← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 312

Sashe 115

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

data fadin hakan still baice komi ba sede yanayin fuskarsan kawai ya isaka ya saka kayi masa kuka tsabar yawan damuwar da furucin nata yake jefashi ciki dan duk duniya baida wanda yake so aransa na hakika kamar mahaifyarsan shiyasa ko kadan baison wann damuwar nata akansa yacigaba da jefata cikin kunci.

Yanaji ta kyabe bakinta ahankl cikin kaucar da maganan. ajiyar zuciya ta sauke snn tace " toh ya ake ciki da case din naku, Is everthing alright?
Nadra tace min akwai cancer patient aciki
..ibrahim ina fatan kasan cewa u can count on me On that one ko..iyayenta suna raye ko sun rasu?

Muryansa a sanyaye sosai yace nasani Ammi, dan kadan ya tsakura maata labarin su mama G snn yace infact hakan ma zanyi, idan Asad sunzo mun tattauna zan yima yarinyar hanyar ganawa da foundation dinki na cancer dan nasan zaki dauki mataki akan lamarinta sosai,

Ya sauke muryansa kasa kasa cikin sauke ajiyan zuciya "Ammi this case is kind of personal to me, kuma duk duniya bani da wata garkuwa face ke..

game da maganaan dazu, Cikin lallamai sosai yahau lallashinta, pls, Ki kwantar da hankli kinji, i am tryng my best for ur sake. Ki cigaba damun addua mamata.

Murmushi tay me sanyi tanamai jin dadin kalamn nasa har cikin ranta, ahnkli snn tace 'nasani..
and i will..ynxu de zan saurare kirarka akan batun yarinyar Idan akwai emergency just call me direct zan turo da ambulance a dauki patient din for immideite attention

Yace toh Ammi bari mu tattauna da iyayentan tukuna. Nazo ne dama na karbi rerpot wajen agent dinmu da take interview da ita aciki after then zamu tattauna da likitocon da abun ya shafa saimu dauke transfer permit izuwa hannunki..

Cike da gamsuwa tace hakan yayi kyau bari na kyaleka toh Allah yay maka albarka ibrahim..

Wani irin sanyi yaji aransa datace mai hakan muryansa a tausashe yace Ameen Ammi.

Daga nan suka katse wayar yana juyo kansa direction din kofa yaga Asad din daga nesa na tafe da dan karamin baby a hannunsa daya runguma calmy kamar za'a kwace mashi shi.

Murmushi me sanyi ne ya kwace akan fuskansa bai sauka a motar ba ya zuba mai idanu daga can yana admiring dinsa tare da kallon how cute he look with his 3yr old baby

Maganganun amminshi ne suka fara dawo masa kansa cikin lumshe ido da budewa ya furzar da wata malalaciyar iska abakinsa "maybe he will try to talk to meenal akan haihuwa wann karon ita dawo kodan mahfyrsa taji dadi duk da yasan ma ba abu bane da meenal din take bashi fuska akai..

Cikin duniyar tunaninshi yaji ana bugamai glass din motar ya dagokai kenan caraf suka hade ido da Asad daga waje nan yaga ya kama fragile yatsun baby yana masa waving dashi yana cewa uncle khaleel uncle khaleel ure under arrest

Khaleel ya bude kofar yana murmushi me fadi yana sauka ya amshi babyn a hannunsa ya rike
yana cewa How useless of a father are you ni
Bansan mesata barka da yarta ba wallh..ina nadran take?

Asad ya kalle parking lot dede inda wata arniyar mercedez maybech take parke yace gata can, she is in the car, baby number 5 on the way wai amai takeji kaga ai Dolene ta barmin rainon wann.

khaleel ya wara ido akansa sigar raha "Oh god... are u seriously taunting me now..Hmm su father of five manya.

Dariya Sukayi me dan karfi atare, yace To me zan jira niba likita ba bayan naji ance ku doctors din nan bakusan haihuwa sabida kun gaji da gani.

Girar khaleel na sama a dage yace "Wayace maka haka,lawyers dama akwai zuba karya.. mtss, kawai lokci ne baiyi ba But Don't worry mr law i will shock u.

Dariya me karfi Asad yay
Cike da shakiyanci da tsokana ayanayinsa yace to kacika aurenka da mata uku mana, sai su dawo su hudu, sai ka musu ciki rana daya su zubo maka yan uku uku, kaga 3+3+3+3= dozen
..dats is wen u will impress me.

Khaleel bai iya cewa komi ba tsabar dariya Anki ayi impressing dinka Pls get out, Asad ure seriously mad dama nasan bazaka taba canzawa ba..

Suna cikin raharsu sai ga nan nadra ta iso wajen tare da sauran yaransun, yaran badai kyau ba dan duk kamannin iyayen nasu suka hada, suna isowa wajen Khaleel suka wuce direct suka rungume shi kowa na gaishe shi babban su is almost 8yrs dan tun a mota nadrahm tace musu uncle dinsu ne.

He look soo cool and happy with them cikin zuciyarsa sai ya dadajin irin kalar feeling din da mahaifyar sa takeji akansa tabbas yara rahma ne sosai.

Tambyarsu labarin schl yakeyi da harshen larabci suna amsawa so fluently cos they can speak like 3 languages english arab da hausa duk dama ba sosai suke zuwa nigeria ba.

Asad ya kalle nadra suka hade ido suna murmushi looking at how cute khaleel is with kids dinsu..

Yanayin tsokana Nadra tace Doc ko zamu bar maka su ne..it seems like babies are fond of u

Yace naaa, rabani.. karki bari mijinki ya koya maki karya kinji..

dariya tay Asad yace mtsww Ji yadda babyn ma ta lafe ajikinka ko kunya bakaji, karde ka sake mu sake dawowa kasar nan banga dozen din nan akasa ba.

da mamaki Nadra tace
"Aww dozen yake hari?

lokci guda yace noo.

Asad yace yess.

Tace okay enuf naga alaman dramanku bazai kare ba, yakamata muje bakin aikinmu ko..we dont have much time

jokingly Asad ya kalleta yace "yess ma:am"

Murmushi me sanyi suka sakar ma juna.

Kusan atare suka je ward din aka kaisu har wajen likitan dake kulawa da case din gracy, nan khaleel yabarsu Asad awajen suna kan tattaunawa tare da likita akan condition din grace shikuma ya fita yaje room dinsun, bai shiga ciki ba daga waje ya kira agent dinsu awaya tabar su halisa aciki snn fito nan suka wuce office din tare da ita.

After few minutes of conversation da bincike nan da nan suka tattara bayanan da zasu tattara snn suka wuce da shi headgtr domin fuskantar
su maman gracy.

sunje sun samesu sunyi zuru zuru duk cikinsu ya duri ruwa dake suna iya karatun turanci sunga logon human right ajikin bangon wajen

Atake atake suka larne fuska suka maida kansu abun tausayi sosai tun zamansu anan sai kus kus suke da junansu cikin matsancin tsorata cikon kwayar idanun kowannensu cike da nadama dan dasun nan zaa kawosu daa guduwa kawai sukayi..

suna cikin wann yanayi saoga Asad da nadra da khaleel da wani agent sun shigo cikin wajen.

Kujera suka ja suka zazzauna suna masu fuskantarsu fuska babu yabo babu fallasa.

Agent din ya fito da ID card dinsa ya nuna musu tare da musu brief introduction na kowa da kowa..

Bakin kawun halisan na rawa rawa yace Shi bai gane dalilin da yasala aka kawosu nan wajen ba.

Kai tsaye nadra tace musu is about his dougther's conditon snm ta fito masa da magann likita dana shugaban makaranta..

Caraf mama G ta amshe maganan tana cewa ai suna son yarsu tunda gasunan sunzo all the way frm benue to lagos
damsu kula da ita

Dede nan Asad ya amshe maganan dake shi bamai iya jure tsamin baki bane..yakanyi dealing da manyan masu lefo akasashen waje ma bare su.. Daga kan record na schl, izuwa na asibiti da recording din khaleel duk ya fayyace musu snn ya nuna musu cewa zai iya sawa akaisu prison idan sukace zasuyi bata mai lokaci.

mama G taji kamar zata saki fitsari ajikinta. Mijintan kuwa sai bare baren baki yake. Ababu yadda suka iya suka amsa lefukansu, suna nuna nadamar bogi nasu san dacewa duk sun karance su tsaf.

Khaleel is a psychologist, asad da nadra kwarrarun lawyoyi ne. Is almost imposble kace zaka zo gabansu duka uku snn ka yaudaresu da wani nadama ko hawayen karya.

Har kasa mama G takai cikin jimami tana cewa ai frustration da talauci ne yasaka ta furta ma yarta duk abunda akaji recording din nan..

Khaleel bai tashi kufuluwa ba sai da kawu ya fara dora ma Halisa lefin komi. A Cewarsa halisan ce ta jawo musu hakan dan tay kudi ta barsu cikin talauci shiyasa basu iya kulawa da rayuwar yarsu ba.

Duk dama ransa ya baci amma cikin ruwan sanyi ya daure kawun da jijiyar wuyarsa..wasu irin tambayoyi da bai shirya jinsu ba khaleel ya fara jefo masa. shikuwa Asad
Da yaji zancen sexual abuse aciki hanklinsa ya tashi sosai, cikin lkcin kalilan suka saka kawo a hot seat har saida yay dan danasanin ambatar sunan halisa acikin maganansa gabaki daya

khaleel make sure to make him admit that sanadiyarsa halisa ta gudu tabar gida and same thing happen to grace..

Akarshen karshe asirin kawu dayawa ya tono na maganan yadda ya walaknta rayuwar halisa wanda lawyoyin suka danganta da irin abunda yakeso yay ma yar cikinshi.

Asad yay niyyar daukar tsatsasauran mataki khaleel ya tsareshi badon komi ba saidan baison Hanklin halisa ya tashi saboda wann sbauwar case din..

Duk da haka saida hukumar human right ta tsare kawu na tsawon sati biyu akan bazata sake shi ba sai tagama bincike, idan angama kuma kotu za'a akaisa for childlabour amd forced prostitution

gashi Khaleel yace masa muddin halisa ta bada go ahead aka bude case din sexual assault dinta to babu tantama zai yi zaman shekaru masu yawa a gidan yari.

Yace masa shi likitan tane dan haka yana da isasshen takardun da zai bayyana ma kotu dayake nuna cewa she is mentally traumatized and that is also an offence according to law prison kawai zaije.

Tunda aka haife kawu bai taba tsorata a rayuwarsa kamar nayau ba yaci kuka kamar dan karamin yaro, yana neman alfarma amma babu me kulashi, mama G kuma aka bata ultimatum na kawo sheda akan abubuwan data fada wanda inhar karya ne tasani sarai za'a kulleta itama , bayan nn aka saka sukayi signing akan takardan jinyar grace karkashin kungiyar masu yaki da cutar cancer..

suna kammala signing khaleel ya tura ma mahaifyarsa text message kan cewa they are ready...

A mugun razane Aka fito da su kawu aka wuce dashi gidan tsaro..
Chapter 115 · 0% Book details