← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 312

Sashe 82

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun nile yana tsammanin ganin sakonta awashe gari har ya hakura ya sake ranshi musmmn ma dayaga femin ya sake da leo ana games ana nishadi mutane na zuwa gidan gaishe da femi kamar abun arziki

Abokansa Idan sukazo haka zasu ta saka su nile suna ji aransu cewa zaman femi acikin su shine masa mafi alheri
Kodan sabida tsaro da samun kulawa.

Leo kuma gaba takaisa dan kullum mashi ake turawa kudin da suke kashewa duk da nile yaki ya sake jikinshi da komi haryanzu.

Ata bangaren halisa cikin kwana biyun babu abunda ta rage daga cikin abunda ta shirya aranta akan khaleel

She do provocked him with her dresses and her fierce sexy looks a yanayin da ita kanta bata sani ba, gashi meenal taki sam ta bashi hadin kai, kusan kullum da dare sai sunyi tashin hankli ahaka harya soma shiga cikin wani matsanncin yanayi da wani bin ko kofar dakinsa baiya son fitowa akan lokaci.

Rayuwa ta fannin fadila tamkar mafarki me daya zame mata gaskiya dan zamanta acikin su monica yasa ta gane cewa tabbas da akwai mutanen kirki da suka rage a duniya.

Babu raini babu kaskanci suke gudanar da rayuwarsu an bata gida ita daya tana zama aciki kowani lokaci sukazo su dauketa suje wani babban ma'aikata nan ne Shuaib umar yake koya mata yanayin yadda aiyukn kamfaninsu yake
Yadda suke muamala da share holders da uwa uba customers da workers dinsu..

Da abinda basu dauka da abunda suke dauka dake kamfanoninsu basa harka da gurbattatun yan kasuwanni..they just take contracts work on it deliver, make products, sell, and move goods and services to consumers.

Hanklin fadila bai taba kwanciya akan business kamar wann ba, aganin ta babu wani abu da zai jawo kayi hainci sede rashin tsoron Allah.

Taji dadi sosai daya kasance halisa ta jonata da musulmi dan kano kuma cikakken bahaushe me riko da Addini wanda yasan kimar mace da girman amana.

Basu wani jima da haduwa ba amma sosai taji hanklinta ya kwanta dasu sosai wanda yasa ta saukar musu da kai suna koya mata nasu salon aikin sosai.

Tun ranar da aka hadasu izuwa yau kusan Kowani lkci in tay sallah sai ta daga hannunta sama tana hawaye tana me rokon Allah akan ya saka wa halisa da alheri duniya da lahira ya kuma daukakata. Ayanzu bata da wani damuwa da wuce neman yafiyar mahaifyarta duk dama tasan itace gaba wajen jefata acikin musibar datake ciki amma awajen uwa uwace bazata iya kyale uwarta da tulin yan uwanta da suke kauye acikin wahalar duniyan nan ba......
fannin su hajya binta shirye shiryen tafiyarsu turkey da hafsat kawai ta shigayi ayayinda hafsat din take cikin wani hali na matsanancin tsoron sakewa atsakar gidansu mahmud badon komi ba sai dan ganin shema'u datakeyi kullum.

Sosai zuciyarta ya karye dan ita kadaice ta san yanayin yawan muguntar shema'u wanda duk cikin sun nan babu wanda ya sani, ganinta datay agidan sosai ya dawo mata da memory na wasu worst experience dinta da ita, kamar irin dukancin mutunci datake mata kowani safiya da ruwan sanyi datake kwara mata akai da ranar data ƙona mata kan harshenta da tafasasshen ruwan zafi

Sau babu adadi ta sha yi mata tsirara bayan ta laka mata sharrin sata haka zata zage iyayenta tsaf kuma ayanayin mafi kaskanci da tozartawa.

Aranta gani take kamar In duniya zata kife ayau a sakeyinta jitake kamar bazata taba iya mantawa da wasu abubuwan da shema'u tay mata ba.

Yau Tun da ta shiga dakinta sai bata fito ba har sai da lkcin daura abincin yay anan ma bata wani saki jikinta ba kominta a dar dar takeyinshi da kyar da wahala take iya sake komawa can sama sashensu domin kaima mahmud abincin ranan sa na kowani lkci, ahakn ma bata iya jure tsayawa a inda yake kawai tana kammala serving dinsa sai kaga ta bace buut ta sauko kasa ta koma dakinta ta zauna cikin kadaici da tsoro.

mahaifyar mahmud hjya badiatu data ke lura da yanayin tan abun sam baiyayi ma zucyarta dadi ganin yadda zuwan shemau gidan ya katse ma hafsat walwala da jindadinta gabaki daya

tarasa wani irin tsoron shemau hafsat din takeyi wanda gabaki daya presence dinta ya gama rikitata ya hanata samun wani nitsuwa tare da kowa.

Hafsat Taki sam ta zauna a inuwa daya da su bare kuma mahmud tabi ta kumshe kanta a cikin daki cikin tsoro da tunanin rayuwa.

Wani lokci haka zata naɗu akan gadonta tayta kuka marar kara ita daya tana lissafi a kwakwalta shin ta ina ne ma ta dace da zamowa kishiyar shema'u...

Abun sosai ya fara damunsu hajya aransu Dadin karawa da basu yawan jin duriyar shemau acikin gidan dan tun safe take ficewa bata kuma kara dawowa cikin gidan sai can dare lokcin kusan kowa yay bacci gashi nan dai haryau mahmud beson jin lefin matarsa kwata kwata.

Hakan yasa iyayen nasa biyu duka suke yawan samun sabani dashi

Wani bin hafsa na rakube najinshi yadda yake kare matarsa agaban iyayen sa duk da shaidojin da ake basa.. duk da haka babu abunda yafi karya mata zuciya game da shi kamar yadda yake yawan nuna cewa bazai fallasa aurensu a fili ba sabida baison matarsa shemau ta raunatu.

In her own little fragile heart takanji ta kaskanta tunda har matsayin shemaun aransa yakai ace ita a boye nata matsayin dan kar ran shema'un ya baci.

Wani bin takanji dana sanin shiga cikin wann auren, wani bin kuma takanji kamar alfarma kawai akeyiwa rayuwarta
So, akan wani daliline zata saka ranta na samun matsayin matar aure a zuciyar mahmud bayan ita bakomi bace awajensa face abar tausayi???...

Yau ranar sunday sassafe vicky ta fito a shirye da kayanta tare da yar uwanta samantha suna ma junansu sallama cikin kewar juna.

Samantha ta shirya zataje church dan haka ta hada vicky da driver yakaita har airport dan ta dawo lagos. Bata ma gayawa kowa batun dawowartan ba dake urgent ne. Jiya aka tura mata sakon email cewa ceo na elmario ya tura mata sakonni a computer ta dake gida.

Sam bata son tay wasa da wann babban daman musmmn ma dataci burin yaface kanta daga rayuwar femi cikin ruwan sanyi.

Batun business din ne ya sakata yin shirin gaggawa cikin dare juya tayi booking jirgin da zaai dawo sa ita garin lagos wajajen 11.30 na safe ta iso gidanta kowa na mamakin ganinta.

Banda masu aikinsu babu wanda ta tarar agidan, dan Koda ta iso hutawarta tay kadan snn ta dudduba boyayyun sakonnin kayden dayake turo mata ta private email din kamfaninshi dake computerta zama tay ta amsasu cikin nitsuwa ta tabbatar masa inda taje snn ta gaya masa cewa ta dawo.

Hanklin kayden akwance yake sanin cewa vicky is not in good terms da rival dinsa femi, yana sane da cewa ita kadanta ta tafi abujan sabida bayan tafiyarta yana yawan ganin henry da femin agidansu kuma yasan me sukeyi most of the times in sun kebe.

Yana da recording din femi in action yafi kala talatin daya ajiyesu a chip dinsa shikansa baisan yaushe zasu amfanesa ba.

Bayan sun kammala chat da vicky wanka kawai ta fada, sanda ta shirya kanta tsaf cikin wata peach gown snn ta fito taci abincin da suzan ta girka mata hadadden tuwon sakwara da miyar egushi taci tay dam dam

Bata bar gidan ba saida karfe 2.30 na rana yayi yau sunday tasan nile yana gidansa dan haka ta wuce gidan direct dan ta samesu duka atare

Sukusan biyar a falon suna game suna nishdi akaro na farko da nile ya dan zauna acikinsu suna nishadin tare ana buga ball a ps which is so fun
Gidan ya cike da surutu
Wani irin dadi Leo yake ji ganin kansa acikinsu prince femi harda wasu abokansa masu masifar kudi su biyu da sukazo wai sunzo gaishesa duk basusan bakinsu daya bane da abokinsan.

Suna cikin wann yanayin nishadin saiga nan vicky agidan tun daga waje take jin muryoyinsu kamar ana wata hidimar aciki abun ya daure mata kanta sosai.

Bell ta danna kusan sau uku kafin nan nile ya tashi ya iso bakin kofar ya bude yana ganinta yaji wani irin farinciki ya mamayesa wawar rungumar da sukama junansu yasaka femi yay mikewar tsaye dan ganin wayene ya shigo yana lekawa kuwa suka hade ido da vicky kallon tsaf takaremain ganin sa wasai ga wani katon kwalban giya a hannunsa jikinshi ba ko aron riga.

Suna hade ido ya wani bata rai itama take ta tsime tay kamar ma bata san shi ba..ganin ta basar dashi shima ya basar da ita ya nemi waje ya zauna yanamai ce ma aboknsa its victoria.

Rike da hannun Nile vickyn ta karaso cikin falon tanamai karewa yanayinsu kallo cikin kyabe baki suka gaisa da kowannensu leo ya taso yazo ya gaisheta cikin girmamawa.

Tunda tazo Hanklinta gabaki daya na kan kaninta ne bata wani kula femin sosai ba shima bai wani kulata ba dake mind dinsa yanxu akan burinsa na samun nile din kawai yake..

Sama sama ta masa tambaya akan abunda ya faru yana amsata ciki ciki cikin shan qamshi itama nan take ta nuna masa cewa tafishi iya shan qamshin shiyasa bata wani tsaya jajanta masa ba wanda Hakan yasaka ko kebewa bata nemi tay dashi ba.

He suggest he want to be spending time with them tace masa is fine with her insu nile din sun amince.

Nile najin kunyarta bazai iya cewa a'a ba, msn da abokinsa leo yanuna musu shima yana jin dadin companyn su femi sabida kudin dayadan fara rudarsa and the fun hakan ya tursasa nile ya hakura yabar maganan ahaka.

Vicky bata wani jima agidan ba tace ma nile din ita zata je kasuwa sai gobe zatabi wajen aikin sa suyi magana me tsayi akebence sabida yaune tadawo daga abuja kuma tanada aiki sosai datake son kulawa dasu na yaran university da aka damka matasu a makarnta.

Vickys mind is on her business now musammn ma wanda take tattauna wa akai da kayden a computerta.

10 am sunday:
Chapter 82 · 0% Book details