← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 258 OF 312

Sashe 258

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

4pm ta fito tareda uztaz da niyyar kama hanyar da zai kaita offishin baban khaleel, sun isa gaban car dinsu din kenan Wayarsa ya fara kara, yana dubawa yaga sakon daga benue ne, assistant commisioner of police na lagos yana nemansa agaggauce a da cewar sun samu wani information akan kawun halisa, sanadiyar hakan yace ma Halisa shi zaije yahau taxi kawai yaje shi police station ita sai taje wajen baban khaleel din idan ya dawo zai gaya mata duk abunda ake ciki.

Duk yadda taso suje tare amma yaki sam, baison suje ace kawun nata ya rasu, ko ya shiga cikin wani yanayi bare abun ya daga mata hankli, he wanted to protect her from geting hurt, his last words to her was. _"bazan iya barinki kije kiji wani abu da zai daga miki hankli ba, Inkin daukeni dan uwan jini, then u shud let me handle our family affairs,nayi miki alkwari zan yi kkri inga cewa na toshe miki duk wani baqinciki a duniya_

A Babu yadda ta iya ta hakura sai tabar masa motarta tace masa zata jira khaleel yaxo dama yace zaizo ya dauketa bata amsa shi ba. Tana kiran khaleel din kuwa ya amsa mata cewa zaizo cikin nan da minti na ashirin.

Ya dau car din kenan zai doso gate sai ga fadila nn itama tana kiransa a waya akan batun meeting dinsu na karshe da zasuyi nan ya dauki wayar sukayi magana yace mata babu damuwa ta samesa A hanya zai dauki halisa ne yakaita gida saisu wuce can.

Dama ba wani nisa dashi take ba nan ta fara binsa
tana driving ahnkli tana Dan magana awaya da mahaifyarta duk akan abunda ya faru yau tsakaninta dasu hajya nadiya da meenal da safe.

duk saurin da Uztaz yake bai bar halisa awajen ita kadai ba har saida ya jira Khaleel ya iso wajen cikin wata sabuwar formatic matrix jeep datasha tinted sosai bazaka taba iya gane wanda yake ciki ba.

Tun daga isowarsu ya hangosu a tsaye da uztax sunata dariya tare gwanin ban shaawa, da alama suna video call ne da matarsa da new born babynsa. Khaleel Ya nada natural zafin kishi me yawa akanta amma He totally understand dat uztaz is filling this part of family experience that she neva gets to see in her life.

Sauka yay ya doso su yana murmushi, yay gyaran murya duka suka kalleshi, uztaz ya mika masa hannu suka gaisa, halisa na tsaye tana murmushi me sanyi yauma yaga duk batazo jikinshi ba, kwana biyun ya lura ta canza,yanayin dressing din nata bai damesa ba amma these two days da suke dan haduwa da safe ko da dare tsakanin jiya da yau her bhrs na zuwa jikinshi are slowly changing kmr ba ita ba...

lura tay da yadda Yake kallonta yana murmushi cikin sanyi murya tace "hey...i am heading sumwher ai sai mu wuce ko? Yace yes ma'am,..
nima dai fadila tana jira na, ajeki kawai zanyi we wll catch up later..tace okay, yace lets go...uztax ya mata sallama, ya juya shima ya shiga car ita kuma khaleel ya bude mata motarsa ta shiga ciki..

hira suka fara me sanyi akan kayan data saka Ajikinta dan dolce and gabana kimono ce coffe brown colour amma bakaramin kyau yay mata ba musmmn ma data rufe kanta da veil dinsa gabaki daya.

Wani hira me sanyi me abun dariya ke wakana atsakainsu khaleel was driving slowly sabida wani kalman love din in aka gayamai ji yake kamar zai narke akan seat din nasa dan dadi.

Ahnkli uztaz yake binsu abaya har yazo ya gaji da slow ride din da suke ya wuce gabansu kadan...

Daf zasu haura kan wani karamin bridge da ake kan gyarawa can suka ga fadila ta bullo itama anata motar acan tagaba dama can Halisa bata son khaleel yasan da cewa zataje wajen babansa dan haka ta fara matsa masa akan cewa yabata car dinsa ta karasa dakanta gida inyaso shidin yabi fadilan suje sugama abunda zasuyi sai yaxo ya sameta a gidan zata jirashi anan.

Gabaki daya murna da zumudi ya cika masa zuciyarsa ganin alama dayakeyi atattare da ita na tunanin cewa tabbas yau zata amshe batun aurensa, duk ya kasa nitsuwa yanajin inama ace daren har yayi.

Sun hauro kan tsohuwar gadan kenan basu wani nisa ba Halisa ta kira fadila a waya tace mata ta tsaya anan baki baki su karoso ahnkli fadila tayi parking sabida yadda motarta yake wani karan da batasan dga ina yake fita ba, daga can meenal da mutanen ta suka leko tabayan wani dutse dake wajen acan sama suna kimtsawa dan tun tuni suka bibiye fadilan abaya suna tracking dinta as target dinsu Har suka kawo nan tare.

Waje yay sanyi dake biyar ya fara gaucewa, meenal na rike da bindiga da wani abun kallo nan ta hango uztax acikin motar halisa shikadai yana kan tahowa tsaki taja tace kaji wann jaki wawan shikuma ina zaije anan

Tana cikin bayanin ne ta hango car dinsu khaleel abayn nasa amma dake batasan motar ba kuma tinted ce sai bai darata ba..

She had her focus on her target, kuma ta qudura aranta cewa sai ta kasheta kafin ta samu wani nitsuwa, rashin sake isasshen kudi yasaka mai bincikenta bai zage ya mata aiki ba kawai sai yay amfani da last last contact na khaleel ya kawo mata evidence na iya Abunda ya gani daga ciki kuma shine fadila fadila and fadila, gashi ya daddauka musu hotona tare most atimes duk haduwarsu na meeting ne, in khaleel yaje ko in ita taje, he was able to convinse meenal cewa wann matar da mijin nata yake son ya aura din fadila ce.

meenal kuwa tana gani ko sekan guda bai dauketa ba ta Aminta da hakan sosai aranta Duba da abunda fadilan ta mata da safe, a tunanin ta fadila ta fito ne dan tay haunting inta, tunda ta kwace mata kamfani shine takeso ta kwace mata mijinta shima, tun dazu take tuna lkcin da fadila takece mata bataga komi ba tukuna yanzu ne ma zata fara tafka asarar abubuwa masu muhimnci arayuwarta.

babu mutane awajen sosai dake hanyar yadan fita a gari kuma under construction ne,Motar su halisa na tsayawa, uztaz ma ya tsaya, khaleel ya bude ya sauka yace ma Halisa drive safe bbygirl zan kiraki anjima. ahnkli Ta gyada masa kai tana murmushi

kafin yazo ta wajen sai ga uztaz ya sauka kasa yana tahowa wanda hakan yasaka bata fito ba tanajiran taji me zaice mata, idon meenal na kan khaleel har ya fara tafiya wajen da motar fadila tsaye dan ko kashe engine dinta batayi ba.

he was smilling cowishly in his mind thinking of wat to wear tonite to impress halisa ita kuma meenal dake kallonsa ta abun kallo sai kumbura take da tunanin wa fadila yake zuba wnn uban murmushi, wani irin abu taji yana sauka ajikinta kamar wuta na cinta bal bal bal ball. Ta juya idonta a kafe tana nishi nishi kamar wacce zata dauke, Zuciyarta a dafe tace ma gayen in 3 mints zata ce mishi "go" snn karya sake ya bata mata lokaci Daga tace masa go tanason taga ya harba bindiga izuwa kan motar sabida explosive din da duka saka acikin car din ya tashi dan jitake kmr ma bazata iya hakura ba kuma

Setin remote din bomb din yay hanklin ta gabaki daya ya koma kan khaleel dake tafiya akab titin, har uztaz yaje ya bude ma halisa mota ta fito ta dawo driver seat ta xauna 3 min on dot baifi taku hudu zuwa biyar khaleel ya isaga motar fadila ba meenal taja wata balaman nunfashi Kamar wata tsohuwar soja ta kalle gayen a dake snn tace blow that bitch up now...kafin kace wani abu dai bauuuuuu bauuu, Motar fadila yay wani irin kara, tare da yin tumble izuwa can sama, wani gigitaccen kara fadilan tay, dan ji tay kamr wani iska me mugun karfi ne ya dagata can sama xai kadata a cikin matsanancin tsorata tace innailillahi wa inna ilaaihi rajiun..

..motar Bai kama da wuta ba sabida low quality explosive ne karfi da karar explosive din ya jefar da khaleel gefe ya hada kanshi da karamin dutsi atake ya suma gabaki dayansu awajen suka rikice lkcin zuciyar halisa kamar xai faso waje daga kirjinta, a razane ta kira sunan khaleel din da wani irin rikitaccen murya lkcin daga uztaz din har Halisa kkrin kallon wajen suke uztaz yana daga idonsa sama yahangosu meenal acan saman wani dutsi suna kkrin harbo wani explosive din ganin wanda suka saka baiyi aikin da sukeso ba.

Kansa yaji ya rikice ga motar fadila can yana tumble ga khaleel akasa ya suma kafin ya dawo hayyacinshi yaga Halisa tabude motar ta diro da mahaukacin gudu zata je wajen khaleel, shikansa uztax baisan ya akayi ya mata daukar cak ya maidata cikin motar yabi ya kulle da security ba.

Ihu take tana kuka a rikice tana cewa uztaz ka bude ni mana ka bude ni pls pls let me go to khaleel Please let me go to him. uztax what is wrong with u, fadila, fadila..please let me out.

Uztax ya kalleta ta waje idanunsa wani iri yace mata i am sorry, i cant let you risk ur life, zatay magana cikin katseta muryansa na rawa rawa yace Dan girman Allah ki zauna anan xanje na kwaco miki khaleel da fadila.

...duk ihun datake masa akan ya bude mata kawai amma baijita ba. Saima hakuri dayake kan bata yana cewa i promise to protect u, so i cant let u risk ur life i am sorry..

Yana juyawa da gudu halisa ta kara birkicewa da tashin hankli da kuka
Khaleel uztax fadila duk ta kira sunayen nan yafi dau akirga badon motar sabuwa bace kuma tana da krfi da tuni ta balla glass din ta fito.

hanklinta baima kan mutane daidaiku dake kkrin parking dansu taimake su kuka kawai takeyi shar shar da hawaye tana rokon abudeta wasu yan maza ne haka yan matasa suka tsaya suna kkrin taimaka mata Dayan gayen dat looks rugged ya saka master key dinsa yanata gwadawa akan motar agaggauce
Chapter 258 · 0% Book details