← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 312

Sashe 61

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunawa da yanayin da yaga meenal ta fice yasaka shi yasha jinin jikinsa. Kallon ta ya dingayi ganin idanun ta sun nuna alaman kuka

Yace "Boss..are u okay?

Ajiyar zuciya me nauyi ya kufce mata ta masa kallo daya batace komi ba ta gyadamai kai ahnkli.

Neman waje yay ya zauna akan kujera yana kan kallonta muryan sa a sanyaye yace Good morning...

Kanta na kasa kusan
Agajiye Tace morning

Yace ya jiki.

Ta bata rai Uztaz is okay bana son gaisu..bata gama furtawa ta kalle jakunan daya shigo da su

Katse masifar tay tace "What are dos?

Yana murmushi ya mike
Yace "Its ur gifts from...sai ya saka hannunsa a aljihun wandonsa ya fidda wata brown envelope ya mika mata tana budewa taga keys Aciki ta dauki keys din ta kalla snn ta bude post card din dake cikin envelope din cikin nitsuwa tafara karantawa

Bata san sanda ssanyar murmushi ya kufce mata akan fuskarta ba musmmn ma dataga handwriting din jasmine tacha akan paper dincike da funny motivational messages akan self love and care...Ga address da number na mutane da rubuta mata shi ajiki..

Crazy Hair stylist, body shops,spas, clubs, wajen massages da wajajen shakatawa da zasu dauke mata damuwa.

Mikawa uztaz paper tay danya karanta tana murmushi ta mike tsaye ta jawo duka akwatunan gabanta tafara dubawa.

Uztaz ka aje cards din nan da kyau...we will visit some of these places saika duba ka gan wanne ne is more private bana son wajen hayaniya..

Yace okay maam
Ummm barinje na kawo miki breakfast me zakici?

Tay shiru kamar zata fadi wani abu sai kuma ta tuna shawaran da jasmine ta bata, take ta sauya mind dinta tace "i dont knw..go and ask ur so called doctor inya gaya maka me zanci seka je ka siya min i am hungry.

Mamaki ya cika uztaz ganin inda ta sauya lkci guda, ya girgiza kansa a hankli yace okay snn ya ciro wayarsa a aljihunsa ya fita waje yanamai turawa khaleel din sako.....

Daga nan dakin kuwa halisa ta mike kamar ba itace bace take kuka dazun nan ta dauki akwati da jakar ta dora asaman gadon ta bude jakar taga kayan make up ubansu ga kyau ga tsada gasunan birjik kala kala da materials din su.

Bata saka artificial Eye lashes,da nails, iya su dinne kadai babu su amma bayan nan komi da ake bukata na kwalliya akwai.

Halisa na murmushi ta cicciro su waje ta fara jerawa akan saman madubin dakin snn ta ciro bags of wigs caps mostly blond and gold su biyu guntaye, da guda daya me tsayi da afro hair cap guda daya baki making it four dede na ranakun daya rage mata agidan nan.

Dariya tay dataga Kwalayen taba akasar jakarta sunkai pack biyar sabbi, saida taji sanyi aranta data gani sabida shan tabar bakaramin distracting mind dinta yakeyi daga shiga cikin yanayin tunani me saka baqin ciki yake ba, itade ta gwammaci tasha maka tabar acikin hanklinta duk dama tasan yana cutarwa akan data sha giya ya gushar mata da hankli, cos she thinks dat duk me shan giya raunatacce ne kawai kamar baban ta mr roberts mansa, wanda bai damu da mutuncin kansa ba. She still rembr how his miserable death remain a stigma to her entire life. Tun tana karama Kowa ya tashi mata gori a garinsu sai ya ce mata ubanta giya yasha mota ya kade shi.

Gani take Shan giya zai iya saka ka kayi abubuwan da zai zubda maka mutunci har dana yayanka, ko ya saka kayi nadama na har karshen rayuwarka, and dats why komin tsananin baqin cikin da zata shiga bata amincewa ta sha wani kayan maye ba...

kamar wacce tasan da camera a dakin saitaki sam ta fito dasu kawai saita cire park din inner wears din dake cikin jakar ta maida new hairs dinta ta rufe jakar dasu ta bude wardrobe din dake dakin ta ajeshi acan can dungu.

Koda ba agaya mata meke cikin madaidaicin akwatin ba tasan kayan sawa ne amma ganin jakar baida girma yasaka taji she is curious to see wasu irin kayane aciki.

Tana budewa tagansu a nade neatly arranged nan tafara ciro su daya bayan daya tana zubawa akan gadon tukuna kafin ta warware su zata fara budewa kenan Karar wayarta ya katseta ta nan ta mika hannunta zata jawo wayar.....
Hannunta tasaka zata jawo wayar sai kuma kirar ya yanke ta kalle saman screen din taga wani special and strange international number ne, takaitaccen kallo tay ma lambar ta girgiza kanta
Batare da ta saka komi aranta ba ta aje wayar ahankli snn ta dauke hanklinta daga kan wayar
ta komar kan sabbin kayayyakin dake gaban ta tafara duba yanayin su one after the oder tana yi tana murmushi mai sanyi Dan Duk lokcin da kawar ta jasmine tace zatay mata abu to dole ne abun yayi amazing dinta shiyasa tun da ta bude kayan taji ranta yay fari tas tass dan kuwa jasmine din tafita dadewa da kuma kwarewa a harkan fashion industry data baro duk dama dacan din they are both super models da ake ji da su a wajen, sede kyaun fuskar Halisa da sexy and sleek shape dinta ne yaso ya bambamce su wanda shine yayy musababbi halisan tayi kasuwa da farin jini batare da tajima a harkan sosai kamr jasmine ba.

Kayan basuda wani yawan azo agani sede Ita kanta tarasa Farincikin menene takeji haka data gansu, ko dan sun balain dacewa da plan dinsun ne oho, itade glamourous and classy fashion sense na kayan ne yafi burgeta matuka sabida tanason harkan girma bata son kayan da zata saka ya bayyana ta a matsayin mace marar girma da daraja. shiyasa ko a designers ne tafi saka irinsu kamfanin LV, Gucci, Hermes, Amina muaddi, hudda kattan, valentino, nadine njeim, zuhair murad, turkish, da dedekun french and italian designers da suke baje fasihahhen basirar su wajen kera nitsattsun kaya masu tsarin fashion creativity na daban wanda suka sha bambam dana sauran manyan yan mata just to spice up her queenly appearance cos She belive she is not a regular trend.

Wann karon sai taga kmr jasmine din ta saya mata wasu designers na daban wanda bata fiye saka su bama,Crop tops, strapless,One hand top, Crawl spaghetti tops, strapless sphaggeti, plunging neck, off shoulders, mostly na kamfanin torry burch, lacoste, chanel, max mara, jimmy choo, dior, da kuma fenty, Kyabe cute lips dinta tay acikin yanayin shagwaba da sanyin kasala daya kawata fuskarta bana wasa ba, bata taba saka all these mini and sexy girly designers din ajikin ta ba. ta zage ta cigaba da bincika wa wai koda zata ga dama dama acikin kayan amma ina daga Mini skirts, sai Petals,Bomb shorts, Saron, da slit skirts inda Kowanne ta dauka sai karamin blush me tattare da kamilallen kunya ya kufce mata aksale, duk ta kasa dena murmushi wani abin ma harma ya sakata runtse idanunta tanamai jin kamar ba zata iya sakawa bama.

Sede aranta ji take kamar she can do anything to gain her freedom frm khaleel snn da wann boyayyar shaukin datakeji na mugun son taga ta nisanta kanta daga meenal na dan wani lokaci mai tsayi da zai iya sassauta mata tulin damuwa da kuma radadin grudges tare da boyayyar fushin datake fama dashi na cin amanar da meenal tamata.

Kalolin kayan take kallo badai daukar idanu ba, dake kaloline masu haske kamar lush pink, peach, sky blue, alots of whites, lavender purple, da uwa uba pepper red, tan and winery gold.

Tarkata kayan tayi ta shiryasu da kyau acikin closet for easy access. Daga nan tay gaban madubi ta tsaya cak tanamai kurewa kanta da kallo sosai kamar wacce take son taga wani abu acikin, nannauyar ajiyar zuciya take saukewa a karo na babu adadi dan Har yanzu kallon kanta takeyi kamar ba ita ba dan abubuwa dayawa sun sauya mata a kamaninta da kuma cikin zucyarta sosai. She is in a stage where she cant recognised herseld anymore, irin ka dingajin kamar brain din ka da jikinki banaka bane din nan.

Daga tsayen ta Lumshe idanunta tana tunanin yadda zata tursasa kanta yin abubuwan da jasmine ta kayyada mata domin samun sauki dan bata da wani babban buri aynzu da ya wuceta bar musu gidansun ta koma ga hidimar rayuwarta data saba koyaushe.

Bata bude lumsashun idanunta nata ba har saida tay convincing kanta cewa lallai zata iya kwaco kanta daga hannun khaleel din acikin sauki, Juyawarta ke da wuya taji wayarta na kara dacan kamar bazata dauka ba tahakura ta taho bakin gadon dede yana daf da yankewa ta dauka kafin nan ta dora bisa kunnen ta tana mai sauke boyayyar ajiyar zuciya, a hnkali cikin sanyin murya tace Helo sir good morning.

Daga ta dayan bangaren Dr Aseem yay murmushi yace Hello dear. Hope ban tasheki a bacci ba?

Babu yabo babu fallasa Tace Na tashi..
daga nan suka gaisa, ta lura ya damu da lamarin ta sosai, na musmn takejin ajikinta kamr yafi kowa fahimtar metakeji aranta game da rayuwarta, snn ya fahimce cewa tana cikin halin kadaici duk dama bakowa ne ya ke mata kallon cewa tana missing din familyn ta ba.

No matter how rich or succesful u are dole ne ka bukaci makusantar ka na jini ko iyayenka atare dakai dan dole ne akwai gurbin kewar su da wasu mutanen bazasu taba cike maka su ba.

Cikin tausashiyar muryansa me saurin kara mata nitsuwa ya tambayeta ya take ji yanxu a jikinta...

Bata boyemai komi ba ta gayamai cewa she is feeling empty tanajin kamar ba ita din bace wata ce daban. Sann ta kara jadadda masa cewa bata son zamanta anan gidan duk dama taki sam ta gaya masa dalilinta game da hakan.

Murmushi yay mai sanyi
Cike da lallami Yace karki damu zanzo na dubaki dakaina sai mu tattauna sosai amma sai bayan kwanakin dana deba makin ya wuce atare da Dr khaleel.
Chapter 61 · 0% Book details