← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 312

Sashe 51

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zancen zuci yake bai idda ba face saida sautin sassanyar muryanta mai mugun sanyi da darsa kafafen tarihi acikin zuciya ya datsar dashi.

Bayani ta masa akan cewa su maman sun fita gaisuwar mutuwa ne da sassafen amma sunje bazasu jima ba.

Ya amsa da okay yanata mamakin yadda ta iya karance labarin dayake ayyanawa a zucyarsa cikin sauki.

Qamshin abincin data taho dashi ya hanashi nitsuwa ya bubbude dakansa yaga pancakes din da ta soya ya tsaya yana kallon abincin "did you make all of this? ya faɗa tareda juyowa yana kallon fuskanta da kyau.

a hankali ta gyada mishi Kai tanamai kallon ƙasa,

dayan warmen dake kan table ya bude qamshin abincin ne ya sashi yaja baya yana kallonta yace
"wannan kuma fa?

da dan mamaki ta wara ido a hankali tace masa ne da miya mama tace in dafa maka danka samu karfin jikinka sosai.

tabe bakinsa yay snn ya gyaɗa kansa yana dan murmushi don ji yayi ta burgesa ba kadan ba gata karamar yarinya marainiya amma tana da nitsuwa sosai snn bata saka komi aranta ba.

Dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta waje ya samu ya zauna akan carpet yana duba time yaga its 8 am now"

matarshi shema'u ne ta fado masa aransa tuna yasan tunda suke bata taba farkawa ta kawo masa koda ruwa izuwa wann lkcin ba, sai da yaga hafsat ta gama serving dinsa abincin sann ya sake ranshi cikin janta a hiran dole suka dan zauna cikin friendly chat suka dan ci abincin tana lura ya cinye nashi tas santin miyar zazzafar masan duk ya nuna bisa kan fuskarsa, sosai ran hafsat yay dadi sai satar kallon junansu sukei.

Bayan ya kammala ta mike kamar yadda ta saba zata hau aiki yace basai ta share wajen shi zai share mata, hakan kuwa ya dauko abun shara ya share wajen ya kimtsa. Dan baison ta dinga daukar kanta kamr me aiki agabansa sabida shi mutum ne me kiyaye dokokin addini, duk dama yasan bai amshi auren 100% aransa ba amma baison ko kadan yayi wani abun da zai kaskantar da ita.

Hafsat bata ce komai dan tsananin kunyarsa yasaka kawai ta takoma kitchen din don tsaftace ko ina musamman inda tayi girkin. Shikuwa lura dayay cewa yanayinsa ne yasa take kasa iya sake jikinta awajen sosai cikin dabara ya dauki remote din tv ya kunna kallo.

Lkcin hanklinsa na kan kallo ta fito ta haura saman ta nufi dakinshi.

As usual samu tayi bakowa aciki,ta tsaya sanda ta ƙare ma dakin kallo sosai snn ta soma da kimtsa masa kan gadon sa ta gyara gadon ya lailayu yay fes tamkar ba taba kwanciya akai ba,daga nan kuma batayi tsamamni ba taga har ta kama goge goge da shara sama sama tayi mooping floor din dakin duk wani kuran da suka makale akan madubi da jikin kujera saida ta gogesu..

within 20 minutes harta kammala komi ta rasa me zata fetsa a dakin yay qamshi, kamar ance ta duba kan madubi aikuwa taga room freshener purple flower vanilla da mixed scent na lavender purple mixawa tayi snnan ta fetsa lungu da sako saida ta tabbata da koina a dakin ya dau kamshin dadi.

rage Acn tayi tabarshi a low snn ta sauko kasa nan taga iyayen nasa har sun dawo, a ladabce Ta musu sannu da dawowa zata wuce daki kenan mahmud dinma ya mike zaije shi cikin daki dan yasan dolene su tambayesa akan hafsa.

Sede Yana mikewar mahaifyrsa tace tana son magana dashi.

Sosa kansa yay ahankli cikin jin kunyarta Yace mama wayana na manta a dakina zanje na dauko ne...sai batace mishi komi ba ta kyaleshi ya haura saman.

Yar uwar maman nasa Hajya binta cs ta kira hafsat ta taho tadan rusuna agabnsu suna yaba mata da kkrin girkin datayi.

Tun jiya hajy bintan take janta ajiki tare da mata tambayoyi akan irin training din da aka basu acan lagos sabida aikinsu hafsa kuwa bata boye musu komi ba ta gaggaya musu har yadda ake koya musu magana da turanci da kuma girke girke da tsafta kusan dai karatu da haqqinsu ne kawai ba abasu dede.

Hjya binta ta gama nazari taga da alamar bazata sha wahala wajen zamanantar hafsa ba dan abubuwan da suka rage yarinyar ta iya basu da wani yawa. Saidan yarinta da kauyanci dayake damunta wanda a tunaninta daga sun dan sauya environment wann yanayin duk zai kawar

Bayan ta kammala lissafinta ta kalle yar uwarta cikin sauke ajiyar zuciya basu cewa junansu komi ba.

Sai can Tace ma hafsat din tashi kije ki duba minshi kice masa ya samemu a daki

aladabce sosai hafsa tace toh hajy mama.

Nan ta mike ta haura sama dakin mahmud tana haurawa suma suka haura can sama cikin babban dakinsu suka zauna cikin tattaunawa.

Hjya badiatu tace nifa na riga na gama yanke hukunci ke kawai nake jira badiatu ku bani go ahead dannima abun nan ya fara damuna sosai sai inga kamr mahmud yana cikin wata damuwa.

Cikin kyabe baki Hajy badiatu tace ahto na nina dauka nice uwar azarbabi amma kema ai kinsan mahmuda da zurfin ciki, gashi nan ya zama tamkar abun tausayi a wann auren nasa da yarinyar can shemau..amma ace yau kusan satinsa daya kenan agidan nan kuma baida lafiya irin haka amma matarsa ta sunna bata leko ta dubashi ba gaskiya abun da abun dubawa dai

Cikin taɓe baki Hjy binta tace hmmm kawai shawararki zamubi dan bazamu zubamai ido ahaka ba. Ga Abinci a hannu ai bazamu fita dawa farauta ba, just a little upgrade zanyi ma yarinyar nan and im sure he will like her snn rayuwarsa zai sauya masa, karamar yarince danya shataf zai moreta nam gaba bana kadan ba, inyaso wancan din karta shiga hayyacinta har abada.

Hajya badiatu tace Toh yanzu me kikeso nayi binta?

Tace Kiyi magana da mahaifinsa kawai nikuma zanyi magana dashi mahmud din akan makarantar ta inji me zaije kinsan koma me xamu yanke akanta saida cikakken amincewarsa tunda da igiyar aurensa ne akanta.

Hjy badiatu tace hakane
Bari naje toh na same baban nashi daga can ma sai afara batun mata visa.

Tace Yawwa tou ba damuwa sai kin dawo

Nan hjy badiatu ta mike dauke da wayarta a hannu ta fice waje tabar hjy bintan a zaune a dakin ita kadai....
Bangaren Mahmud kuwa koda ya haura sama izuwa dakinsan sosai ya sha mamkin ganin yadda hafsat ta tsaftce masa dakinsan ko ina ya dau qamshi duk dama ransa na cike da kewar matar sa shemau amma with each day saiyaji yarinyar nan hafsa tana kara burgesa.

Tun da ya shigo dakin bai iya tabuka komi ba Yana kwance shiru.

wayarsa ce ta fara ringing ya dauka da sauri ya dauka shemaun ne dake itadin kawai yake tunawa aransa can sai yaga contractor dinsa ne na nan Abuja da mahaifin sa ya hadasu dashi akan sabuwar contract daya sama masa a memakon wanda ya rasa a lagos.

Daukawa yay suka gaisa da mutumin snn ya fara masa bayani ranar da zasu dawo bakin aiki dan dama ya fara gajiya da zaman gidan yanaso ya dan kama aiki kodama jikinshi zai warware sosai.

baifi minti uku da fara wayarba hafsat tay kncking abakin kofarsa batare da yasan waye bane ya bada izini ta shigo ciki, dago kanshi yay zai duba idanunshi suka sauka akanta t tsayawa cak tay Shiru shikuma ya cigaba da amsa wayar yana dan satar kallonta idanunta dayasha baqar kajol yay wani irin haske sai cikakke kuma doguwar eyelashes dinta dake kadawa yadda ta taho ahnkli kamar bazata karaso ba yasashi dan dauke kaansa bada wani manufa ba saidai halinda ya tsinci zucyarsa aciki and he dont want the feeling to grow much higher.

Jiransa tay harya kammala wayarsa Kafin nan ya rufe ido ya bude Gani yay harta rusuna agabansa aladabnce tanamai gayamai sakon hajya cikin sanyin murya.

Batamaji amsar daya bata ba . Taga yana murmushi. Mikewa yay lokci guda babu yabo babu fallasa ya fita sann tabishi abaya har suka kai sashen basucewa junansu komi ba

Suna isa sashen ta wuce dakinta abunta shikuma ya karasa cikin dakni ya same hajy binta tana zaune shiru cikin nazari.

Smirk me taushi ya kufce masa agefen bakinsa yana mai fidda kirkirarren murmushi ya zauna akan kujera acikin yanayin nitsuwa yana satar kallonta.

Can yace Mumy lafya naganki haka?

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sn ta dubeshi tay murmishi ta karkada kanta batace mai komi ba sai kuma yaji ya damu sosai da yanayintan da yagani.

Yafi sakewa da ita fiye da mahaifyrnsa dan haka Babu wani bata lokci suka tsunduma cikin tattaunawa harta shawo kansa cikin maganan makomar rayuwar hafsa duk dana ya nuna mata shide ba auren ne agabansa ba yana dai son hafsat din tay makarnta ne yanxu.

Dama can shi Shawaranta kawai yake nema akan qudirinsa na sakata a makarantar dake baisan wanne ne ya dace asata ba.

Gashi aransa bayason yasata a makarantar da yay kusa da gidansun sabida baison sukai wani matsayin da zaiji sha'awar aikata wani abun da zai zalunci rayuwarta musmmn ma aynzu dayasan da cewa shemau ce kawai a cikin zucyarsa bazai iya cin amanar matarsa ba.

snn yana son ya samu wadda zasu dinga saka mata ido akan rayuwarta na yaranta asan duk wani abunda takeyi da wayan da zatana muamala dasu sabida igiyar auren sa dayake kanta ynxu.

Bai iya furtawa hjy hakan ba amma sosai ta fahimce shi, abu daya ne kawai yay mata dadi daya kasance yana so din tay karatu ta samu nitsuwa, wanda shine ya bada dama ta kawo masa maganan tafiyarsu can turkey akan cewa sai hutu hutu zasu na dawowa inda zatayi saurin lanƙwasuwa ta kuma san ciwon kanta sosai.

Dama kuma akwai wani sabuwar private college da aka bude a kusa da anguwarsu mai suna Harish international college, babban makrnta ne me kyau makarantar yana nan a tsallaken titin anguwar sun dake can turkey so baida wani nisa da gidansun sosai.
Chapter 51 · 0% Book details