← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 312

Sashe 109

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda hafeez ya amshi tukin khaleel ya bata cikin shiru tareda tsunduma kansa cikin wata duniyar tunani wanda bai fito aciki ba saidai suka kai gidan hafeez din. Jikinshi a sanyaye ya nemi waje ya dan kwantar da kansa.

Maganin ciwon kai yasha ya kwanta cikin son yasaka kansa baccin dole, da kyar baccin ta dauke sa, after like 2hrs ya farka jin zucyrsa ta rage nauyi, bai tsaya cin komi agidan hafiz din ba ya kamo hanyar gidansa kai tsaye..
DONT SHARE NA KUDI NE INKUNASON KUBIYA CHAT 08060712446
wajajen karfe 1 na rana khaleel ya iso bakin gate din kofar gidansa agajiye yay horn mai gadi yazo ya bude masa kofar ya shigo ciki, tun lkcin yana kkrin kammala parking wajen aje motocinsu ya ga motar jasmine Din a parke sanin cewa tana gidan haryanzu tare da halisa yasaka yaji hanklin sa ya dada kwanciya..

Kafin ya sauka daga cikin motar yaga environment din gidan gabaki daya ya sauya masa, koina a harabar gidan yay fess fess har wani fresh air ke kadawa duk datti dattin flower da suke kasa yaga ankwashe yanxu babusu an kwashe weeds dake manne da walk ways an tandeshi tass da shara...

acikin nitsuwa tare da mamaki ayanyinsa ya sauke kafafunsa kasa idanunshi sunakan kofar me gadi da tsammanin kozai gansa ya tambayeshi koshine yay wann aikin sharan yana daga kai wajen daya saba zama sai baiga kowa ba face yar butarsa da alaman har yay alwala ya wuce sallah a masallaci.

Tunanin hakan shima yay ya dau butar yaje gaban tap ya kunna ruwa ya nemi waje ya dan zauna yafara alwalnsa a nitse

Ta gaban motar jasmine din yake kalla direct daga inda yake tsugune sunan dake gaban deck din motar yaja hanklinsa ya karanta sai yaga ashe ma yasan mahaifintan wani sananne kuma shahararren billionaire ne amma kuma musulmi ne probably mahaifyarta ce christian shiyasa dik sukabiyo nan.

Aransa bai taba kawo tunanin auren christian girl ba amma kuma haka kawai yau yaji tunanin hakan ya fara fado masa aransa batare da ya shirya masa ba..

tunda ya fara alwalan imagining yake how Is going to be fun and challenging sede baya tsammanin mahaifinsa zai taba amincewa masa a wann karon musmmn ma dayaki jinin auren sa da meenal da kuma personal abunda yake tsakaninsu na sabanin fahimta tun yana makarnta.

Mahaifyarsa ce kawai yake da yaqinin zata iya amince masa akan komi
Dan Itadin irin wayayyun matan nan ne da sukayi karatu me zurfi bata aikin gwamnati amma tana saida gwagwalan gold da zinare kala kala masu daraja tsakanin nigeria da kasashen waje.

she is also a philantropist her biggest obsession shine taga tana taimakawa marasa galihu da marasa karfi hakan yasaka take da gidan marayu masu tashe a garin lagos snn tana taimakawa kowa da kowa bata iya discriminating kowani yare ko addini ba..

yana cikin wann tunanin Can saikuma ya rasa mesa ma wnn tunanin ya fado masa aransa cikin basarwa ya sauke ajiyar zuciya yanamai maida hanklinsa kan alwala

yana gama kammala alwalansa ya taho ya wuce babban masallacin dake kofar gidansa kai tsaye anan ya gabatar da sallan zuhr dinsa acikin jam'i tare da mutanen anguwansu da sauran ma'aiktan dake kula musu da gidajensu anan.

Already duk anfara shirye shiryen shigowar watar ramadana kusan kowani magidanci a areansun yana da plans dinsa na azumi shi kuma saidai ya kallesu dan meenal bata masan me akeyi na aikin alheri a watan nan dan asame lada ba, gudanar da azumin ma ya aka kare da ita bare kuma batun sadaqa da sauran su. Haka zaiga anata shirye shiryen rabon kayan masarufi tare da abinci ma mabukata kusan kowa da abunda iyalinsa zatana kawowa amma bandashi,shi kam Saidai in za'ayi wani abun ya dunkula kudadensa na sadaqa yana bayarwa wa commitee na masallaci.

Kusan yauma haka nan ya zauna looking so odd acikin sauran mazajen anguwar ana hira ana raha har aka kammala dik wata plan din abincin sadaqa da za'ayi daga masjid din as usual shi kudin kawai yake dashi da zai bayar.

Daga cikin gidan kuwa halisa da kawarta jasmine basu wani jima suna hira ba nan cikin son ta warware mood din halisan tasakata agaba sukayi abubuwa agidan da yawa tare Sukayi rearanging room dinta sukayi mopping floor.

Jasmine duk ta rasa gane kan tsaftar gidan haka tay convincing din halisa akan suyi hiring house keepers suzo su kimtsa shi tasss tasss

A halisa tanaso bata so hakanan jasmine ta saka ta dole, nan suka kira wani kamfani aka turo musu home keepers a location dinsu su hudu Maza biyu mata biyu..

And she make it fun da music da hira da komi saida cikin gidan ya zamo kamar bashi ba falonsun ya fita kal kal yana gamshi sosai.

Iyakar inda basu taba ba shine rooms din gidan da halisa tace sam babu ruwanta aciki, amma bayan nan tun daga wajen gidan har cikom babban falon gidan suka share suka yi mopping har izuwa cikin kitchen
nan ma Tare da halisan suka arranging abubuwa a kitchen din Dan bata fiyeson tana kayan wani ba, iyaka wanda zatana yin amfani dashi kawai ta aje kurkusa, 3hrs house keepers din sukayi kafin nan suka kammala komi jasmine ce ta biyasu kudinsu suka tafi.

Yunwa yasaka Halisa ta hakura ta dafa musu hadadden yam porridge me masifar qamshin dadi yaji sardines da veggies Din da jasmine taje siyo musu a kasuwa

A cooler halisa ta zuba abincin duka snn ta kawo musu kan dinning suka zauna suna ci gabaki daya qamshin abincin ya karade cikin gidan, cike da zolaya jasmine take ce ma halisa tay kkrin tana keeping kanta busy kamr haka dan intana motsawa bazata na zama acikin kadaici da yunwa ba, cewarta aikin gida yakan dauke ma mutum hankli Daga tunani kuma shidin ma wani sabon salon motsa jiki ne babba.

Cikin raha kawai sukayi hirar halisa bata dau abun serious ba sabida batason ma ajega wani abinda zaina hadata zaman cin abinci waje guda da meenal bare kuma mijinta.

Ta kammala cin nata kenan tabar jasmine din a falo, ita ta haura sama taje room dinta tay wanka lkcin jasmine ta fito da wine dinta Dataje ta siyo a kasuwa ta aje akan table dan ko zubawa a glass cup batay ba ahaka take shan abinta ahankli yana bugar da ita tana sha tana kan cin poridge dinta cikin nitsuwa.

Baifi saura kadan a plate dinta ba taji sautin alaman bude kofa ko juyawa batayi ta kalleshi ba dake hanklinta nakan wayarta ne.

Shikuwa tun daga bakin kofa yakejin wata bakuwar kamshi mai masifar dadi ya haɗe gidan dik qamshin turare dana abincin da halisa ta dafa ya gamutso yana bada atmosphere me dadi da bai tabajin irinsa agidan nasa ba.

Karasowa ciki yay ahnkli yanabin koina da kallo ganin yadda gidan yake kyalli yanabi da ido har yakusa karasowa wajen da jasmine take zaune akan dinning da mamaki akan fuskansa ya hango warmer dake gabanta tana cin abinta batare da taji motsinsa ba sabida wayarta dake hannunta tana kallon wani video aciki. Bata sani ba sai tuntsirar dariya take famanyi, uhm uhm yy gyaran murya tay saurin dagowa adan razane suka hade ido tagansa a tsaye baice komi ba kallonta kawai yakeyi.

murmushi Ta sakar masa cikin sanyin aji tace hi doctor u almost give me a heart attack

babu yabo babu fallasa y yace "My apologies. dont mind me I am almost lost. Satan kallonshi take ganin yadda ya sake karewa gidan kallo cos he cant get enuf of it da alaman yaji dadin ganin yadda sukayi da gidan sosai, yana juyowa kanta kuwa suka kara hade ido, girarta na sama a dage, tace "Why dont u come and join me?..

nauyinta dayakeji yasaka Baice komi ba duk dama tun safe bai tsaka komi acikinshi ba jasmine ta bude warmer din danta nuna mashi abnda ke ciki tana budewa take aroma din abincin ya bugi kofar hancinshi for the countless time yaji cikinshi tay kukan yunwa taciki..

yana murmushi Cike da jan aji yace "I dont think i can eat this. Tay dariya Cikin fahimtar yanayinsa najin kunya Tace "cmn doctor ai mu ba baki bane awajenka just refreshen up i will park it up for u pls.. i promise.

ahnkli yace okay shiknn

Dadi taji aranta Ta mike sama taje ta same halisa a daki lokcin tana zaune akan chair din gaban mirror tana shafa mai a jikinta ahankli kamr bazatay ba..

Kallonta jasmine take tun daga kofa tasan inta gaya mata cewa khaleel ne zaici abincinta bazata taba amincewa ta sauko tay serving dinshi ba..

tana zama ta marairace fuska halisa can u pls come and serve me kinsan ban iya ba kuma inaso ne naje na ci awaje. I want to smoke weed kar na bata muku cikin gidanku da warinshi.

Rashin son fitina yasaka halisa ta jawo robe dinta ta daura ajikinta snn suka sauko kasa tay servng mata abincin a plate ta barta anan dashi ta koma sama ta cigaba da shiryawanta a nitse.

Kallon kanta take a mirror da wani irin rauni acikin zucyarta dan har yanzu tanakan jin kanta kamar ba ita ba ta kasa iya cire zagin da khaleel yay mata aranta badon komi ba saidan sam batay tsammanin zai gaya mata hakan ba

Dalilin hakan yasaka ta fara nitsuwa tana kkrin reflecting akan dukkanin wasu maganganun da jasmine ta gaya mata akan meenal dazu dik dama batason tay ma khaleel din saukin kai amma gani take kamar hakan zai zame mata dolenta muddin inde tanason reputation dinta ya zamo safe a idon mutane.

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama abakin gadonta cikin rafka wani uban tagumi ranta na baci taciki tuna duk abunda batason kusan sune suke zamowa mata dolenta yanxu wanda tasan inhar bata dauki matakin gaggawa akan dabiar meenal na bata ta abayan idonta ba toh tabbas wata rana hakan zaiy mata babban illa ga rayuwarta and she is neva gonna get over it.
Chapter 109 · 0% Book details