← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 312

Sashe 197

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahnkli khaleel yajawo halisa gefe ya bude motarsa ya sakata aciki ta riko hannunsa tana cewa Dan Allah kazo mu tafi, ka kyaleshi kaji kazo kawai mu tafi. Cikin kwantar mata da hankli yace halisa Is my duty to protect u i am just going to make sure he knws dat dan karyana damunki

batace komi ba sann ya dawo ya matso daf dashi suna fuskantan juna cikinsu kowa na huci.

khaleel na nade hannun rigarsa yace why dont u shut me up now befr u receive our weding invitation Naga kamar ji kakeyi da karfi.

zach yana huci yana wani buda kirji, idonsa yay jaa yace in har zanyi fada dakai anan sede na kashe ka amma bazanyi ba sabida nasan akarshe kaine da asara.

Khaleel yay murmushi yace soyayya na da ita babu Asara bbu kuma karshe,..kaifa? U already lost the vry day u left her on that alter..and u still loose the day she found me, i am with her now, bazan taba rabuwa da ita ba ko mutuwa zakayi, I have, and am going to give her everything u fail to give her..

zach ya kallesa a miskilance yace Wow the Arab money is already shakin u huhh? Kana tunanin dan kudin da zaka samu zai saka halisa ta soka ne haha she is not a gold digger, kafin kaga kudi halisa tariga tasan I can buy her the world if i want to.

khaleel na murmushi yace money is all u got?
wat abt values and trust? well, dats not my style, but lets start counting from the undiluted and uncoditional love she deserve that ur money cudnt even buy for her..
give up moron. I am in love with her, and i have acceptd evrthng abt her, including her worse and her past sumtin u cud neva. Kaxo kana wani burgan karya.

Tunda khaleel yafurta masa hakan zach yake wani irin vibrating tsabar zuciyarsa ya harba sama hakoransa har cicxijewa suke dakansu..

A zuciye ya daga hannu zai kai ma bakin khaleel din naushi khaleel yay sauri ya capke hannun nasa ya murdashi baya,

He cant help but to shout in pain cikin haka yake ce masa halisa bazata taba zama da mijin kawarta ba, she is not like any oda woman inma jikinta kake so bazaka taba samu ba, just let me have her i will give u anything u want.. u have no idea wat i am going tru.

Khaleel yace ure also have no idea wat you put her tru..i am just glad u knw wat you loose..ure a coward to think she is for trade i am not stupid like u..she was even ready to die for u..and i wll die just to have her in my life
..It doesnt matter who im married to. In ban aure ta ba kasani kaima bazaka taba samunta ba har abada..

..wani kukan kura zach yay juyi a hargitse ya miko hannu ya punching khaleel a gefen fuskansa bai wani samesa da kyau ba khaleel ya zage ya naushe shi aciki saidai yay tumble akasa yafadi akan hannunsa wani irin mummunan targadewa yay ya rike hannun yana juje juye yana ihu, tuni gayu da yan mata aka fara juyowa kansu sai ganan halisan ta karaso wajensu da gudu ta rike hannun khaleel tana cewa "are u okay? Kafin yay magana tajashi tace lets go, zach na cikin azaban zafi amma jan khaleel datazo tay suka bar wajen batare da ta kulashin ba yafi komi kona masa zuciya.

Kafin su bar wajen mutane sun taru akansa
Karshe security dinsa suka kaisa asibiti sabida dan targadewar dayay a hannu.

Halisa tay tay khaleel ya gaya mata meyafaru saidai yace mata babu komi suka dawo gida ta dauko ice ta zauna gabansa tana matsa masa agefen fuskansa inda yadan tashi kadan kadan.

Tun zamansa anan yake tambayarta abunda zach yagaya mata tana mayar masa, Babu abunda ya kwantar masa da hankli face lura da yay kamr she is not okay itama da bhr din zach din

hakan yasaka ya tursasa mata ta goge lambar sa awayarta sabida court hearing yace lallai saidai hukuma ta shiga mgnn tasaka masa restriction

Bata son wani tashin hankli haka ta Amince bayan sunci abinci sukayi wanka sukaje wajen lawyenta aka rubuta letter aka turawa zach he cud only contact her da permission.

Bayan Faruwar haka khaleel ya fita gari be dawo gidan ba sai can yamma lkcin Wajajen karfe biyar da rabi saura,

yana shigowa gidan yazo ya samu halisa na zaune a falo tana chat da aliyu sama sama tana kallon fashion shows a tv.

Murmushi ta tarbesa Ya zo ya zauna agefenta hannunta cikin nashi ya cigaba da amsa wayar sa wanda daga jin yadda yake maganan tasan maryam ce.

Yana kammala amsa wayar ya juyo kalleta a gajiye yace Bbygirl ki shirya mana muje wani waje zan amshi sako ne and we won't be long bari naje na shirya ko

Tace okay..
Nan itama ta tashi ta haura sama ta gyara make up din fuskanta snn ta saka straght skirt lavender colour da kuma cotton shirt dinsa snn ta dauki wani expensive gucci kimono fari kal dashi sharara ta saka kayan bakaramin kyau yay mata.

Dama kuma already ta tattara sumanta sama tay chuku dashi farin veil dan karami ta yafa akai ta saka wedge me tudu iri daya da lavender side bag dinta ta fetsa turare snn ta wuce kitchen ta dauko box of cup cakes da milky donuts ta zuba a boxes, ta bude warmer ta juye chicken ppr soup dake wani irin mayyar qamshi a wani hadadden warmern Amina talba dayaji kudi, da ginger juice datayi shi a katon transparent bootle, yau mummyn khaleel zata dawo daga wajen siyayya a Dubai tanason suma suje sugaisheta tare duk dama dai bata gayamai ba already aliyu yagaya mata cewa yaje aiport dauko ta yanxu.

tana fitowa da basket dinta riki riki sai ga nan khaleel ma ya sauko cikin shigarsa datay kama da na sabon ango yana wani irin baza qamshin kyelien love da zebra rasasi me azaban sanyaya rai da saka nitsuwa. Wata kalar milk colour yard ya saka me fallasa tsafta gata nan sharara jumfar data masa cas cas ajiki taji wata sassnyar aikin wuya da hannu yabi ya saka coffe meduguri cap da coffe colour agogo da bakin half shoe na Masimo dutti simple and stylish...halisa nata kallonsa can ta kyabe baki tace hmm Mr milk and honey wann wankan duk na karban aikan kenan? yace malama banda sharri dai kice nayi kyau kawai awuce wajen, Dariya tay tace tab baka min ba nide. Da gefen idonsa ya kalli basket din dake hannunta cike da abubuwan data debo yace malama wann fa? Ba yabo ba fallasa Tace na mummy ne. in munje wajenka sai muje nawa.
..hmm kawai yace ya girgiza kansa baice komi ba har suka fita agidan suka shiga car dinsa wata dunkilliyar lexus jeep me kyau, suka dau hanyar wani sabuwar anguwa suna hira kadan kadan tana masa video da wayarta dan sosai yau din yay mata kyau.

Ana daf zaa kira magrib suka iso wani waje da akayi babban taron bude wajen cin abinci da alama angama taron mutane na dan watsewa

khaleel ya rage Speed din motarsa suka fara tafiya ahnkli saida suka kusa isowa wani babban gida snn ya dube halisa yace " Babygirl aje cameran nan ki saurareni pls.

..Saukewa kasa tayi snn ta tsura masa idanunta yay murmushi yana kan kammala parking snn ya dubeta yace "I want u to meet sumone..ya ciro ivn da maryam ta kawo mai a office jiya ya mika mata ta karba taga an rubuta opening cermony of Batul's cakebury..

Tace ohh ko shine hidiman da akeyi anan naga taron mutane?

"Yace yeah..kafin ta furta wani abu sai wayarsa ya fara ringing ya ciro daga aljihunsa yay sallama maryam tace har ka ison ne to ai Yaran gidansu ma har sun gaya mata tace min tana fitowa.

tun be amsa ba ya hango wacce sukazo wajen nata sanye da plain abaya baki kirin tana fitowa da bby dan karami a hannunta, Yace its okay..nama ganta..

Mryam tace okay be nice pls..ya katse wayarsa.

Yana juyawa yaga Hankalin halisa tini ya koma kan babe din dake tahowa dake ire iren fararen matan nan kyawawa, tsririyace sosai tana tafiya kamar zata karye da babynta dake mugun kama da ita a hannu.

Hannunta taji ya kama ta dan farga ta juyo yace hey ga bakuwarmu nan tana zuwa..batare da kulawa sosai ba halisa tace okay..is She ur cousin? Ahnlkl yace no, My ex..da wani irin sauri yaga ta juyo ta kallesa yace meye kuma na hararata kinsanta ai.
itace wanda baba ya hanani aurenta aka aura mata wani..halisa tace ohh toh why did she invite u here. Naga kamar hidimarta ne ko

Yace yes, irin alkwarin nan ne ta masoya it was her dream to open this cakebury.. her only wish is for me to attend and have a bite. halisa tace uhmm okay..gashi ai ta iso sai kaje ka sameta tana fadin hakan ta dada gyara zamanta a motar.

Ya dube ta yace haba madam muje mana tare meye amfanin zuwanmu in zaki barni nikadai.

Tana tura baki cikin mita tace ai bakace min gidan budurwanka zamu je ba

Yace toh sorry sauka muje pls..cikin kasala da yauqi tace ka sauka nide ka budemin kofa hannu na na ciwo..

yana murmushi yace hmm toh as i wish ur majesty..haka ya sauka
Banda kallon yarinyar ta glass babu abunda halisa takeyi the girl is indeed very gentle and pretty tsiririncin ne kawai ya batata amma irin pure and applied fulani girl din nan da iyayensu suke da kudi sosai. Halisa nata lura da duk wani kalar yanga da murmushin da babe din take aikowa ma khaleel daga nesa da alama ta daula shi dayansa yazo

Daf da isowarta taga ya fito ya bude ma Halisa kofar mota ahnkli ta sauko kasa ta tsaya daf dashi lkcin yarinyar ta tsaya cak tana dan satar kallon halisa daga bisani ta karaso cikin sanyin jiki.

Kanta na kasa tace salam alaikm, noorl qalb
maraba da isowa..
Chapter 197 · 0% Book details