← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 152 OF 312

Sashe 152

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryanta harna rawa tace wat do u mean what i have done?....tsaki ya ja cikin katseta snn yace kin makance ne da bakiga konata da kikayi da ruwan zafi ba.

idonta a rufe da kishi tace ohh pls khaleel Ni ban konata ba, tsorata kawai tay ta zuba ruwan tea ajkinta dan anganni na shiigo..

cikin katseta halisa tace "tsorata dan an ganki kin shigo ko? Amina u got to mind ur language.

Dataga ran halisan ya baci kuma sai ta sauko ta sassauto cikin sauri

"kai babe nifa ba haka nake nufi ba, gani nayi kamar zai miki dure shine nashigo da sauri bansan zaki tsorata ba.

Halisa ta mugun hade rai
"Hmmm,Nikam shikenan, i am no longer intersted in the tea. Awani irin ynayin sanyin shagwaba ta kallesa ahankli da muryan daga ita sai shi sukaji tace mishi nice tea doc..! Daga haka ta shiga bayin gida ta kulle kanta aciki.

Meenal ta rasa me halisa ta gayamai da bataji ba

Khaleel yay murmushi aransa, snn ya juya ya kalle meenal din Tun beyi magana ba tace khaleel waimesa kakeson hadani fada da halisa ne yanxu zata dauka ko zarginta nakeyi.

yace wann kuma ke kika sani, inhar kika sake bata sha tea din nan ba ranki zai baci,..daga nan shima ya fita ya bar mata dakin

Magiyan duniyan nan tay ma halisa amma taki kulata gashi abunda tagani gabaki daya yaki fice mata ido, karshe da hawaye ta koma room dinta ta kwanta cikin rudani. Can snn halisa ta fito ta zauna akan couch tare da rage fitilan room din ta bar guda daya cikin sauke nannauyar ajiyar xuciya tana murmushi tace okay lets see who is going to be soo frustrated in this house. shanye shayinta tay hankli kwance sann tay bacci......washe gari 6:30am.

wani irin shiru koina ya dauƙa ayayin da zaka iya tsintar kowani mahaluƙi iyanzu a cikin gidansa wasu ma basu ko farka daga bacci ba,rairayin sanyin iskar safiya ce take bala'in busawa wata iska mai sanyi da dadi tana sauƙar da tsananin ni'ima da kwanciyar rai tana kaɗawa game da mamayar zucyar dukkan wani mahaluki daya raɓeta a sanyin safiyar.

Khaleel ne kacal a zaune acikin massalacin ƙofar gidansu,an idar da sallah yana zaune a inda yay sallahn rike da qur'ani dan shi dama karatun qur'ani yafiye yi da safe, hanklin shi da nitsuwarsa gaba daya naga kan karatunsa ne, wanda yakeyinta a cikin sanyin nitsuwa da jin dadin fidda sautin muryanshi mai tsananin dadin sauraro.

Light grey jallabiyace ajikinshi wacce ta haskashi sosai, yana idar da karatun ya tashi ya bar masjid din ya nufi cikin gidansa Kai tsaye ya haura sama room in meenal, yana bude kofar dakin can ya hangota akan makaken gadonta tana tikar bacci har da minshari. agogon bango ya kalla yaga 6.45am na safe kallo daya zaka mata kasan batamayi sallah ba, A nitse ya daga kafafunsa cikin yar sauri domin isowa ixuwa bakin gadon sede ko taku biyu baiyi ba yaci tuntube da Takalmin da ta saka na jiya data watsar dashi a tsakiyar dakin da sauri ya rike kafar sabida zafi tare da kare ma ilahirin dakin kallo, kayane here and der, wasu akan table wasu akasa wasu akan gado takalmi jaka jewries duk suna kasa kowa da mazauninsa, ga used towels dinta akan vanity chair cikin dakin dai kamar na mahaukaciya, Ita yar gatace ba'a koya mata tattalin room ba sabida aikin gida na masu aiki ne. Ahakama gani take kamar zaman ta anan gidan khaleel tana kokari sosai tunda tana iya hadama kanta ruwan wanka har ta shirya kanta, dan inba dan son khaleel ne zai sakata zama a wann yanayi ba da har duniya ta kife bazata yi irin wann rayuwar bama.

Karasowa bakin gadon yay ya zauna yana dan kallonta kafin nan ya shiga tapping gefen gadon da kyar tajiyoshi ta bude ido ta kalle shi cikin gigin bacci takejin shi yana cewa kinma yi sallah kuwa??? Dada runtse idonta tay gam kafin nan ta bude cike da bori da bambami Dan ta mugun tsanar a katse mata baccin safiyarta.

Bai kyaleta ba kuwa har saida ta tashi da gigin baccin da komi ta shiga bayin gida tana ja masa tsaki, tunani tay ko zata masa wayo ta jima acikin bayin har sai yabar dakin snn ta dawo ta cigaba da baccinta amma ina jin muryansa datayi a bakin kofar bayin yasaka ta hakura ta debi ruwa kawai ta shasshafa a fuska hannu da kafa ta fito rana tura baki ganin har ya shinfida mata sallaya.

Kallonta ya dingayi jikin shi nabasa awani abu ganin wasu wajeje a jikin nata basu samu ruwa ba
da har kamar zaice mata ta koma suje tay alwalan agabansa yaganai sai caraf cikin tsaresa da harara tana cewa "Sallahn ma sai ka sakoni agabane?

Kafin ya amsa har ta jawo gown din data saba sawa ta zura cikin mita
Tana cewa"..pls u need to go, bagashi zanyi sallahn ba..meye ne kuma.. mtss. Kasa kasa yaji take cewa inma wani abu kake nema awajena bazaka samu ba, tana tsakin tana hamma, Cikin hade rai tare da katse bambamintan da wani irin kallo, Yace kwantar da hanklinki inbadan hakki bane akaina nasaki kyi ibada da bazan zauna for gud 1 mint cikin wann dattin ba, cmon kiyi da jikinki Ki kammala sallah snn ki tattara kayan nan dakika watsar akasa haba Amina ki jibi makwancinki kamar ba mace kike ba, jakr dake kusa dakafarsa yay ball dashi yanayinsa cike da masifa just take a look at ur room for god sake!...

da wani kalar ruwan masifa ta juyo idanunta kamar zai xube kasa tsabar harara "a'a a'a malam dakata min and pls don't lecture me on anything, wann ai lefinka ne, kai ka jawo ayi kazantar ehe, ai bakaso ganin tsaftar bane agidanka shiyasa ka ki akawomin me aiki, tun farkon auren mu mumy na tace zata biya, nima i said i will pay amma kaki, tou ynx kuma ina ruwan ka da saina maka wani aiki agidan nan mutun yana da kudinshi sai bazai amfanesa ba .

girarsa na sama a dage Yace tou sannu me kudi, ke bazakyi girki ko tattalin gida ba, fine, but "will u also pay another woman to give me a child or atleast satisty me in bed????...bawai bazan iya barinki kiyi duk abunda kikeso bane but trust me amina, bakisan
meya kawoki gidan miji ba tukuna.

Wani irin rolling idanunta tay akansa yadda zaka san maganan ya cakketa a zuciya, a mugun fixge ta dauke kanta akansan takuma kallon gabar cikin danne zucyarta dan karta amsa shi tatsokalo makanta wata babban maganan da batason ji wato na batun haihuwa ,

cikin girgiza kai tace hmmm ince dai duk akan sallahn ne shine zakana gaya min baqar magana? Toh shikenan,.. daga nan Allahu akbar" kawai yaji yaga wai harta tada kabbara karkada kansa kawai yay ya fita a dakin batare da yace mata komi ba.

Fitarsa baiko da secnd goma ba ta dago daga ruku'an snn ta bar kan sallayar da sauri ta dauki key ta tura kofar ta kulle kanta taciki ta haura kan gadonta tana huci tana tuna rayuwarta na baya na cikakkiyar yar gata yadda komi mata akeyi bata tabuka komi, cikin hakan after a while wani baccin ya sake daukarta abunta.

Bangaren khaleel din kuwa yana komawa room dinsa baiyi wata wata ba ya fada wanka maganganun halisa na jiya ne kawai ke dawo masa kansa..

Kwantaccen sumansa data sha gyara da mayu kan qamshi tay baki kirin me kama da na sadaqa yalla yake tajewa agaban madubi yanakan tunata yaname sakin murmushi duba da yadda ta tsara musu ranar gabaki daya.

saida ya kammala kimtsa kansa yay tass tass yana zuba qamshi snn ya bude closet dinsa ya zaro Wata cool milk plain transparent yard an masa dinkin fitted jumfa datay cas cas da dirin jikinshi dake kayan shararar ce kusan duka inner wears daya saka taciki takamfanin calvin klein ce, zama yay bakin gado yana saka takalmin shi na dolce, sann ya kafa hular Dara ppr red in colour data mugun dacewa da kayansan sosai.

wajajen karfe 9.00am ya fito daga room din daga wallet dinsa sai key din motarsa ajikinshi duk sanyin qamshin turarensa me tsada na Guilty absolute gamutse da bold rasasi ya baza ilahirin gidan..

kai tsaye ya nufi dakin halisa a tunaninsa duk tagama shiri, yana tafiyarsa cikin nitsuwa yana duba watch dinsa har ya iso, yafi minti biyar atsaye abakin kofa yana knocking ba'a amsaba can snn ya dan tura kofar sama sama ya leko ciki nan yaga wayam bata ciki, jakarta da kuma qamshin turarenta na rebelle by rihanna yasaka yasan da cewa bata yi nisa ba.

Waje ya nema ya zauna akan couch dinta kafarsa daya akan daya, wani irin kyau pose din yay masa msmn yadda agogonsa da fararen idon sawunsa suke haskawa, kana kallonsa daga can kawai accesories nashi sune zasoma dauke maka idanu da hankli, cikin kankanin lkcin ya kare ma ilahirin dakin kallo ganin inda koinanta yake kintse tsaf tsaf kan gadonta ta lailayeshi da tsaftaccen zanin gado tamkar ba ataba kwanciya akai ba.

after like 3 min ya duba agogonsa duk a tunanin sa ko taje kawo makanta coffe ne Jim kadan yana zaune sai gata nan ta shigo cikin nitsuwa da farin tray madaidaci a hannunta, wani elegant black dubai abaya ne ajikinta me hade da kimononsa ajiki wanda kana ganinsa kasan branded ce, ba wani kwalliya me yawa tay ba amma sosai ta tattake suman kanta tay acuci dashi, snn ta rufe kantan half way da veil dinsa yadda sumanta yay coil ta gaba gaba har wani kyalli yake sosai..

suna hade idanunsu waje guda ya mike tsaye yana sakin wata sassanya kuma rudadiddyar murmushi batare da ya shirya ma hakan ba.
Chapter 152 · 0% Book details