← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 312

Sashe 123

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaune ranar koyan abincinsu na karshe inna hjya tace mata tay local kunu kala kala one one cup, aka siyo mata hardasu cow milk, gari gero dana dawa da sauran cereals.

Bayan ta gamashi aka sake bata wasu kayan shayi kamar kala takwas kowanne tayishi shima

gefe taja tana zufa tana fifita da hannu, Hular kanta ta cire kanta babu dankwali gashinta mai cika da tsahon gaske ya bayyana ta nannade shi acikin ribbon satan kallonta hajya takeyi tana murmushi ganin yadda suman ya wani kwanto mata agaban goshinta musamman sabida hamamin turirin ruwan shayi data hada Tana kashe last tea pots ta juyo a takaice tace" mama na gama.

Hjya tace jeki kira inna hjya tazo ta gani, tace toh snn tafita.

Har iyanzu kirjinta bugu yake tana ta tsamamnin jin coments dinsu

Jiya da sukayi judging din smoothie dinta they were tough though, dan Da kyar ta samu making 99.99%..

Inna hjy na zuwa suka hau tattabawa, sai bin reaction dinsu take da kallo kirjinta na bugawa, bayan sun gama duk sun gamsu suka mata nasiha atare hjy binta tace mata ba iya abincin bane kawai nasarar mace a gidan mijinta

Halin kyautatawa da tsafta da kuma riko da Addini uwa uba sanin daraja da bukatar namiji sune mabudin samun hasken zamantakewa.

Inna hajiya tace mata kafin taci nasara a rayuwa sai ta nitsu ta san waye kanta waye kuma mijinta meyake so meye baiyaso da kuma triggers dinshi .Tace mata duk yadda akayi tay kkri ta iya kalami, dan duk dadin gindin ta, da dadin girkinta if she have no respect for her man bazata je koina a rayuwar aurenta ba.

Sosai hafsa ta gamsu da bayanansu Cikin gamsuwa da jin dadii suka mika mata wani box me dauke da kyautar abun hannu da abun wuya aciki..

inna hajya tace mata congratulations,infact Ure the best cook ive ever seen..

Wani Washe bakin bazata hafsat tayi kamar tayi cillo can sama dan dadi...

Tace nagode sosai inna hjya Allah ya kara lfya ta juya wajen hj binta tace nagode mama Allah ya saka da alheri.

Dukansu murmushi sukayi tare da saka mata albarka.

Dama wannan ajin shine karshe ko?gyada kai tayi tana murmushi sosai

Hajya binta Tayi dan jimm kamar mai shirin tuno wani abu can tace
Cikin azumin nan babu wani aiki sosai dan haka daga kin dawo schl zamu na zuwa Spa. Dake duk suna sane da cewa mijinta zai iya zuwa lokcin sallah sunaso yazo yaganta cass cass

Da tsallen farinciki hafsa ta amsa cos she is dying to became clean itama she really want to have her confidence too kwata kwata bata kawo tunanin mahmd a duniyarta ba...
Yau sati biyu kenan da shiga cikin watan azumi, lkcin azumin yana neman rabawa tsakiya kusan kowani bangare da kalar abunda yake faruwa a labarin zamantakewarsu.

Wasu kuma rayuwar ce ta tsaya musu cak bata motsawa.

Ata fannin kayden rashin samun vicky kwana biyun acikin boyayyar duniyarsa bakaramin dagamai hanklinsa yay ba. dan kamar wanda bai da lafiya hakanan zaka ganshi, kullum yana gida yana kwnce a dakinshi cikin tunanin inda take cikin matsanancin damuwa da kewa, iya bincikensa dayay agents dinsa sun cemai tay tafiya garin su ne,but witout notice kuma babu wani kwakwwarr hanyar communication yasan dolene da akwai wata matsala daya faru da ita wanda shikansa bai sani ba.

shakuwar da suka yi da juna Na Kwana biyun nan yasaka suka zamto kamar wasu zautattu dan itama acan garin nasu batajin dadin rayuwarta ko kadan kamr inda shima anan abun ke nemn ya dawo masa tamkar ciwo, taje ne nesa ne dan taga ko zata iya mancewa da kalamn sa amma sai taga gabaki daya takasa, sau tarin yawa takanso ta daga wayarta ta nemeshi koda a tex messge ne amma kuma sai taji bata iyawa.

Duk wani tunanin duniyan nan shima yay amma zuciyarsa bai zargi komi ba face femi, he is an overthinker kullum ya zauna cikin lissafi yake, hakan yasaka tsammanisa yajega cewa kodan kamfanin daya bata ne yasaka femi ya sakato agaba. to waysan ma hakan shine ya jawo tay cuting comuncation da kowa, shide duk ya rude yana tunanin ko vicky zata fito ta dawo masa da kanfaninsa ne tace masa bataso kuma batason shi.

duk da bai tabbatar ba but he felt depressed damuwa ya cikashi Sai kuma ya dawo yana matsancin jin haushin femin aransa badon komi ba saidan katse masa jin dadinsa dayay na samun attention din vicky akowani lokci.

Rashinta ya zamo masa tamkar duhu baiiya ji baya gani acikinsa

tabbas, vicky itace hasken rayuwanshi snn itadin nunfashine dayake shaka wanda bazai iya rayuwa babu ita ba..

It took him a while kafin nan ya gano abunda zaiyi ma femi domin ya kwace vicky daga daurun da igiyar aurensa yake mata kwata kwata...

tsawon satikai biyu dayake ciwon sa a room dinsa baiya yadda ko yayansa henry yana zuwa damunsa..

Rana tsaka sai henry yaga kayden yana zuwa wajenshi akai akai suna hira, henry baisan me yake damun kaninsa ba amma har yar raman nan na damuwa saida yaga yadanyi. Tausayinshi yakeji yana tunanin ko zaman nigeria ce ta fara gundurarsa. Haka kayden ya jawo henry ajiki yabar sa yana jinyarsa dan yaron akwai kwakwalwa in zai nemi information wajen mutum baya nunawa da wuri.

Saida ya tabbata henry ya sakankance dashi sann ya soma jansa da hirar harkan da sukeyi dake henry baya boye ma kayden komi. Haka zai masa wayo ya bashi giya me zafi ya sha sosai, in suka fara hiran LGTBQs haka kayden zainamai tambaya yakance ma henry What if yay aure yana da mata how is he going to cope with her duba da basujin shaawar mace anasu clique din.

gaba daya Henry bai kawo komi aransa ba yakan dauka kawai hira ne normal, dan haka zai ta zuba yana gayawa kayden tactics dinsu yawancinsu dai karyan ciwon mazakuta sukewa matarsu, wasu kuma sukanyi claimg basu da lokcin sex ne kwata kwata sann sukan spoiling matansu da kayan duniya masu irin wann harka suna sake hannu kuma basa rowa sam sam. Acikin tadin henry baida wanda zai buga misali da shi sai abkinsa femi.

Babu tsillin sirrin femi da bai gayawa kayden game da hakan ba, har da labarukan kalar asibitan da vicky take kaisa da irin kudinda suke biyan likitoci dan azanca result na potency dinsa zuwa lowest matakin da zai nuna kamar ma bazai gyaru nan kusa ba...

kayden yaji babu dadi aransa dan sosai lamarin vicky ya bashi tausayi ya kuma dagamai hanklinsa bana wasa ba..

Duk yadda yaso kar hakan ya nuna ayanyin sa saida ta nuna, cikin dakinsa ya koma cikin kasa samun nitsuwa ziriya kawai zaka ganshi yanayi cikin damuwa har saida yakai matsayin da yaji cewa bazai iya hakura yabar femi yana cutar da rayuwar macen dayake so harhaka ba

4yrs in a sexually starve marriage witou her knwldge is more like a death sentence in kirikiri prison with hard labour.

Duk da yana cikin matsuwa amma A nitse yay tunanin daukar mataki, wann karon baiyi yunkurin nemo temakon baban sa ba, na yarantar kawai yay cikin satin ya saka a nemo mai best private investigator a lagos snn ya bashi kudi yace anemo masa cikaken evidence dake nuna cewa femi is potent akawo masa..

private investigator yace masa wann aikin mai sauki ne dan har MRI scan na mahood din femi da calls dinsu da doctors da deal dinsu na bribe din duk zai iya kawowa kai harda drugs din dayake sha na gudun kota kwana dan kar vicky ta kamashi.

Tunda sukayi haka kayden ya fara sake ranshi dan yasan muddin yay sanadiyar da vicky zata san karya femi yake mata she will be free and will have no body controling her life shikuma anan ne xai samu daman nuna mata soyayyarshi dagasken gaske dan bazai iya risking rasata a rayuwarsa ba......

*************
5:30pm.

wani irin shiru koina ya dauƙa ayayin da zaka iya tsintar kowani mahaluƙi iyanzu a cikin gidansa wasu ma basu ko motsa daga inda suke ba sabida yadda hadari me yawa ya mamaye gari.

sanye da Dan multi colour dress me tsantsi dark blue and red colour me hannun spagheti riga da guntun wando halisa ta fito kafafunta sanye da roam about sleepers taraba lallausar suman kanta kashi biyu ta kitsashi tay dashi duk baya wanda ya kara fidda tsantsan kyaun shape din fuskarta dake baza kyallin sanyin yammaci.

saukowa take ahankli jin yadda koina a gidan ya dau shiru bata wani damu ba dake kwana biyun nan khalel baya zama, already sun fara presenting paper works dinsu na arab program dinsu kusan komi ya dau zafi ,tun azumi na biyar kowani rana zai shirya ya fita sassafe karfe shida, bashida dawowa Gidan ba sai wajajen karfe shida ko bakwai na yamma. ga yanayin weathern lagos ya sauya gabaki daya kusan ko wani rana sai anmusu ruwan sama me yawa ga sanyi ,toh ko acikin ruwan ne sam baida hutu dolensa ne sai yaje, Wani bin har tausayinshi takeji haka zai dawo gida ruwa yay masa lisss lisss da uban gajiyar da suke kwasowa acan duk da haka baiya fasa mata nata jinyar anan gida ba.

Kwana biyu lami lafya suke rayuwarsu duk dama me hali baiya fasa halinsa, khaleel karfin hali halisan kuma taurin kai hakanan dai suke fafatawa.

Tana karasa saukowa kitchen ta nufa ta bude ahankli snn ta shigo ciki da tunanin abunda zata girka musu kafin six yay.

Kafin ta fara aiwatar da komi ta bude windon kitchen din tuni rairayin sanyin iskar yanmacin da take bala'in busa wata iska mai sanyi da dadi tanamai sauƙar da tsananin ni'ima da kwanciyar rai ta mamaye ta ayayin da take kaɗawa game da mamayar zucyar dukkan wani mahaluki daya raɓeta a sanyin yammacin nan.

Lumshe ido tay jin iskan yanamai ratsata kafin nan ta bude ido ahnkli cikin sauke ajiyan zuciya me dan nauyi

drwar ta bude ta dauko wani pink bowl ta ajeshi a saman kitchen island sann ta debo garin flour
ta tankade da sieve ta zuba aciki, within few minutes ta debo kayan hada samosa wraps bayan ta gamashi ta kyalesu suna shan iska
Chapter 123 · 0% Book details