← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 312

Sashe 140

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki jasmine tace "Why why meyafaru kuma ynxu..

maganganun dataji khaleel na mayar ma yar uwarsa da dan tsirarrun dataji yar uwar nasa na maida masa tafara maida ma jasmine filla filla, she sound so so confused and dispointed da abunda meenal ta aikata bana wasa ba.

jasmine kinsan kukan fitar rai da Amina tay ranan? Kijifa amma ai cemin tay matar nan ne ta zuba mata abinci ajiki snn ta tureta kasa Amma ashe tsinannen rashin kunya ta juye mata harma fa zaginta tay tace mata ta zuba musu maganin boka a abinci ta kawo dan arabata da mijinta wai ashe Har kuka maman nashi tay mishi awaje..

Jasmine tace bura uban can.. shine bai sake yar bura uba ba ita waye haka da ake barinta tana bazawa mutane iskanci? Cikin cizar labba tace kasssh ohh my god
...hmmm yanzu naji batu, cos dats more like her..Uwarta ma bata daraja ba saikike tunanin zata daraja na wani?? yar iska, wacce batada aji, wallh Amina dakikiyace nawuce misali. Aiko wanda baida ilimi bazaiyi wann tashan cin ma uwar miji ba.

Halisa batace komi ba dan meenal ta mugun bata mamaki jsmine tay wata shewa Hehehe Ayyuriri Allah ya kara, dama ai nasan dolene yanada kwakkaran dalilin daya sakashi dukanta dan haka kawai bazai kamata rana daya ya hau bugarta ba...did u see what i am telling u now? That bitch is a devil frm the pit of hell, bura uba inama ace uwata ta zaga dana sai yankata, ya mugun burgeni daya daketa dama wani shegen ne za'a raina mai uwa snn ya zuba mata ido yay shiru da wani ne ma bayan bugun daya sake yar iska kawai.

Halisa tay shiru duk dahaka itade bata wani gamsu ba dan hanklinta yaki dedetuwa da batun violent behrv din nan nashi.

Wani zucyar yace mata ko hala dan ciwonsa ne but inma hakan ne saidai ace yay kokari tunda a iya dukan kawai ya tsaye bai saketa ba.

tana cikin wnn tunanin jasmine tace toh aikinji kema da kika fushi dashi sai ki sassauto kiyi hakuri ynxu ko.

Ajiyar zuciya ta sauke tace jasmine i dont knw yet. Bcos i still don't get why he will lay his hand on his woman. Dats domestic violence, what if she sue him, ko hakan ya batamai suna awani waje.

Dariya me sanyi jasmine tay tace halisa kenan, i get he disspointed ur expectations Amma meyasa tun zamanta a lkcin dayake dukantan bata kai kararsa gida ko takira lawyers dinta ba.

Or u think batasan ryt dinta bane..waye besan meenal Talba is a chronic feminist ba, a'tho her own feminism is pure madness but omo shegiyar fa tasan metakeyi sarai, batason ya saketa ne dan tasan in har ya saketa itace da babban asara.

Murya a sanyaye halisa tace kedai jasmine kin fiye shan bakin gayen nan,shima yana da fault dinsa da yawa Waimesa bakiganin lefinshi ne.

Jasmine tace "Men hate disrespect halsy ke kanki kinsani... mace ta kawo kyau, ta kawo gindi me dadi, ta kawo diri ta kawo arziki, ta kawo soyayyar duniyar nan, but if she lack tarbiya and respect she go collect shege banza frm her man ooo.
yanzu kinsha coffe din ne ko baki sha ba

Cikin sauke ajiyar zuciya tace bansha ba fa

Jasmine tace okay go on, am glad u knw the truth. Left for u to judge him fairly atleast kiyi wankan sallahn mana ki turamin hotonanki kinsan fa musulmi zan aura so we go dey celbrate sallah and xmas together with my husband bazaiyu kina barina ina hidiman sallan cebration din nan nikadai ba.

Karamin dariya halisa tay snn tace kefa baki da matsala bagashi kin fara koyar zuwa bama?. Toh shikenan kije ki same su zamu hadu a online later innayi wanka.
Ahaka suka katse wayar halisa ta fito waje kai tsaye tahau kimtsa gidan koina saida ta share ta goge ta fetsa qamshin purp'e lavender a duka corridor na falon snn ta bar Ac a medium waje ya kama sanyin kamshi.

Coffe din kawai ta dafa ta dawo dakinta dashi tazauna tana sha ahankli tanakan tunani akan abubuwan da suka faru .

bayan nan wanka ta fada tana fitowa ta kimtsa kanta acikin nitsuwa tare da aje zancen jasmine agefe, sama sama ta qyara fuskanta da light make up bata cika make up a fuskanta ba banda lips glow da eyeliner bata saka komi nadaban ba..

Sumanta kawai ta zage ta gyara sosai tay styling dinshi da argan oil, mint and barbasu yay laushi yana qamshi me dadi, snn ta mikar dashi da hair stretcher da gels, ta zubo jelarshi duka ya bazu mata tun daga kafadunta har izuwa gadon baya,.all White inner wears ta saka tare Italian gown dinta fari kal na sara battagli, bajajje ne amma dogo ne har kasa me tsagu da aka daukosa tundaga cinya ata gaba ta zura ajikinta.

silver colour Flat shoe ta zura akafafunta snn ta fetsa turarenta tabude jaka ta ciro kudi tayo waje dashi nan ta samu dede me gadinsu ya dawo daga masjid ahankli ta karaso inda yake fuska babu yabo babu fallasa yau ya saka yar jamfarsa brown colour sabuwa kal da kha'eel ya bashi tun a farkon azumi, nan suka gaisa har kasa ya tsuguna yanata mata addua da godiya kamar zaiyi kuka akan irin kyautata masa da tayi alkcin azumi. Har mamaki ya bata da kalar adduoin dayake mata ita da khaleel, dan wani abun ma da alama baisan yana furtawa ba, alot of things he say dat she neva expected.

me kuma ya kawo Allah ya hada kanku ya baku zuria dayyaba. Hahaha

Abi me gadi don marry her off to khaleel ne?

Tunda ta bashi kudin tace mai goron sallahn matarsa da na yaransa yake ta murna kamar zai tashi sama cos is almost the amount of his salary.

Tun data bar wajen take dariyarsa a zuciyarta shigarta gidan bada jimawa ta sake jikin sallamarsa akofar dakinta ta fito tace lfya kuwa?

yana Washe baki yace hajiya madam kunyi baki ne awaje

Da mamaki "Tace baki?

Yace eh.

Tace ohh okay kace musu su shigo ciki mana sujirashi a falo, sai inka fita ka kira ogankan naka awaya kace masa ya dawo gida yay baki.

A' ladabce yace toh snn ya sauka.

Da kamar bazata kula bakin ba sai kuma tace babu kyau wakalanta mutum dan haka zata fito taga suwaye ne koda gaisawa ne suyi, me gadi yana sauka after like 3 mint sai gata itama ta sauko.

Ahankli take tahowa inda qamshin turaren da baqin suka shaf yake mugun debar ta ayayin da kwakwalta yake jiyo mata shi kamar ma qamshin jikin khaaleel din ne.

Can cikin babban falon tanufa a hankli ta kutso kanta ciki bakin ta dauke da yar sallama" salam alaikum..

dukansu a lokaci guda suka juyo atare suna masu zuba mata idanu cikin tsandarewa duk da sukaji muryan mace sun dauka ko meenal din ce ta dawo sai kuma sukaga wata angel din tadaban gashi dama farin kayan ta saka.

..wani shiru ne ya ratsa wajen halisa ta tsaya cak tana dan rarrabe idanu tana dan satan kallon su.

Kyakyawawan mace na ajin farko kamanta zak khaleel, tare da kaninta dake mugun kama da mum dinsu dukansu sanye da tsadadun kaya

Maryam din ta yafa babban swvroski veil da hadadenn jakanta na balmain da wasu yan yara agaban su wayanda bazasu wuce shekaru 6 zuwa 10 ba.

cikin nitsuwa halisa ta karaso ta gabansu da sakin fuska tace sannun ku da zuwa, ina kwana?

cikin rudewa da kyaun halisan Aliyu ya amsa gashi gabaki daya qamshin turaren rebelle by rihanna da ta shigo musu da shi din ya gama tafia da su, maryam kam shiru tayi tanata kallon irin tsaban kyaun da Allah yy ma halisa, kaf kaf ta tsaya ta kare mata kallon kurel kamar wacce taga fatalwa.

Haka nan h'alisa ta musu tarbar mutuntaka sudai har yanzu Basu ganeta ba dan haka kowa ya zuba mata idanu yana faman magana shikadai a zuciar sa .

waje ta nema agefe ta zauna inda ta dada basu aikin kare mata kallo.

da har maryam din zata tambayeta ita wacece charaf sega sallamar khaleel a tsakar falon fuskansa dauke da mamakin ganinsu.

Suna hade ido da haleesa ta tashi da sauri ta haura sama abunta yabita da ido yanata kallonta adan shagale.

Da sauri maryam ta tashi tana dariya ta dan fado jikinshi cikin dawo dashi hayyacinshi ya dan rungumeta sosai yana cewa i cant beleive this.

Aliyu ya mike tsaye yana murmushi yana cewa yaaa ibrahim ita tace sai munzo muyi suprising dinka tun jiya da dare tazo lagos ingaya maka.

daga cikin zuciyarsa sassnsyr dariya ta fito yace hmm i love this surprise. shine ko kacemin tazo ko.

sake ta yay yaje gaban yaran yana murmushi ahnkli yace Mayaudariya kawai Dama ashe kina garin nan kike raina min hankli da safe wayann yayan waye haka kika kwaso?

tana dariya tace na makwabta. Dama cewa nayi sena zo gidanka yau koda korarmu za'ayi injii dai nazo naganka, i was so distubd with the way u talked to me daxu..

Harara ya watsa mata yace dama wazai koreki yar rainin hankli kawai cmn seat down.

Dede nan halisa ta sauko da tray, me dauke da da botle water da viscuits da nau'oin junks na yara ta shigo dasu ta aje komai agaban su.

yarinya yar 6yrs din ce ta soma kaiwa hannu ta dudduba batace komai ba ta kalle maryam anty ni ba zanci biscuit ba

,..Ahmad yaron 10 din shima ya make kafada yana mita a dole shi asalin abinci yake so,

Take aliyu yahau masifesu "Kai kunci kaniyarku bakuce ma anty thank u ba, kuna demanding din abinci?

halisa na murmushi me sanyi ganin yaran duk sun jiyo da fuskan tsoro tsoro suna kallonta ahmad yace we are sorry anty, yarinyar tace good morning anty.

Kansu ta dan shasshafa snn tace good morning, cuties, and happy sallah.

Yanayin sakin fuskan data taresu dashi yasa yaran suka amsa ta da dan sakin jiki....

Sosai maryam taji nauyin idon halisa tace sorry abt that miss..

ahnkli tace Its okay i will get the food, ai yara ne.
Chapter 140 · 0% Book details