← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 257 OF 312

Sashe 257

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

immidietly tana saka hannu, mr shuaib omar ya saka hannu akai yay reviewing kafin ta bar wajen sharp sharp har masu rushe rushe da gyare gyaren wajen sunxo nan suka gama magana, na yadda zasu sauya ma wajen tsari dan bata son duk wani badluck din meenal yabisu a harkan business dinsu. Duk wani abu daya shafi meenal aranan tasaka akayi waje dashi

Bayan kamar awa uku ana neman wajen karfe 12pm na rana kafin nn hjy nadiya ta samu meenal a wani asbiti an kwantar da ita. Likitan ne ma ya kirata awaya dake dakyar aka iya bude wayar meenal din aka dau lambar last call dinta snn yace mata wai BP ne ya kayarda ita, zamanta wajen baifi da awa ba meenal ta farka da wani sabon bori, tace sam mahaifyarta tata ita ta jawo musu irin wnn toxarcin da walakanci babu kalar zagin maman nata da batayi ba .

Karshe hajy nadiya taji haushi ta barta a asibitin taje wajen wata kawarta neman shawara koda zuciyarta zaiyi sanyi.

Ta fice kenan wayar meenal din ya fara riinging ta dauki wayar ta leka da fargaba aranta taga private number ne da kyar ta danna sai ji tay muryan mai binciken ta...muryanta a shake tace kai kuma ina kake??
bai bata lkci ba ya bata adress, ta duba tagani saida taja wata arniyar tsaki me tsayi ganin zai dauketa 2hrs kafin ta isa wajen akwai nisa sosai can bayan gari..

babu jira ta sauka akan gadon ta fincike canulan ta zubarmusu awajen ta saka takalminta ta bar asibitin batare da tabar kowa yagane ta ba.

Motar haya ta dauka drop suka fara tafiya har wajen.....Tana Allah Allah su isa da tunanin wann ne mata dama na karshe da zatayi amfani da shi ta dawo dede.

Ata fannin Fadila kuwa bata da wani matsala face yadda zatay ta kawo halisa kamfanin, sanin yanayin halisan yasaka ta rasa wani bayani zata xo ta mata akan hakan,..
Will she ever accept her best friends company as her own? Karma tace bata aminta da haka ba
...amma kuma wani zuciyar nace mata ko ahaka aka tsaya ta dau fansa..but she dint want halisa ta get hurt by this
shiyasa batagaya ma uztz ba shima, ta kira uztaz din awaya yace mata sun fita wani waje da Halisan ynxu zasuyi meeting awani sabon kamfani amma da yamma ne zasu dawo kawai su hadu duka agidan halisan da dare...

Wani babban abokin business din Halisan ne ya bude kasuwanci na karafuna acan bayan gari and he wants her to really invest in it shiyasa sukaje can bayan gari dubawa agaggauce duk dama babban plan din ta na yau din shine zuwa offishin mahaifin khaleel domin neman taimakon sa akan sabuwar Addini data karba. Gashi tana son ita da khaleel yau sukai ga wani matsayi a soyayyarsu ta riga ta shirya kalamai da wajen da zasu hadu domin ta kawo karshen komi dayake barzanar hanasu kasancewa tare.

Sun jima Anan sosai har kusan karfe biyu na rana ita kanta halisan tana matsatsin son taga sun gama sabida tana son taga ta fi bada hanklinta akan addini dake hadiza ta gaya mata cewa in baka neme ilimin addinin dakyau ba bazaka ga saukinsa da dadinsa ba, hakama bazaka samu rahmarsa da dadin yinshi sosai ba. A wani fannin kuma tana mugun tausaya ma uztaz sosai, dan kuwa tun data amshe addinin musulunci salon yanayin shi ya sauya, he start to double his kindness for her, wani abun in yay har abun yana taɓa mata zuciya tana jin matukar tausayi da nauyin yadda yake daukrta da muhimmanci arayuwarsa sosai kamar dan uwanta na jini...

arnd 3clk na yamma suna daf zasu gama meeting dn tace masa daga sun tashi yaje gida kawai ya duba matarsa da yaronsa, she wants to spend time with khaleel da dare, amma sai in ita kadai zataje wajen dad din khaleel din ta dawo, dan aganinta uztaz need some rest with his family shiyasa take kkrin ta fitar dasu kasar waje hutun haihuwa in visan su ya iso zuwa gobe, shikuma harga Allah yafi jin dadi yaga yana tare da ita in all her important steps tunda taki tagayawa khaleel komi akan addini data karba, badon yaso haka ba amma ya amince mata.

Wajejen karfe biyu saura meenal ta isa wajen da gayen yake,witot wasting time yace mata gaskiya sai ta kara bashi kudi snn ya bata abun sabida akan binciken ta jawo masa asara dayawa kiris ya rage akamasa shiyasa ma ta jima tana nemansa a waya bata samesa ba.

Ko sauraransa batay ba zumudi yasaka ta kasa hakura agabansa ta bude files din tagggani dan tsabar notinan kanta sun kunce take taji numfashinta yana nenan daukewa cikin karfin hali da rudewa ta hau wani irin busashiyar dariyan mahakaukata da ta farayi da karfi ta fara musu hauka saida gayen ya tsorata ya riketa.

ba acikin hayyacinta ba take cewa take zata yi kisa yau dinnan she must kill sumone daga yadda take ma kasan she cant take it anymore.

Tafi awa awjen bata ckin hayyacinta tay kuka tay buge buge, kafin nan can gayen yace mata zai iya mata aikin kisan inzata biyashi..

She have no choice dan kudin dake acct dinta daya rage din beifi milliyan ashirin da bakwai ba wanda duk khaleel ne ya tura mata, haka ta tura masa fiye da half ahaka ma yanata mita saida ta bashi agogonta tace ya bita bashin millyan goma
sabida aikin express ne dolene yaja kudi gashi tace masa ita yau yau yanxu yanzu take son akashe mata matar she dont care kawai batason ace wann Maciya amanar ta kwana a duniya yau....NA KUDINE
08060712446 CHATS ONLYSURAYYHMS

Suna kammala hada deal din gayen ya dauketa cak a car dinsa suka nufo cikin gari tanajin kamar bazasu iso ba dan sama sama meenal take fidda numfashi har kamar zata
Hadiye ranta ta mutu tsabar damuwa da takaici datake shaqa..

hawaye masu tsananin radadi na fita a idonta tanajin tsananin zafi a kijinta dan Batayi tsammanin khaleel zai mata haka ba, batay kuma tsammanin abunda yake faruwa a bayan idonta ba kenan tsabar ta zubda hawaye fuskanta da idonta har wani kumbura yaay .

Adduarta daya shine a Allah yasaka ta kamasu yau Din red handed sabida shima ta dandana masa azaban harsashi a kirjinshi dan ya gane cewa ita ba acin amanarta akwana lafya.

A situation din datake ciki ji take kmr bazata kai gobe ba in bata kashe yarinyar nan ba, she did not even want to mention her name in her mind tsabar ranta na soyuwa da tsananin zafi..

suna isowa gari already karfe hudu na yamma ya wuce an doshi biyar wani boyayyen gareji mutumun yakaita ya bude wata computer suka fara tracking location na target dinsu.

Meenal na jeka ka dawo tanajin kamr bazai gama tattara bindiga da explosives dinsa su isa location din ba..

Suna zaune awajen ya kira wani gaye yazo ya karbe small small time bombs da explosives ya wuce dashi akan zaije ya saka a acikn motar target din Kafin nan su shirya su isa wajen da zasuyi traping inta dan meenal bazata iya hakuri ba kusan dolene ay kisan nan agabanta tana so ne sai ta harbi yarinyar da hannunta inta kasheta kafin tay exploding ta mutu su hada ido ta san cewa itace nan meenal Ali talba ta kasheta.

3:40pm ana fita daga sallahn asr khaleel yaga sakon Halisa a kan screen din wayrsa yana budewa yay murmushi sabida duk sanda zata turamai sako saita masa sallama cikakkiya, she is inviting him to a candle night dinner at her house tonite yau tun da asbhi ta shirya komi nata sabida yanayin rabuwar cin amana da kawancen hadiza da shemau ya ginu kuma ya ruguje akai bakaramin bude mata ido da kwakwalarta yay ba.

tasha jin wasu boyayyun kalaman da meenal take furtawa akanta ,taganr cewa meenal still feels she owes her a debt dan ta taimaketa acikin tsanani ta kawo ta lagos, sai take ganin tunda har ta riga tacire ma meenal iya abunda zata bata na kudi akan hakan, Koma yaya ne dai its time ta fito fili ta gaya mata gaskiya akan abunda ke ranta inyaso su rabu...
But she had to leave this friendshp with no guilt or grieve na cewa ta yaudareta ko ta cuceta.

Shiyasa ta shirya fara gaya ma khaleel komi, she want him to knw dat she is no longer meenals friends,gaskiyan su vicky ne "selfish ppl live longer" duk yadda kakai da juriya da hakuri wata rana dole u have to put urself first befor anyone elses, a zahirin rayuwa shine kowa kansa ya sani, Dan Adam shikansa abunda baxai iya daukawa ba Amma xai ce ma wani ya dauka, in yaki kuma zaije masa baida hakuri. Toh me za'ayi da munafukin aboki ko mutum me fuska biyu???? Manxon Allah tsira da Aminci su tabbata agareshi ya siffanta mai fuska biyu a matsayin mugun halitta munafukin mutum kuma hatsari yake dashi snn kuma wutarsa fa tana can kasar na kafurai...

Wayynn halayen biyu ajikin dan ada kusan dolene ka nesanta kanka dasu sabida halaye ne masu tsananin muni da cutarwa. Wanda ixuwa yanxu duk ta gamsu cewa meenal tana dasu kuma bata ga alaman zata sukesu nan kusa ba.

Bayan haka ta na so koma yaya ne dai ta amsa masa cewa zata aureshi khaleel ayau kodan hanklinsa ya kwanta na iyayensa ma ya kwanta

..tun yana karanta sakon nata jikinshi ya bashi hakan sai yay murmushi me sanyi Ahankli ya lumshe idonsa Yace Alhamdullhi, Allah na gode maka, "yess!!..Haka nan Yagama murnansa sann ya rubuta mata sako yace tagaya masa inda take shi xaixo ya dauketa ya kaita gidan amma sai bata amsa shi ba.
Chapter 257 · 0% Book details