← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 312

Sashe 100

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin har karfe goma na safe yay bai fito ba yasaka ta fara tunanin kiransa a waya ko hala harya wuce office ne bata sani ba,wani zucyar yace ta kira wayarsa.

Aikuwa batay kasa a giwa ba ta dau wayarta ta kirashi kusan sau uku na ringing bai daga ba sai can ana hudun ya dauka tunda ta shako muryansa tajishi wani iri taji gabanta ya mugun fadi...

Hanklinta a tashe take tambayarsa mahmud lafya kuwa naji muryanka haka? Kana ina ne..

Yana da kunya sosai dan haka Bai iya gayamata abunda ke damunsa kai tsaye ba yace mata yana dakinsa yana kwance...

Tana katse wayar tayo wajen agaggauce tazo ta sameshi akasa akan dadduma jikinta na rawa rawa da fuskar razana da damuwa ta karaso ta gabansa tana me tambayarsa menee ke damunsa, dakyar yake magana yana ce mata cikinshi cikinshi duk sai taji ta rude kan kace waa
ni abu tafara kiraye kiraye..

Tana tsaye akansa Har akazo aka kaisa asibiti aka sakamai ruwa bai gaya mata abunda ya samesa ba sanda likita ya fallasa snn shi mahmud din ya daure ya hau mata bayanin cewa wani abinci yagani a kitchen jiya da dare ya dauka yaci.

Salati tay tana tuna ashe ma abincin shemau ne data ajiye akan da safe zata zubar dashi ma dabbobi.

Aikuwa kamar an kunnata, duk da yanayin dayake ciki bai hanata tsilleshi tass ba, tacemai duk shine yakeyim sanya akan lamarin shemau amma ace abinci na rana daya kawai datay saida aka hada da gadon asibiti? Hmmm toh ai ka gani dama kasheni zatay da banciba shine ya fada akanka tunda dama kaine me daure mata gindi..toh wallh karyanta ta kasheka bare kumani mahmud inkai bakason kanka ni inasonka, bazan yi wahalar daukar cikinka na kawoka duniya abanza wa wata yar banza tazo ta kashe min kai ba...

Hajiya badiatu ta inda take shiga bata nan take fita ba. Abun yabi ya ishe shi, bayan ciwon yay sauki ya lafa masa, daga asibitin ya kira shemau yace mata yanason ganinta amma tay burus bata yarda ta dawo gidan ba sai can da yamma kusan bayan ishai.

Lokcin ya fito daga masallaci kenan suka shigo cikin gidan tare tana huhhura hanci tana gatsine..

Tun daga babban falonsu sukaci karo da hajy badiatu na zaune fuskrta kamar bata taba dariya a rayuwarta ba, anan aka zauna yin sharia ta inda hajy take shiga bata nan take fita ba, dama can wann daman take nema da zata fidda abunda ke cikin ranta gaban idon shemau dantasan sun gaji da hqri ita akan dansu sosai.

wasu irin baqaqen maganganun ta zage ta gaggaywa shemaun babu sani babu sabo..

Kuma ba acikin balbalin masifa take maganan ba, ba akuma cikin sanyin nama ba, yin maganan take da dattako da nuna nitsuwar dayake cikin yawan shekarunta.. acikin ruwan sanyi take fiddasu manya manya

Lafuza masu cin rai da shiga jikin duk wani dan adam me busar nunfashi ita kanta shemaun sede tay hawaye dan babu inda yafi ci mata rai kamr inda hjy take ce mata

Ke ba yar uban kowa bace yikowar kashi nasan waye ubanki na kuma san uwarki ciki da bai, Dama ace bamu san asalin balbale bane da sai anuna mana farin kai ganan mahmud ki tambayesa kiji wallh nida ubansa sam bamuso ki kasance matarsa ba shine yace mana yaji yagani yanaso mukabar sa. Toh kisani alfarmar hakan ne yasaka mukayi shiri muka zuba maki ido badon kin isa ba.

kin taso gidn ubanki kina girki, kina wanki, kina kuma ibada sai auren dana ne zai sauyaki dankin raina mana wayo???? Toh Tir dake shemau..sam Albasa batay hannun ruwa ba, da can dana hadu da mahaifyarki naga tarbiyanta na dauka ke din yar mutunci ce hala zaki rikemin dana amma kincuci Uwarki shemau dakika dau rayuwar karya kika dorawa zuciyarki kina wasa da aurenki kamr ke ba yar musulma wanda iyayenta suka bata lokci wajen baki tarbiyan addinin islama ba.

Toh wallah Baki isa ki kashemin dan dana haifa ba kin yi kadan...banda ma qaddara mahmud ai ba sarar auranki bane..

Ta juya kansa shima ta wankeshi tacemai baida zuciya ya bari ya kare ya dauka akan shemau..
..tace mai tura yakai bango tun zancen lafyarsa ake shikadai ta haifa bazata lamunci abunda zaizo ya rabata da danta kwalli daya ba

Agaban shemaun Tace masu kwana biyu ta bashi inhar bataga canji akan dabiun shemau ba duk hukucin data yanke masa karyaga lefinta yaga lefin kansa daga nan ta tashi tatafi ta barsu awajen dikkansu babu wanda ya iyayin motsi.

Kuka shemau ta dingayi kamar zata fidda ranta bawai dan nadama ba gani take lefinta ne data auri mahmd tazauna har wata gidahumar local tsohowa take mata zagin tas tasssssss...but enuf is enuf..yaune karshe!!!

Mahmud na shirin mata magana yaga ta mike tsaye kuma a mugun fizge kamar wata me aljanu ta haura sama tana shiga room dinsa ta kulle kanta ciki ta dinga kuka dan tasan dolene hanklinsa ya tashi sosai.

Tanajinshi yazo bakin kofar yana bugawa yay magiyar duniyan nan danta bude mishi suyi magana amma shemau bata tankasa ba barema harta bude masa..

Hakanan har ya gaji ya hakura ya kyaleta aciki karshenta a masallacin gidan nasu yay barci cikin damuwa da tunani.

Washe gari ana idar da sallahn fajr sassafe ya dawo cikin gidan ya nufi dakin mahaifyarsa da tsammanin zai lallasheta tay hakuri ta dena fushi amma koda yaje sai yaga itama ta tsananta bacin ranta, kwata kwata yau bata kulashi ba.

Dan gaisuwarsan ma da kyar ta amsa masa snn tun nan bata sake tanka masa ba bata kuma sakemai fuska ba, jikin shi a mugun sanyaye ya fito ya rasa abinda yake masa dadi.

Hanklinsa a tashe ya dawo wajen shemau da kyar ta kammala wayar datakeyi da alhaj shafiu kafin nan ta bude masa kofar ya shigo ciki.

Yana mata magana ko kulashi batay ba saima tsabagen baqar magana data dinga jefa masa daddaya...

A wann yanayin ya shirya yaje wajen aikinsa duk hanklinsa ba kwance yake ba da yanayin yadda yabarsu a gidan kowaccensu tahau dokin zuciya.

Abubuwa sun masa yawa aransa adan dolensa yau ya nemi shawarar Abokinsa duk dama bai mayar masa komi baa amma abokin ya jadadda masa cewa abinda ya dace yay shine ya saka shemaun agaba suje har daki subawa hajyarsa hakuri.

Wann shawarar dama tuntuni tana ransa Ynxu Babban damuwarsa shine yadda zai sako shemau agaba duba da irin izgilin data tareshi dashi da safe

Adan dolensa yay ta maza da yamma bayan ya dawo yazo ya samu bata gidan, tun safe ta fita tare da driver alhaj shafiu aka kaita aka mata visa na zuwa United kingdom akan zataje ta sameshi acan gobe.

Bai sani ba shemau ta riga ta shirya tarkon da zata kamashi dashi wanda take saka ran shine zai kawo silar rabuwarta dashi dan harga Allah bazata taba daurewa ta zauna dashi ayanzu ba, musmmn ma da uwarsa tafara saka ido akan auren nasu batason case din yakaiga iyayenta bare ajawo asata zaman auren dole agidan mahmud.

Ji take kmr in haka ya faru zata iya hadiye ranta ta mutu cos She just cant commit to him no matter what dan tafara son alhaj shafiu aranta sosai snn babu komi aranta game da mahmd din aynxu face nadaman aurensa datakeyi tun farko..

Hakanan mahmud yayta jiranta harta gama shirye shiryen tafiyarta awaje ta dawo gidan agajiye.

Bai hakura ba ya sameta a daki yahau mata nasiha wanda god knwa bama jinshi takeyi ba..
Bayan ya gama yace mata suje su bawa mamansa hakuri..

Shemau ta kalle cikin kwayar idanunsa tace masa bazataje ba ai ita aka ciwa mutunci aka zaga dan haka shi yaje yace ma mahaifyarsa tazo ta bata hakuri.

Ran mahmud da wuya ne yake baci amma data furta mai hakan saida yaji yawu ya dauke abakinsa tsabar bacin rai

Abunka da wanda bai saba masifa ba yau dayake mata masifar har muryansa na rawa rawa.

Yace mata Ki iye bakinki shemau duk abunda zamuyi dake banda kawo zancen raina uwata..

Tay banza dashi ya gama masifar ya fita yauma kusan a falo yay kwanan cikin kunci wani zucyar yace masa barinta yakeyi

Da sassafe yazo dakin ya sameta ta gama shirinta tasssss harta aika da jakarta waje an zuba matasu a motar da driver alhaj yazo daukarta dashi, ya sameta taci kwaras kamar wacce zataje gasar kyau babu komi nata a dakin face handbag dinta data aaje akan gado.

fuskarsa babu alaman wasa ya riko hannunta sukayo har waje sashen mahaifyrshi, shemau batace mai uffan ba ta bata ranta sosai.

Lkcin hjy ta gama gaiswa da hafsa daga can turkey kenan tanakan kunna turaren wuta sai ga nan sun shigo a rikirkice da juna kamar sun fito filin dambe .

Tana zaune tana kallonsu batace musu uffan ba ya dangwalata kasa a durkushe ransa a bace yace mata umarni yake bata data bawa maman nasa hakuri.

Shemau ta bushe idonta ta miƙe tsaye ta kalleshi tace wallah bazan bata hakuri ba..in kaga na bata hakuri to nima ta bani ne. Inba haka ba to zan bar gidan nan saidai ka zauna da uwar taka.

Baki bude mahmd yake kallonta dan tunda suke da ita bata taba mai irin wann tsangwaron rashin kunyar agaban mahfyarsa ba...

Idanunsa sunyi jaaa akanta yace shemau kika ce mene?mahaifyata ce zata baki hakuri ashe baki da hankli??

Tace masa eh ai uwarsa bata fita ba.. Da bori da hauka ta bangaje shi ta fuce waje fuuuuuu tay waje tana kananan maganganu masu zafi kafin ya fita daga shock din data jefasa aciki ya fito harta dauki jakarta ta fice acikin gidan..

For the first time in his life ya shigo dakin da mugun bacin rai yana ihun sunanta sai wayam baiga kayanta ba bare ita.

Da sauri sauri ya fito waje har bakin gate yana kiran sunanta, yana isowa dede bakin gate din lokcin yaga wulgawar wucewarta a wata kafurar jeep an wuce da ita tasha gilashi dauke kanta tayi danma wai karta kalleshi yabata tausayi idonshi da sukayi ja suka sauka akan deck din bayan motar yaga an rubuta A.A shafiu...haka sunan ya tsaya masa ransa batare da yasan meyasa ba.
Chapter 100 · 0% Book details