← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 312

Sashe 67

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meenal na tafiya a hankli ta fito daga inda ta dan boye dan duk shure shuren su da nishi da gurnani duk ta ji

Suna hade ido da mahaifyarta ta bata rai tabi ta harde fuska tana jajjan mata tsaki..

Ko kulata batayi ba ta shareta uban me ma ya kawoki gidan nan by this time is evrything alright?

Cikin matsanancin fushi kuma a hatsale meenal tace mumy uncle tjay?
Uncle tjay fa wann kazamin wawan haba mumyy ure such a disgusting big slut..
acikin karuwan ma ke karamace wallhi..

Da sauri hajya nadiya ta wanka mata mari with utmost i dont care face najin sunan sata ambaceta dashi...

Meenal tafara kuka mummy marina fa kikaya?

Tsawa ta daga mata cike da bude mata idanu..
"Be Quiet...we are not going to have this conversion Amina, ki fita aharkan rayuwata kiyi abunda zai ficce ki, nima zanyi duk abunda naga zan iya da rayuwata nidin dakike kira da mugayen sunaye nina kawoki duniya. If am a slut then ure the only doter of the slut.

Meenal Kamar zata fashe tace mummy amma....

Shut ur trap nace miki
My sexual life is none of ur concern..nace meya kawoki? Inbazaki fada ba kifita min agidana duk kinzo ki katsemin jin dadi wallh amina baki da imana baki da tausayi tunda ubanki ya mutu kin taba tunanin ya nakeji da sha'awar dake jiki na? Ko akace miki ni ba mutum bace...

Hawaye masu tsananin daci suka kufce wa meenal dan ita ba zinan bane damuwarta uncle tjay fa..uncle tjay? Aiko da mmumy zatay ta nemo dede da ita amma uncle tjay da baida komi na arzikinsa sai arzkin katon bura? Mtsww.
Wayasan ma tun dady yana raye mummy take harin mutumin nan.
Ta gama raya hakan aranta saann ta y hakuri ta danne maganan ta wuce kitchen fuuu ta debo ruwan sanyi dan tasan in mumynta zata kawo namiji gidan toh korin masu aiki takey for some hours, meenal na dawowa ta samu hjya ta haura sama yin wanka.

Zama tay a falon tana shan ruwan zucyarta cike da takaicin kusan komi ba.

After a while sai ga hajy nadiyar ta fito sanye da wata doguwar riga ta babban holland atamfa ce blue colour bbu wani kwalliya me yawa ajikin sa.

Tunda ta zauna meenal ke sha mata qamshi kusan ince da kyar ta shawo kanta dadin karin abunda yasaka ta kira business patner dinta na vegas kenan suka dan tattauna akan matsalolin da meenal din take fuskanta da kamfaninta.

Bayan sun kammala wayar ta dafa kafadun meenal cikin rarrashi my Baby karki damu ai kinji sunce nan da sati biyu zuwa uku za'a yi juye akan game din sai ki samu shiga ciki snn any amount kika samu zaki iya dawowa da contracts dinki tunda dama kudin ne damuwar su..just relax, its gonna be a win win. Hakuri kawai zakiyi na dan wann lokcin kinji meenalyn mummy?

Cikin sauke ajiyar zucyar meenal tace toh naji mumny i wi try my best amma kinsan hanklna bazai kwanta ba har sai naga naci riba akan game din nan ko????

Hajya tay dariya With confidence snn tace Zaki ci riba mana, nina fada miki..ure my doter fa
U will neva fail.....

Meenal tay murmushi..
Relaxing kanta tay akan cushion suka cigaba da tattaunawa akan sauran business dinsun suna sharing ideas akan kudin dayakamata su saka a farkon game din dansu samu isasshen riba akai.

Altho meenal din akwai wayo, duk da influence din mum dinta aksar ranta tana baya baya tana son tagani akaro na farko in tay nasara sai kafin nan ta sake jiki da game din sosai.

She need this money fast and desperately kodan ba dan tay controlling rayuwar khaleel ba she need it for her confidence tun kafin mutane masu daraja su fara jan baya dayin harka da kamfanoninta dan ita kanta tasan da bazarsu take taka rawa.

Anan gidan mumynta ta huta bata koma office ba bayan waya me tsayi da suka sha da shema'u marafa.

Bayan dan bacci da tayi daga bisani da yamma liss suka fita cin abinci da dan shakatawa tare da mummynta.

A wani open luxury restaurant suka zauna hjy nadiya tanata mmki sanin cewa sam meenal batason zama a wajajen sa are below her standards.

Suna kan cin abincin hajy nadiya ta kalleta da mamaki Ganin ta bada sabuwar oder na fried rice da chips da pper chicken take a way

Cikin tabe baki tace ikon Allah meenal i dont understand..

Meenal na murmushi tace menene mummy

Hajya Tay kwafa Aah naga baki son wani restaurant ne sai chinese yau kuma saigashi kin kawomu wannn wajen and whats up Baby me zakiyi da Abinci haka da kike packging?

Tanakan murmushi tace is for my husband from my best freind.

Hajy nadiya tace ohhhhh plan din nan ko? Tun meenal bata amsa ta fashe da dariya sosai saida meenal din ma ta tayata sukayi me isarsu..

I reserve my coment gobe da safe kiban labarin yadda aka kaya kawai..

Meenal tace kisha kuruminki mummy.

Bayan hakan basu wani jima ba aka kawo mata odernta suka bar wajen hjy nadiya ta koma gidanta meenal ma ta doshi hanyar nata gidan.

9:00pm dot ta iso me gadinsu ya taho ta bude mata gate ta shigo tay parking motar yanata mamakin ganin ta sanin cewa bata saba dawowa gidan da wuri haka ba..

Jira yay harta sauko kasa da ledar abincin a hannunta kansa kasa cikin girmamawa yace
Hajiya barka da dawowa.

Bata amsashi ba har saida ta kulle motarta snn ta juyo tanamai bin sa da wata kaskantaccen kallo..

Nan da nan ta hade rai tabisa da masifa why are u speaking to me? Bashi kake bina ne ko me???...

Kansa kasa yace a'a, gaisuwa ne dama.

Gaisuwa my foot maye kwadayayye. Kaga abinci a hannuna ai dole ka gaishe ni, abeg getttat.

Shibaima lura da abincin bama saida ta fada baice mata uffan ba ya juya jikinsa a sanyaye zai koma bakin aikinsa tace "kai.. Juyowa yay not minding how she call him aladabce yace naam hjya.

Harara ta banka masa up and down kamar wanda take gaba dashi, mtsss jibeka ko kunya bakaji, ga rashin ilmi ga rashin, tarbiya ga tsantsan jahilci dumu dumu ajikinka, wani rau da ido tay ta harkuzo shi da masifa kamar ma zata wanka masa mari taja tsaki mtsww... "ya ina maka magana kana tsaye ni sa'arkace da bazaka tsuguna min ba ?

Baice komi ba ya tsunguna kansa na kallon kasa jin maganan nata na masa ciwo aransa bama wasa ba

Tsaki mei tsayi taja ganin yakai ma ya haifeta a shekaru Sanda ta dan ja lokci snn tace."khaleel yadawo?

Yace a'a hajiya bai dawo ba dan bai jima da ficewa bama.

"Ehen, Ya gaya maka inda zaije ne?

Ya dan jinjina kadan yace
Eh to amma yace min dai yanxu zai dawo

Good tashi kaje...

Baice mata uffan ba yabar wajen tabishi da kallon banza kafin nan ta dauke kanta ta shige ciki

Dakin Halisa ta nufa straigth just to make sure she is der dan plan dinta ya tafi dede...

Ahnkali ta turo kofar bata iya motsawa ba ta tsaya cak kamar an dasata tanata kallon halisan daga nan Ganin yadda tay wani fess fesss fatar jikinta yay smooth yana mai baza kyalli ga wata qamshin body mist na musammn kamar an mata proffessional wankar amare.

Tun daga kan suman kanta har izuwa kan yatsun kafafunta meenal take kallo dan kuwa abun kallone dan sun sha gyarane na kece raini
Kamar ka saceta haka nan fuskarta yay haske yana wani irin fidda kyalli mai daukar hankli.

Lkcin halisan na zaune akan couch da system dinta akan cinyarta tana cooperate meeting da uztaz akan sabuwar boyayyar kamfaninta datake shirin budewa wanda bata sanar ma kowa ba daga shi sai ita.

Altho it has to do with tsohon saurayinta zach shiyasa bata fayyace maganan kwata kwata wa kawayenta ba.

Kamfanin na daya daga cikin investemt dinta dashi,wanda suka fara a kasashen waje lokcin suna tsaka da soyayyar su,duk dama da kudinta ta bude bada nashi ba saidai shidin ne dai yake rike mata komi yana kuma processing mata validation forms da sauran formalities na kamfanin kafin nan har aka zo lkcin da maganan aurensu ya ruguje da ganan kuma sai bata kara neman takardan kamfanin awajensa ba.

Bayan rabuwarsu halisa bata damu da dukiyarta dake wajen zach ba duk dama uztaz yay iya bakin kkrinsa dan yaga ya kwaco mata but all to no avail lkacin zach yana cikin wani yanayi yaki sam ya saurareshi bare ya basu takardan.

Infact alokcin labari sukaji cewa har yay lounching kamfanin yana amfani da ita a kasar spain under his name.

Tun lkcin Halisa tace ma uztaz su kyaleshi dashi kawai batason ta tarowa kanta wani fitinan akan dukiya.

Har sun hakura sun mance da zancen Saiyau kwasam tana wajen gyaran jiki taga sako a email dinta ta bude taga jerin sunayen officiating members na zachs industries wanda sune suka turo mata letter da yake nuna cewa She is still the owner of that construction company da zach yake running a spain.

Snn Daga rana ta yau duk wani activities na kamfanin zai dan dakata
Harnan da wata guda dan itadakanta ta samu isowa, ko ta turo wani delegate dinta domin acigaba da running business din acan kamar yadda aka saba dan yanxu haka kamfanin nata na cikin list din sabbin kamfani wanda ake ganin za'a gwabza dasu sosai.

ita tun bata gama karanta sakon bama ta rufe ta ajiye, dan dama kamfanin ya riga ya fice mata arai sabida bata kaunar wani abunda zai sake hada ta da tsohon saurayin nata zach musammn ma abun da yashafi kasuwanci.

Duk dama tana cikin damuwa Aranta jitake kmr ta yafe masa duk abunda yayi mata musmmn ma daya kwatanta neman gafararta kwanan nan amma bata son wata alaka ta hadasu sam sam.

She is not reallly intrested in the whole thing amma haka uztaz yazo ya tursasata akan lallai sai ta duba takardun bayanai da suka turo mata a nitse tunda kamfaninta ne bana wani ba...
Chapter 67 · 0% Book details