...

Karamin dariya ta kufce masa cikin gintsewa yace Kikashe mana ko kina tunanin matsoraci ne ni kamrki.

kanta sama cikin yanayin masifa tace toh har kofar ma zan rufe kawai ta tafi
Harya budi baki zai amsa Dede nan wayarsa ya fara ringing kusan a tare suka kai idonsun kan screen din wayar sai yaga meenal ce.

Rike wayar yay batare da ya dauka ba aransa yana ta mamakin ganin kirarta a wann lkcin.

Idonshi nakan screen din halisa Ta zame tabar wajen Cikin sauri ta haura sama dakinta da tunanin kodan tsayuwar datay gabansa ryasaka bazai amsa kirar matarsa ba...

daga idonshi ke da wuya sai yaga halisan batanan kamar wacce ta bace bat haka yaji, sai kuma yaji zucyrsa bataji dadin haka ba sam, nannauyar sautin hmm ya kufce masa yana murmushi ya fito daga kitchen din yanata kallon hanyar databi can snn ya haura sama tare da kara wayar a kunnensa.

Ba wani abu yasaka ta kirashi ba saidan ta gayamai zata kara kwanaki akan wanda zatay. Tone din gadara data gayamai maganan dashi yasaka yaki ya bata permission din yace mata nan da sati biyun yake son yaganta a gida.

Tana katse wayar tay banza da zancen nashi abunta aganinta babu abunda zai yi yasakata tay azumin dole itade.

*******

Washe gari da safiyar Allah suka sake ficewa field basucewa junansu uffan ba har suka gama routine din suka dawo.

Tun tana saka ran cewa zai tambayeta batun kawunta har abun ya fara fice mata arai gashi routine din yasaka yanzu tafarajin kanta wasai so energetic and enthusiatic

Irin kaji ka da karfi karfin kan nan, she is bcming bubbling strong, fresh air da feel of nature datake arangama dasu sassafe in sun fito field din a take yake sata jin nitsuwa har brain dinta takanji sanyi da sauki

agidan yau Banda nemanta da magana babu abunda khaleel yakeyi dake yunwa na damunta sai ta shareshi,

kafin tay wanka nan ta tsaftace koina kafin nan ta kira me gadi ta bashi list da kudi kimanin 100k tacemai yaje kasuwa ya siya mata duk abunda ke kan list din ya kawo mata

Doguwar list ne kusan babu abinda babu aciki
Chicken, goat meat, red meat,varieties of fishes, kayan miya, kayan yin cakes da small chops, patotoes, yam, fruits, da kala kalan spices da sauces kusan komi na girki na zamani akwai acikin list din.

Dedeku da suke gidanne kmr su drinks, kayan tea, bootle water egg, bread, bamas, sardines da sauran raw food kawai bata saka dasu ba.

kafin Me gadi ya wuce sanda ya same khaleel agaban motarsa yana tsaye yana amsa wayar maman sa akan jikin grace..

a gefe yaja ya tsaya har sai bayan da suka gama snn ya gayamai cewa madam ta aikesa kasuwa dan baison ya bar gate din bakowa batare da ya nemi izinin ogansa ba...

khaleel ya karbi list din ya karanta ya girgiza kai yana mamakinta lallai mata akwai son jin dadi
Anyways is his fault da bai aje dadin agidansa ba cikin wata sassnyar kwafa data kufce masa aransa yace tohh ko ya aje ma saidai su jima a fridge har su lalace cos meenal is soo allergic to cooking karshe me gadi ke tattarawa ya zubar ko ya kai gidansa suci.

atakaice Ya kalle malam liman yace ka tsaya a gate din kawai tunda fita zanyi zanbi kasuwan na siyo... Bazaiyu abar gidan babu security ba

Malam liman baimasa musu ba ya ciro kudin data bashin ya mika masa khaleel ya kalle kudin yace kabari naje na dawo tukun.

Daga haka ya shiga motarsa ya fice yaje ya dauki abokinsa hafeez sukaje kasuwan tare babu abunda yake
cikin list din da basu sayeshi isasshe ba,

Hakanan ya dinga bawa hafeez labarin yadda halisa ta iya abinci me dadi da saka nitsuwa irin na mamanshi har cewa yake wata rana zai kirasa yazo yaci shima.

hafeez na dariyarsa yace mai shifa tuwo ma yafiso a dik cikin abinci dan haka in zaizo tuwo kawai zaici, wanda yasaka khaleel ya tuna da wasu abubuwan kamar su egushi, ewa, sesame seeds,flour, garin amala, garin kwaki Komi dan dede ya siya dake suna da oils da semovita agidan nasu,

Ganyayyaki da fruit hilimi guda suka dawo gidan dashi, haka nan suka sauke ma malam liman agabansa yace masa ya hada mata da kudinta yakai mata ciki.

yasan intagansa agidan haka yau zasu kwashi drama dan haka yaki shiga ciki yajuya yabi abokinsa hafeez suka shiga gari yabarta agidan da malam liman sukadai

Aikuwa tana ganin kayan riki riki jikinta ya bata cewa khaleel ya saka mata hannu ji tay kamar tayi ihu snn ta kamashi ta zazzane shi a mind dinta, tana jera kayan a kitchen amma babu kalar mitan da batayi ba kusan gemun malam liman din ne kawai ya hanata masifeshi shidin ma daya dawo mata da kudinta.

Duk da haka saida ta gaya mai cewa batason ta sake aikanshi ya nunawa khaleel aikan, ganin ta bata rai yasaka ya dinga bata hakuri

a masifenta yau ta zauna Jiran khaleel, dacan ma zuciya tay tace bazata taba kayan abincin ba amma daga bisani bayan ta huce sai ta tuna kalar nasihar da jasmine ta mata kawai ta share batace mai komi ba.

Koda ya dawo banda harararsa babu abunda ta dingayi wunin yau Din cur sukayi bata amsa masa maganansa ba, wani kallon inta masa baiya iya daurewa daki yake zuwa yaci dariya ya godema ma ALLAH.
Fannin Halisa a kwana biyun da suka shude kusan a dan dolenta ta daure tay amfani da duka vegies din daya siyon tay musu miya dashi har kala uku snn ta sakasu a airtight containers ta ajesu a frigde dan kar kayan su lalace.

Hakanan khaleel ya sakota agaba duk sanda tay girki Agidan shine yake cinye rabi yay biris yace mata be masa dadi ba.

Babu ranar da basu drama me ban dariya akan abinci, wani bin jasmine ce kawai ke iya raba fadar tasu dan itake kadaice ke iya lankwasa ra'ayin halisa take barin shi yana cin abincin.
Chapter 119 · 0% Book details