← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 312

Sashe 21

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meenal ta wuce mata matsayin ƙawa saidai yar uwan jini dan bazata iya fasalta zafin dataji akan abunda tay mata ba sai taga Abunda zach yay matan ma kamar bakomi bane akan wann sabida sosai take daukar meenal da daraja a zcyarta.

taji ciwo aranta da meenal take ambatar ta da sunan "the dirty girl i picked up frm the street" karuwa, kaskantacca. Yadda takey ma mutane alfahari da cewa itace taimaka ma rayuwarta wani azaban ne ma shikansa.

Sai yau take dada Godewa Allah da bata kashe zcyrta ba, dan Da yanxu ta sake jiki bata tashi ta nemi nakanta ba takuskura ta gina rayuwarta da arzikin meenal da yakenan abunda zai kasance musu oho? halama tou bazata kyaleta ta bushi iskan nunfashi ba seda izininta. tunda aynxu dalilinta kenan dayasaka takejin sam bazata taba iya kyaleta ta cigaba arayuwarta ba.

Tunani take So now how can she repay meenal for the help?? A tunaninta those helps are priceless and divine, ta dauka duk sabida Allah meenal tay mata hakan badan tayi mata kallon kaskantacca nakasa da ita ba, iyakar tunaninta tay tsammnin amana da halacci da kuma soyayyar datake nunawa meenal ya ishesu suyi rayuwarsu cikin aminci. Saidai ba hakan bane, it feels like meenal takes pride in everything, dan haka dolene ta qudurci biyanta bashin temakon data mata a nan gaba.

Tunanin yadda zata biya meenal acikin sauki ya gama cikka kwarlwata..

Tasan tana da kudin da meenal ayanxu haka bata dashi amma inta tambayeta nawa ne farashin temakon data yi mata zai iya jawowa suyi fadar da basu taɓayi arayuwarsu ba cos evrything is gonna turn out insultive and argumentative duk dama zcyarta ne kawai yake zugata tay hakan kodan ta huce abunda takeji.

gashi dazu da safen hankalin ta yayi mugun tashi da ta ga sakon zach kusan komai ma damunta yake gauraye da haushi..

Da meenal bata lakata tsakaninsu da zach ba hala da yxu komi ya kasnce mata da sauki da bata cikin wann yanayin rudanin datake ciki arayuwrta. Her life will have been a mini paradise on earth atare da zach, amma aynxu is quiet the opposite, dan in the process of loosing her trust and love she also lost her biggest friendship journey with meenal .

Hankali kwance khaleel ya kammala yimata kominta atsanake dan hatta alluran daya mata yasha mmki da yaga batako motsa ba...

Iya Wann tunanin datake yin shiya dauketa cakkkk a duniyan nan yakaita wani duniyar na daban banda ruwan Alluran dayay mata yake kashe mata jiki ta ciki babu abunda takeji a sarari.

sama sama tafara jin muryanshi yana magana da uztaz dayay sallama ya shigo dakin yanamai ce mishi.."Dare yay ya kamata ka kaita gida ynxu and lets make sure she have a long nite sleep.. Uztaz ya amsa shi a ladabce, khaleel na ficewa awajen ya nufi offis dinsa, nan ya iso wajenta idanunshi suka sauka akanta tsayawa cak yay yana kallonta ahnkli yace "let me take you home ma'am..
Batasan sanda ta gyada masa kai agajiye ba dan ji take kamar she can't wait to be in her home.

Aranta so take tajita itakadai batare da kowa ba kodama halama zama tayi tunanin me zatayi acikin nitsuwa dan bata jin ciwon komi ajikinta face gajiya da rudani.

Da sauri shema'u ta miƙe ta matso kusa da ita sai ga nan vicky ma ta taso.

jiki a matukar sanyaye halisan ta miƙa musu hannu suka kama ahankli suka rike hanun junansu su ukunsu da wani iriyar kirkiraren murmushi a fuskarta
tace shema and vicky, bazan taba dena baku hqrin sakaku acikin wann yanayin dana sakaku aciki ba wanda nasan badan nay haka ba da bazaku katse abunda ke gabanku kuzauna anan tare dani ba, thank u soo much for being here with me. Hawaye ya ciko idon su duka, da ita datake maganan da sudin da suka kureta da idanu dan agajiye sosai ta furtashi.

Acikin ynyin matukar tausayinta vicky tace

"what ever is going on in ur life is over in the mighty of name of jesus.
Hawayen tabne ya sauko ahankli batace komi ba

Shema'u ta dada rike hannunta tace Halisa we all here for u damuwarki damuwarmu ne, dan haka ni zan tsaya tare da ke until ure ready to talk to us abt him..we dont care how long it will take you amma zamu jira cos zach will not go free musmmn ma da dabbancinsa yay kusan ya rabaaki da rayuwarki.

Hawayenta na zubowa ahankli tace cmn shema dont be ridicoulous this is not even about him bansan sau nawa zan gaya maki ba, or are u willing to wait forever???.

Shema zatay maganan cikin katseta tace shemau kituna fa mijinki mahmud yanacan abuja yana kwance yana fama da jikinshi amma haka kika zabi kizauna anan tare dani cikin nuna min amana da gata..aganina kin bani muhimmacin da harna mutu bazan manta dake ba iyakar abunda zan saka maki dashi shine in shawarceki kije Abuja kikula da aurenki
I promise u bazan sake yunkurin kashe kaina ba,..wata irin kawa zan zamo idan nay sanadiyar da darajar aurenki ya tabu, ive already have enuf traumas...banason nakara da jin damuwr cewa na rabaki da samun ladan aurenki..

Yadda tay magana acikin sauke mata nakasashun hawaye yasaka zucyrta yay sanyi batare da bata lkci ba sai ta haqura ta amince.

Dede nan meenal ta bude kofar ta shigo ganinsu ahaka atare akan halisan suna magana yasaka gabanta yay mummunan fadi da wani irin sauri ta tunkarosu kafarta harna harhadewa ta karaso kusa.. "she.....ma shemau mekukecewa, vic..k y vicky whats she saying? Duk Ɓarin baki da Stuttering din datake yi su duk sun dauka tsananin damuwa da halisan ne ya jawo mata rikicewa da ɓarin baki basusan tsoron kar a ace an furta wani abu da zai jawo tonon asirinta takeyi ba.

Idanu kawai halisa ta zuba mata da mamaki tanata kallon reaction dinta dan itakadai tasan dalilin dayasaka meenal ta rude amma bawai dan ta damu da ita ba

Cikin tarota vicky tace Meenal calm down bawani abu bane an sallameta ne we r just talking about that

Sihirtaccen ajiyan zcya ta sauke snn tace ohhhh okay da daren nan har an sallameta but why..
Waya bada izinin ayi haka ko kune kuka basu go ahead amma ai da an shawarceni.

Shema tamata wani irin kallo ganin irin jiji dakai da kuma isa din datay maganan dashi.

Tace hmm su meenal manya mijinki bai gaya maki komi bane??? i tot kince u had him under ur control... kamata yay a bakinki ma zamuji dalili, aydda muka gani dai its easier said than done ryt karki damu an fahinceki.
Ta karashe maganan with mocking tone.

Atake Meenal din tabi shemau da wani irin harara da zafi zafinta ta hayyako zata bata amsa

Cikin katsesu vicky tace hey hey ya isa haka girls u need to behave.

Ta kalli Shemau dake dariyar meenal kasa kasa snn tace shema be kamata ki gaya mata haka ba, ke kuma meenal be calming down okay lets focus on halisa.

A fixge meenal din taja tsaki ranta a dan bace tace haka kawai sai adinga gaya ma mutum baqar magana dan anrainasa atleast ni ai bana bin bokaye akan dan na mallake namiji kede kyaji dashi shema'u.

Shema'u tay rolling idanunta alaman ko ajikinta daganan sai basu sake maganan ba kowaccensu ta dauke kanta gefe cikin jin zafin maganan da suka furta ma junansun aransu dan sai yanxu meenal ta gane cewa ashe shema'u tana lura da yanayin basar da ita da khaleel yake yawan yi agabansu bayan cika musu baki datakeyi akansa kullum.

hakan ya dada sawa ranta ya dada harzuka ya lalace yay baqi qirin.

Cikin sauke ajiyan vicky tace are we ready to move naga kamar halisa tafara jin bacci....

Sama sama Halisa takejinsu acikin gigin baccin dake fizgarta sabida acikin allurar da khaleel yay mata akwai mesaka baccin aciki.

Muryanta kasa kasa tace its all fine kuje gida kuma ku huta i wll be fine..

Shema inkin isa abuja gobe pls call me naji ya jikin mijinki, and vicky u need to go and plan for ur weding anniervesry okay??? Uztaz zai kira min hadiza..dukan su suna murmushi suka amsata meenal tanata jira taji sunanta ya fito abakin halisa amma sai shiru. Tarasa meke mata dadi sam aka barta daga ta kalle vicky saita kalle shema'u.

She cant belive that wai halisa ta yi convincing dinsu kowacce zata koma harkokin rayuwarta

Abu kamar wasa har suka gama sallama da su shema'un halisa batace ma meenal din uffan ba har bacci me nauyi ya soma kwasarta.

Goma da rabi dede khaleel ya leko dakin da wheell chair da za'a dora halisa akai a fitar da ita

uztaz ne ya amso wheel chair din suka tayashi ya dorata akai yana turota ahankli har suka sauko kasa cikin harabar asibitin inda shemau da vicky suka tsaresa suna masu masa godiya Duk dama haryau polisawa basu fito fili sun fadi labarin cewa shine ya ceto rayuwar halisa daga ruwar ba amma asalin labarin ya bazu wa wasu mutane musmmn wanda suke wajen da abun ya faru, sai kuma irinsu zach da sukejiyo labarin daga source awajen cp na police.

Bayan nan media da duk wani kafafen sada labari ce musu akeyi a group of engineers ne suka ceto rayuwarta acikin ruwan shikansa khaleel din yafi son hakan sabida baison unncessry interviews da publicityn halisa ya shafe hidimar rayuwarsa nayau da kullum dan haryau baisan meyasa mutane suka damu da sonjin labarinta ba.

Shema'u tana kirkiran murmushi tace masa "thank u so much Dr khaleel, uhh we really apreciate ur effort on halisa. Allah ya saka maka da alheri.

Ahnkli Vicky tace kuma munyi farinciki daya kasance kaine zaka cigaba da kulawa da lafyarta atleast we can fully trust u with her more than that doctor strange.

Karamin smirks ne ya kufce masa fuska ba yabo ba fallasa yace its my job ba wata matsala i will do my best in sha Allah.

Basuce masa komi ba Sukayi murmushi mai sanyi.

Shema ta juyo ta dafa kafadun meenal a sigar neman tsokana suna hade ido ta keshe mata da dariya meenal ta wani hade ranta sosai.
Chapter 21 · 0% Book details