← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 304 OF 312

Sashe 304

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana fadin hakan ya ciccibe halisa a hannun sa suka wuce ciki meenal tafara binsu abaya tanason sanin meya same halisan inma zata samun hanyar kasheta dashi da sauki.

Dede kofar dakin ta fauce key a hannun mai gadin tace masa Da Allah ka koma waje ka kwashe aman da akamin a tsakiyar gida ni zan bashi key din.

Me gadin da taurin kai bai wuce ba saida ya leka dakin yace oga key din sabuwar motar hjya na hanun wann matar

khaleel ya sallameshi
Meenal taja tsaki ta shigo dakinsun dashi

Wani yatsine take tana kallon dakin up and down ranta a mugun dagule shide baice mata komi ba ya fara duba jikin halisa ya duba BP dinta Kafin nan ya saka mata ruwa ya dauko file dinta dake cikin wata jakarsa ya rubuta abubuwa ya barsa anan akan table.

Ya zauna yana latsa wayarsa lkcin jikin halisa
yay lugwi kamar ba itace awaje take tsalle yanxu ba.

Gyaran murya meenal tay
Muryanta ciki ciki tace ga "key din ka..Batare da ya kalleta ba yace drop it on the table. Da kamar bazataje ba dataga file din abude sai taje da sauri ta zuba ido akan file din dan tasan khaleel yana da very clear hand writing aikuwa tana lekawa taga sunan halisa
And her pregncy test result attachd to it cikin har ya wuce wata guda yana neman shiga da sati biyu. atke Tay lissafi a mind dinta taga auren nasu ma kwata kwata wata biyun ma yanxu ne yake cikawa wani doguwar hmmmmm ta saki aranta tanajin matsanncin zafin kishi na cinta aciki wato sati biyu kenan da shigarta gidan tay ciki.

tana juyowa Dukansu tabisu da harara mai zafi aranta tace jarababbu akasa ta buga key din da zafin kishi ta fita waje bata masan ko khaleel ya daga ido ya kalleta ko be daga ba...

Batama ganin gabanta tsabar duhu tana isowa dakinta ta rushe da wani matsanancin kuka me uban kara...

Duk sai ta rasa me ke mata dadi ta dauki wayarta ta kira mumynta ta dinga surutan da ta saba tana cewa anci amananta khaleel yaje yay ma halisa ciki bata yafe ba menenenta..

Tun hjya nadiya najin tausyinta harta dawo mata masifa ta kara mata da nata borin haukar tanace mata ai na jima da baki shawarar kiyi cikinsa ki haihu dashi koma meye ne da zaina ragar maki akan abunda zaki haifa masa amma haka kika maidani mutuniyar banza yanxu wa gari ya waya..

agabanki kawarki tazo tay cikin, kuma tana da kamfani wanda ma yafi naki daraja tana kuma kula da mijinta amma duk be hanata yin cikinshi ba...Amina kinga dik abinda nake gaya maki kenan kina runtse ido akai to ni me zanje miki yanxu..

Wayann maganganun bakaramin tsaya ma meenal arai yay ba

Tanata kuka tana nadaman kin bin wann shawarar..wayasan ma hala itama daya saya mata abubuwa koma ya fara sonta inta haihu masa she jst realise dat she fucked up one big time again..Yauma bakaramin cizon yatsarta tay cikin kukan nadama ba, ga dumbn mamakin sanin cewa khaleel is capble of pampering his woman this way dat she neva expect to see.

Aranta cewa take datasan haka maza ke tarairayar matan su da duk dai batay masa wasu abubuwan girman kai da hauka datay adacan ba

yauma Saida likitanta ta bata maganin depression kafin nan ta samu nitsuwa.

Zuwa can da yamma datagama tunaninta taga ne me zatay snn ta fito
Waje ta zo ta samu gidan ya cika da baki yan uwan khaleel...maryam da mijinta sunzo duba jikin halisan ga aliyu yazo all the way frm lagos zai xauna a maidugurin dasu for a while sabida yana hutu sai wasu causin dinsu mata su uku kyawawa dasu sosai.

Tun data kare musu kallo daga nesa taga kaf cikinsu babu wanda zatamai kallon banza sai taja tsaki kawai ta koma dakinta ta zauna tanakan jira su gama surutunsu su fita.

Time to time takan leko wani bin hartaji cousin din suna magananta calling her all sort of names kowa nacewa ta boye kanta a daki ne sabida ciwon Haukar karya.

This moments hurt her soo much, dama ta tsane taga yan uwansa .sai taji ranta na kuna musmmn ma da aynxu bata da wasu kayan da zata sako na barazana bare ta fito ta musu rashin mutunci susan ba tsoron uban kowa takeji ba.

She was boiling inside har saida yamma yay suka fito zasu tafi kafin nan saigata nan ta fito tana yatsine tanabin su da kallon banza.

Maryam da ciki ya saka tay freshh ko kallonta batayi ba hargara ma su aliyun da suka ce mata sannu tay banza da su
Sai basu kara kulata ba
Ruwa kawai ta dauka a fridge ta zauna a dinning tanasha dan ta kalle komi dan bakaramin saka ido da baqin cikin taji dataga uwar hidimar abincin da aka ci da kalar tarban mutuncin da halisa ta musu ba, upon duk da cewa bata wani jin dadi amma da jikin ya wartsake bashi ya hanata ta jonasu a falon sukasha hira ba.

This is sumtin she can
Neva tolerate Allah ya kiyaye mata zama da dangin miji kaf a mtsyin munafakai mayu maroka take kallonsu..

sai can Wajajen sallahn magbr snn suka watse Aliyu ya bi yayansa sukaje masallaci ita kuma halisa a kofar gida kawai taraka sauran bakin ta dawo dakinta tay alwala ta shimfida sallahya ta gabatar da sallahn magrib..

bata tashi awajen ba Ta dau qur'ani ta na duba abinda khaleel yake koya mata every morning har aka kira isha'i ta mike tsaye ta gabatar dashi a nitse shima..

Ta yi sallama kenan taji an turo kofar ahankli tana daga kai taga meenal da wani irin mamaki meenal din take kallonta kafin nan ta sake kofar da sauri jikinta harna rawa ta karaso...halisa lallai kin cika babban makira munafuka..hmmm na sara maki...wai dama dagaske kike kin musulunta??? Yanxu tsabar son ki makalkale min mijina ki rabani dashi shine har canza addininki saida kikayi ke wata irin mayaudariyace haka.

A kasale halisa tay murmushi tace thats is a very good way to express ur shock Amina. Koma me zakice ki fada i dont owe u any explanations.

Tana maganan meenal na kallonta da dumbin mamaki harta cire hijabinta ta linke ta nade sallayar ta aje ta daga qur'ninta ta ajeshi kan gadonta ta nufa meenal nakan binta da kallo me cike da baqar kishi dan wata shegiyar abayace me tsada ajikinta purple colour tana zama abakin gadon ta kalle meenal din snn tace Waime ya kawoki dakina ne ko kinxo neman mijinkin ne?

Nannauyar ajiyar zucya ya kwace ma meenal dan har yanxu mamakin ganin halisa tay sallan bai saketa ba...muryanta wani iri iri tace "kinsan ni ba muguwa bace kamr ki nazo ne inga ko kin samu sauki dazu naga kinata suma haqqi na yafara binki muguwa ...

Dariya halisa tay tace thanks jikina da sauki..

...waje ta nema ta xauna abakin gadon halisan snn tace "wai ciki kike dashi???

Halisa tay shiru sai kuma tay murmushi tace Eh.. haka champ ya gaya min..we are going to be parents soon.

take fuskar Meenal yay jaaa da mugun kulli aranta tace hmmmm
Okay.. kin masa magana na ko dama makirci da karyankine??

kai tsaye Halisa tace ive talked to him, amma yace zaiyi tunani akai

Tsaki meenal taja snn ta mike tsaye tana cewa dama abunda ya kawoni kenan inkin ga dama karki warke kimutu ahaka
Znga kuma dan uban da zaki haifa agidan nan wallh baki isa ba..

Dariya kawai Halisay batace mata komi ba harta fice tanajin haushin dariyan halisan aranta bana wasa ba...

Koda taje room dinta kasa zama tay tayi nan tay nan tanata tunanin yadda zatayi itama

washe gari sassafe ta fito ta jira har saida halisa ta fito snn ta tsareta da magana,duk dama ba me dadi take gaya ma halisa ba amma sosai halisan ta bata shawarar akan ta sauya takunta intanason kan mijinta sabida apart frm mugayen abubuwan da meenal tamata wann soyayyar datake ma khaleel din shikadai ne yakesata taji tausayinta aranta duk dama bata fiye nuna mata a fili ba.

Bayan nan Meenal tafara tunanin bin salon halisan koda itama zaa kulata saidai itafa tafison abunda zai mata aiki ne cikin agaggawa, yau kwananta biyu kacal da sanin cewa halisa na da cikin amma tabi ta dora abun aranta cewa itama lallai sai tay wnan cikin sabida khaleel ya juyo da kulawarsa da hanklinsa kanta babban burinta shine ta kore halisa agidan ta mamaye dukiyar mijinta itama taji irin dadin da halisa take ciki yanxu..

Tanason taga sun gwabza akan miji da halisa amma Gashi babu sauran lokci, sati biyu ya tafi already acikin wata gudan da kotu ta basu dan haka she have to take all risk to see her dreams comes tru.

a kwana na ukun Sassaafe ta saka likitarta
tamata gwaje gwaje ta bata maganin da zai dakatar da drug din datasha dan ya katse mata yin period da kuma haihuwa tun da jimawa

ranar da likitan ta bata maganin tasha ko aiki baiyi ba saida aka sake mata allurai snn jini ya barke mata tayta fama da azaban ciwon ciki, kafa, baya, ranar tasha azaban bana wasa ba.

Ana washe garin ranan da khaleel zaiyi deciding yafara zuwa dubata din kamar yadda halisa ta bukaceshi meenal tafara shirin daukar cikinshi saidai Haryanxu jinin da suka ballo yaki tsayawa

Shikuwa koda yazo ya samu halinda take ciki dama baizo da noyyar tabata ba Haka yace lallai saidai a dangana akaita babban asibiti aka fara duba lamarinta..

Ranan bakaramin baqin ciki da haushin hakan taji kawai ta lura dashi neman duk wata hanya yake da bazai hada gado da ita ba..

Atakaice saida tay kwana hudu masu kyau a asibiti akwance tana xubda jini
Ganin abu yaki ci yaki karewa ga lkci ma tafiya tafara ta fara daagawa hajya nadiya hankli akan lallai itadai sai taimaka mata an tsayar da jini dan ta dau cikin khaleel din itama.

Da wuya da wahala Da Taimakon Alfah jinin ya tsaya a akwana na biyar ranar ranar tace ma likita sam akaita gida wajen mijinta ai yau kwanta ne bana halisa ba..
Chapter 304 · 0% Book details