← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 312

Sashe 68

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiyasa tunda ya dawo da ita gidan suke video call suna tattaunawa suna kuma reviewing files din atare dan babu wani abu na kamfanin da ba a turo musu ba harma da cigaban da suka soma samu sakamakon rikewar da zach ya masa na dan wann lokcin dan sosai ya jajirce ya tayar da kamfanin snn ya dora mata manyan manyan mutanensa masu kudin gaske from all over the world su goma amintattu acikin share holders din kamfanin duk dama kamfanin sabo ne.

Shiyasa daga zarar mutane sun ga list din holders din suke razana sabida kowa yasan daga sun fara aiki kamfanin zai iya tashi a bugu daya....
Halisa tay shiru hanklinta nakan system din sai ga nan Meenal ta karaso cikin dakin tana tafiya cikin rangwadi hartazo ta zauna kusa da Halisa tanamai dada kallon kyallin da gabaki daya fatar jikinta yakeyi "Hey babe..u look soo Shiny halisa ta mata kallo daya snn ta dauke idonta akanta batare da tace mata komi ba.

Dada gyara zamanta tay tanamai karewa sabuwar gyaran gashin datay kallo yadda ya kwanta yay luf luf yay baki kirin, kusan a bazata tace "woww nan ta dora hannunta kan hair din halisar Tana shafawa ahankli jin sassanyar qamshin turaren dake fita daga jikintan gabaki daya ya saukar mata kasala ajikintan tabi ta lumshe idanunta tanasauke ajiyan zuciya me sanyi

Juyowa halisan tay fuskarta babu yabo babu fallasa ta kalleta snn tace "Hows work?...

..meenal ta bude lumsasshun idanunta cikin jin dadin amsata da halisan tay tace"work is fine, komi lafya...Am Really tired na dawo da wurine ma dan na dubaki kinsan tunanin jikinki ya kan hanani sakat a office..

..shiru halisa tay batace mata komi ba ta cigaba da danne dannenta cikin nitsuwa batare da ta kalleta ba..

bakinta ta kyabe snn tace "toh ya jikin kin ..oh gosh babe u don't even look sick anymore ki kalleki fa kinje spa ne?

Idanuwan halisa na kan computerta bata amsa ta ba dake tana hankalce da duk wani motsinta dan bata son meenal din talekota cikin computer bare taga abunda takeyi.

Uztaz dake ta dayan bangaren najinsu baice komi ba ya kure halisa da kallo aransa ya jima yana mamakin yadda ta sauya yanayinta wa meenal sosai abun har yana damunsa aransa shima..

Minimizing din meeting din nasu tay, Tana daf zata rufe kuwa caraf meenal din ta miko hannu zata amsa tagani duk a tunaninta game halisan takeyi shiyasa batason amsata da wuri

cikin katseta da kallo halisan tace "its alright Amina, You need to go. Ai mun gaisa ko..ni bacci nakeji.

Meenal Tamata wani irin kallo snn takyabe baki slowly tace okay ba matsala, i bot u food sede babu yaji aciki sai ta bude jakarta ta fito da yajin ta aje kusa da ledar abincin, Halisa bata ko kalleta ba tace okay.

Ficewa tay batace ma halisan komi ba jim kadan ta dawo da plate da spoon ta bude abincin ta zuba akan plate duka lura da tayi da cewa halisan bata kallon abunda takeyi yasata ta barbada yajin akai me yawa ta gauraya sosai saida ya sauya ma abincin kala ya zamo jaa.

Tana gamawa ta rufe kirif snn tace "Here is ur food.

Halisa tace Amina na koshi kicinye abunki ko ki aje wa mijinki kawai thanks bacci nakeji..

Dadi taji aranta dan tasan dama halisa bazata ci abincin ta ba,

da mamakin halisa taga meenal din bata wani damu ba instead ma tasaka hannu ta dauki abincinta ta rike tana murmushi me sanyi..

Okay ba matsala i dont want to bother u pls rest. Zan kai ma khaleel yaci amma fa zance masa kece kika bashi dan yasan ban iya irin wann abinci ba kin amince?

Sounding unintrested da maganan halisa tace do whatever u like gudnite.

Da murmushi meenal ta fice a dakin. Halisa taja karamar tsuka snn ta bude computerta ta cigaba da magana da uztaz abunta Batare da ta saka komi aranta ba

Tunda meenal ta fito da abincin bata wuce ko ina dashi ba sai dakinta, aje abincin tay akn table snn ta shiga wanka after few minutes ta fito ta kimtsa kanyaa snn ta saka wata doguwar floral gown green and white marar nauyi yau bata tsaya shafa komi a fuskarta ba ta fito tare da abincin har izuwa falo ta aje akan dinning ta nufi sashensa agurguje.

Isarta kofar dakin ke da wuya sai gashinan sanye da jallabiyarsa yana kkrin fitowa daga room dinsa

Tun daga can ta sakar masa murmushi me taushi ahankli ta kira sunanshi ta juyo yana kallonta da mamakin ganinta anan din

Tana murmushi kamar abun arxiki ta taho tace "Khaleel your food is ready..come come..let go downstairs..ta riko hannun shi cikin nata da karfi ya fauce ya dubeta

"Yace what?

A Jikinshi ta larne slowly tare da riko arms dinsa tanamai shakar dadddar qamshin turarensa daya shafa ta guilty absolute tanamai sakar mai wata makirtaccen Sautin shagwaba tace baby ai kaji menace..yay rau da idanu kafin ya bude baki harta fara jansa kasa izuwa inda ta aje.

Meenal stop dis nonsense bana son wasan banza bata ko kulashi ba Kusan zaman dole ta saka shi yy akan table din snn ta bude mai plate din tana mai sosa mai tsakar kansa da zuka zukan nails dinta baby Pls don't say no to this food, Halisa ce ta girka kuma ita da bakinta tace min na kawo maka kaci..

Tsabar mamakin jin hakan kasa iya cewa komi yay ya kure abincin da kallo...

ganin ta fara zubawa masa a dayan plate di yasaka ya riko hannunta meenal kibari kawai ni na koshi, i cant eat dis, It even look pperish kinsan kuma banason yaji..

Har zai mike tay saurin dawowa dashi kan seat dinsa a shagwabe haba khaleel kaifa ba'a abun arziki dakai...i knw u dont like her.. but jinya fa kukeyi kamata yay ace karkana yin abunda zai sata baqin ciki tunda ita tace inbaka kaci kawai kaci..

Wani tuwon harara ya watsa mata "dan tace naci sai naci what do u think i am a toy? ke nace miki na koshi ko ana dole ne

Da sauri ta shagwabe murya cikin tsareshi lallami ta cigaba da shafashi sosai Okay naji just do it for me plsss Ko kadan kaci i dont want her to feel bad haba khaleel. She is my best friend inbaka sonta ni ai ina sonta..do it for me pls kay baby.

Shiru yay ya shareta, jin magiyan yaki ci yaki karewa yaji kansa na neman ya masa ciwo badon son ransa ba yace okay fine.. i will try for ur sake.

Lumshe ido tay ta bude tana murmushi sosai
"Yeeey, thanks. Bari na zubo maka..

Yaja tsaki ahankli harta gama ta debo mai uban yawa a spoon takawo setin bakinsa ya dinga kallon abincin yadda yay jaaaa tsabar yani barkwano ga kuma turirin zafin yaji dayake ji aciki

"Kikace wann abun ba yaji bane?...

Trust me babe..bazan baka abunda zai cutar dakai ba beside na gayawa halisa cewa bakason yaji, so she is quite aware.

Qamshin abincin already ya gama cikashi dum dama yana dar dar Yace okay ko bismillahn bata bari ya karasa ba ta tura mai abincin data debon duka abakinsa, a tauna na farko yaji bakinsa ya dau zafi kamar an jona masa wuta.. da wani irin mugun yunkuri ya tofar da abincin waje. Ya rike bakinsa fuuuu fuuuuuu.

Da kyar Innalillhi ya kufce a bakinsa inna ilaihi wa inna ilahi rajiun what the fuck is this meenal...

Tamkar wacce bata san komi ba atake ta rude ta fara rirrikesa what? Meya faru khaleel are u okay

Tari me karfi ya kufce masa, ta rikito masa ajiki bakinta da jikinta har na rawa tana cewa khaleel lafya? Meya faru. what is happening

Tulin abincin data tura masa abakinsa bana kadan ba kafin kace wani abu zafin barkwanon ya haura har kansa yana masa wani irin zugi me radadi ajiki.

Sai dabur dabur meenal take agabansa na makirci dagangan taki ta zubo masa ruwa duk dama taga idanunsa yay jaaa ya fara tari me karfi.

"ohh my god khaleel...
Sai daddafa shi take tan bari yanata mata hannu ta miko masa ruwa tay kamar bata fahimce meyake nufi ba.

Halisa..halisa...halisa pls come down ta kwala ihu kamar irin barawo ya shigo musu dinnan..

Halisa tay sallama da uztaz kenan tana kkrin rufe computerta taji ihun meenal duk sai taji ta tsorata atake ta fito sanye da rigar baccinta me duhu bata saka ko takalmi kafafunta ba.

Tun daga can ta hango yanayin da khaleel yake ciki haka kawai taji krjinta ya buga da karfi da sauri ta karaso ta wajen su ta tsaya daga stair sann tace "What happen?

Da makirtaccen rudewa tare da bacin rai meenal ta kalleta " look at his conditon girl i dont knw what is in this food da kika ce na nabashi yaci kiga abunda ya jawo he is in pain

Innocently halisa tace
Is that why u call me hmm toh Meyene acikin abincin? How is dat my...

Da sauri ta katseta dan karta karasa maganan yaji, kusan a rude tace I dont knw, ke kika sani tunda kece kikace in bashi yaci..

Halisa ta rasa meyene meenal take nufi da kalmomin nan nata Dan Magana take fiddawa kamr irin bata cikin hayyacinta nan ganin ga khaleel din yana tari sosai a dame tabi ta dafashi da fuskar damuwa' khaleel yajin ne ko? Ya dago da kyar ya kalleta muryansa bai fitowa sosai yana cewa water water amma tay burus tay kamar bata gane yaren hausa bare turanci.

Ya kasa tashi sabida tattareshi da tayi, tayi bankama ta gabansa ta damkeshi a kafadunsa sosai ahakan Ta kalle halisa tace babe Inaga yajin nan ne wallhi.

Halisa batace mata komi ba dan sosai ya bata tausayi ganin yadda ya rikice lkci guda idanunsa sukayi jaaa ga tari me karfi dayaki daukewa sumtime allergies are the most torturing ilnesses saidai na wani ne yakan fi na wani hatsari..

Khaleel Zai iya ci maka yaji normally amma daga zarar ya wuce misali to wani bin sai yay kwana biyu yanajin zugin abun akansa da bakinsa wani bin har sai yay zazzabi.
Chapter 68 · 0% Book details