← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 312

Sashe 149

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

maryam da aliyu suka tsuramai ido da alaman suma sunason ji wacece ita awjnsa dan anan ne suka dan gane cewa kmr itadin watace duba da attention dayawa na media and all the formalities and security stuff. Cikin katse mum dinsa da murmushi yace maama i will tell u, amma not here, har gida zatazo ta gaisheki.

hararsa tay snn Tace yaushe kenan, kasan dai zan iya kiranta personally intanbayeta inji komi dama ai bamu gaisa da ita ba.

Murmushi kawai yay baice komi ba.

Maryam tace hmm maa bafa gaya maki zaiy ba muma haka yamana agidansa wallh

yace tafican 'Toh ita dake daya ne? aliyu ma zai magana cikin dakatar da shi yace ka tashi kawai kakai mama gida yamma yayi yanxu za'a kira magrb in sha Allah Muna zuwa abayanku.

Suna mikewa tsaye maryam tabishi tana cewa "inadai gidanmun duk zamuje ni daku zan dawo. Baice mata komi ba ya karkada kai har suka taho wajen su halisan tare. Sunxo dede lkcin vicky tana insisting on staying with her, suna karasowa wajen cikin sanyin muryan maryam ta mika mata hannu snn tace hi Halisa ta juyo da sakin fuska tace mata "Helo. Maryam tace im really sorry for ur lost miss halisa..hannun su cikin na juna Tace thank u soo much sister.

Vicky this is doctor's twin sister she got my mum's name. Her name is maryam!

hakan da halisa ta fada yasaka maryam ta dada sakin jiki dasu sosai

Da murmushi vicky ta mika mata hannu suka gaisa sukayi ma juna jaje

khaleel yace ma vicky wani waje zasuje yanxu saidan in gobe ta dawo tace babu komi sukayi sallama da halisan cikin aminci.

Kafin 6:30pm taro ya watse securityn hadiza suka rakasu har gida ita da maryam suna zaune a back seat suna magana jifa jifa akan yadda speech inta ya baza koina adan kankanin lkci shikuma waya yakeyi abunsa har suka isa kofar gidansu me gadi yaxo ya bude musu suka shiga ciki.

sama sama halisa ta karema gidan kallo dan kuwa Katafaren gidace me manyan manyan modern duplex guda uku aciki sai wani katoton parking lot an parker hadaddun motoci aciki sun kai kala goma..

Harabar gidan yana da wani irin fadi sosai snn basu da tulin tarkacen flowers amma suna da ire iren decorative exotic trees din nan na kwakwa dana dogon yaro Kowa ina is looking super clean.

Yana kammala parking motar ya bude mata ta fito snn yace musu su shiga daga ciki shi zaije masallaci, daga yay sallahn isha zaizo ya kaita gida ta huta dan yasan ta gaji, Maryam dai nata kallonsu yadda suke maganan cikin kulawa gabaki daya ta rude takuma rasa meyene asali ke wanzuwa atsakansu

khaleel na wucewa cikin masjid har cikin hadadden falonsu dake wani irin tashi da fitinanniyar qamshin turaren meduguri me kama waje da sanyin qamshi maryam ta mata jagora, sosai qamshin ya tafi da imanin halisa hade da sanyin Ac sai takejin kamr ta kwanta anan din kawai tahau bacci, maryam Tay da ita su haura sama izuwwa room dinta amma haka taki fir ta zauna anan ita daya.

Tv maryam ta kunna mata ta barta dashi snn ta haura sama da sauri dan ta rage kayanta snn tay sallah tazo.

Bata wani jima da ficewa
Halisa tay tagumi tana karewa haduwar falon kallo tana lullumshe ido jin yadda qamshin turaren wuta yake kkrin kama mata jiki, can taji wani balammen murya akanta Mai cike da karama da kwarjini muryan tasa a mugun murtuke yace "who ever is der yaje ynxu kawo min four eggs and a coffe, dont waste my time. Yadda ya karashe maganan da comand me cike da kwarjini yasa halisa mikewa cikin sauri

Ta nufi sama inda taga maryam tabi, zama yay akan dinning da wani katoton littafin sharia a hannunsa da alaman baiko kalleta ba, tana kaiwa sama ta rasa ina ne maryam din ma tabi,

gashi tsoro yasaka tabar jakarta da wayarta a falo, saida tay minti uku tana dan zagaye kafin nan ta gano Wata yar yarinya da bazata wuce shekara sha biyar ba amma tana da girman jiki sosai.

Halisa ta sauke ajiyan xuciya thinking she is saved nan da nan ta gaya mata Aikan, cikin takune fuska yarinyar tace tab di? Anty kiyi hkri inkin ganni a lahira kaina akayi, laaa bakisan kawu ba ashe hmm, toh inde bani ya aika ba naje nayi masa shirme wallh zan shiga uku kawai kije ki masa tunda ke ya aika

Halisa ta rasa me ke mata dadi but is just eggs and coffe sumtin of 5 mint, ,Can tace ma yarinyar toh ina kitchen din yake nuna min mana.

Har kitchen din takaita ta nuna mata komi, sai ta shiga cikin sauri taga egg din a sama cikin casket dinsu ta fasa guda hudun dayace ta masa omalete snn ta shirya coffe.

Kafin nan daga fannin Alhj hasheem duk ya sake baki maryam ko yar rikonsa siyama ya aika shi baima lura da wata ba, tvn da halisa ke kallo ne ya dan ja hanklinsa ya aje littafin ya tsaya kallon progrm dinsun da ake nunawa a tv yana kan kallon speech din sai ga nan Aliyu ya shigo tare da khaleel duka suka tsuguna cikin ladabi suka gaishesa ya amsasu ciki ciki batare da ya kallesu ba sabida mugun haushin khaleel din dayakeji.

Hanklnsa ya mayar kan tvn yana kallon abinda halisa ke fada cikin nitsuwa sosai, her name sounds familier to him ya rasa a inda ya santa.

Jefa jefa yake tambayar Aliyu game da event din shike gaya masa Abunda ya afku yace masa ai yar uwarta ce ta rasu yau da ciwon cancer.

Tunda yace ummm, Bai kuma cewa komi ba, sukan su da suke tsaye anan basu san yaushe ya saka sunan nata a wayarsa cikin files nasu na record ya fara yar daddanawa ba, jim kadan ya kamo bakin zaren cos he knws her charity acct is constant, uztaz yana yawan kawo musu abubuwa na alheri da sunan kamfaninta ana kuma sponsoring marayu dashi sosai, marasa lafya da yara yara yan mata marasa galihu dayawa a makrntu, shikansa sunanta kawai ya sani bai taba ganinta aziri ba, gashi irin uztaxin nan ne da bai iya tsayawa karewa mace kallo ba duk da kallon sama sama ya mata a tv aransa saida yace tubarkallah, masha Allah, she is soo young and smart, yay kwafa alaman be yi tsammanin ganinta haka bama, dan ya dauka irin babban mace ce din nan ce kuma musulma, yafi sau uku aransa yana cewa masha Allah da speech dinta aransa amma fuskarsa yadda yake kallon tvn fuska a murtuke bazama kayi zaton he give a damn ba.

Khaleel ya kalle jaka da wayar halisa Dake yashe akan cushion dinsu duk ya dauka ko maryam takaita room dinta ne dan haka baiko zauna ba ya haura sama wajen mum dinsa ya samu lkcin ta idar da sallah kenan tana zaune agaban burner na turaren wuta yana dan dumama mata jiki da qamshi.

Da sassnyar sallama me tafe da ajiyar zuciya ya shigo cikin dakin dan sosai yake son qamshin dakin mahaifar tasa dan har wani nitsuwa qamshn yake saka masa

Da murmushinta me taushi ta tarbesa, Wani peach colour doguwar rigace ajikinta ta yafa mayafinsa dan madaidci akanta wani irin qamshi ke ficewa tunda daga suman kanta har tafin kafafunta dayaji jan lalle. a nitse Khaleel yanemi waje akasan carpet ya zauna yanamai satar kallonta jin tsaftarta na dada burgesa har cikin ransa

Tace ..ibrahim har ka fito? Yace eh mama, ahhm ahmm maa maryam bata leko tanan ba ne? Kulacham dake hannunta take murzawa batare da ta kallesa ba Tace no why? Dan sosa kansa yay yace bangan bakuwata a falo bane so i tot ko suna tare.

Murmushi tay tace ohhh
"Halisa ko? I really want to meet that sweet girl hmm to ka kira maryam din awaya mana kace mata suzo nan tare.

Tsaye ya mike yace aa gara dai naje dakaina na taho miki da ita ku gaisa ko

...tun kan ta bude baki tay magana sai ga nan aliyu ya shigo kamar an korosa, kallo suka bishi dashi. Tace Aliyu lafyarka kuwa? Yana dan zazzare ido yace maa baaba ne fa yace ki zo falo ki same shi yanxu yanxun nan

Gabanta taji ya fadi cikin dakewa tace hmmm ba a samu me masa eggs dinsa ba kennn ko?..

Aliyu yay shiru yana satar kallon khaleel, gyalenta ta gyarawa zama tana ficewa suka biyota abaya

Samun Halisa sukayi tsaye tsabar tsoron idon mutumin hannunta ke wani irin rawa rawa, ta aje masa tray din data dauko egg da coffe kenan agabansa ta tsaya adan tsomare kanta na kallon can kasa.

tun zuwanta wajen ta gaishe sa amma baiko amsa ta ba, Masifa kawai ya mata wai ta kawo mai abinci da guntun skirt gashi bata daura dankwali ba.

Duk da basu san meya faru ba amma Khaleel saida yaji kmar kirjinshi zai fashe dayaga halisa tsaye gaban babansa, a cikin sauri sauri ya iso ta wajen tare da aliyu saiga maryam nan ma ta fito tana sauri, tun daga can tana ganin halisa a tsaye gaban babansu bakinta ya subuce tace innalillhi da sauri ta taho zatay wajen halisan dan ta jawota gefe baban nasu yabita da Wani irin mugun kallo ta tsaya cak saida ta hadiyi yawo.

Halisa ta sunkuyar da kanta can kasa agaban sa kirjinta na bugawa da mugun karfi kamar zai fashe dan akaro na farko dasuka hade ido dashi ma saida taji kamar xata saki fitsari ajiki.

Itade bata dauki masifar nasa a bakin komi ba dake bada tsawa ya mata, ko ya furta shi acikin cin mutunci ba, tasha zama da mutane kala kala and she is quite familier da ire iren waynn malaman addinin tasani sarai basu shiri da me irin shigarsu ta xtians din nan.
Chapter 149 · 0% Book details