← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 312

Sashe 122

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin shiru yay yawa yasa ta kara kutsowa ciki sai can ta hangosu kan wata katuwar turkish capert milk colour kalar manya manyan kujerun dake wajen suna zaune akai suna hira da kayan karyawa agabansu ga wani irin luxurious golden colour incense burner agefe na tashi da hayakin original Sandal flakes da sanyin dadinsa ya kama koina musmmn ma da Ac yake dada hurashi yanamai kama har jikin labulayen wajen

right from her eyes zakagane yadda yanayin sun yay affecting mind dinta yasakata jin sun mugun burgeta sosai, wani sanyi da sakewa ta soma ji aranta dan hafsa tana mugun son harkan gayu da tsafta arayuwnta bana wasa ba,..

Kanta ta sauke kasa tana boye sautin ajiyar zuciyar daya kufce mata ta iso gabansu da sassnyr sallama abakinta

abazata Suka juyo suna masu amsa ta da sakin fuska da murmushi me sanyi.

Bayan sun gaggaisa sun ji lafyarta Kai tsaye hajiya binta ta mata bayani snn ta gaya mata cewa nan da sati uku ne zata fara schl din sabida anje hutu fresg session ne zasu fara da ita..

Inna hajiya ta sauke boyayyr ajiyar numfashi bata sake ce mata uffan ba sanda tanemi waje ta zauna snn tace mata tna son magana da ita

..duk da nauyinsu datakeji batayi musu ba ta zauna adan rakube agefe dan duk halin da ake ciki alredy hjy binta ta zayyana mata komi.

..wani shirun minti biyu ne ya gifta a tsakanin su nan inna hjya tay gyaran murya ta juyo ta fuskan ce hafsa snn ta soma ma hafsa din magana cikin tausahiyar muryan ta wanda yy kama dana fada tare da lallami, tace mata kaf duniya babu maraya sai rago dan haka dagewa take son taga tay dan ta kwaci mutuncinta da darajarta akowani fanni na rayuwarta da cewar suna nan su zasuna dorata bisa kan hanyar samun hakan akan lkci.

Addini, Ilimi, tsafta, juriya, hakuri, iya girki, da rike darajar miji da iya kula dashi shike bambamta tsakanin cikakken mace da wacce ta rako mata.

Acewar inna hajiya su dacan ma auren kawai aka musu basu san mijinsu ba saida aka kawosu dakinshi dan haka yanayin auren da aka mata da mahmud ba dalili bane da zai sakata tay sanya wajen kintsa kanta da rayuwarta na nan gaba da zatay dashi.

Duk wani raunin da hafsa ta cusawa ranta akan aurenta mahmud saida inna hjiya ta warware mata kashi 70% daga ciki a zamansu na farko.

Tace mata qaddara ce ba komi ba, dan haka itace zata jajirce tay shaping din qaddarar yadda Allah zai ji dadi ya saka musu albarka aciki..

Inna hjiya tace mata mace itace jigon da namiji ko mata dari mahnud yake da shi idan har ta jajirce wata rana sai labari.

kaifin nasiharta tuni ya hau shigar zuciyarta ta yanaimata debi da soyayya irin na uwa zuwaga yarta datake matukar kauna da kuma jin tausayi..

Maganganun inna hajiya sosai yasata tuno da nata mahaifiyar hawaye ne suka kwace da qarfi acikin idanunta sukahau zubowa, ta tuna tunda tazo duniya tsakaninta da ita kullum nasihace

saurin share hawayen da sukekin dena zubowa tayi dan ta saurari inna hajya da kyau

A hankli harta dan samu nitsuwa, sosai ta gane cewa akwai masu kudin da sukagaji ilimi kuma sukeyin amfani da ilimin zaka samu sam basada matsala wajen muamala dana kasa dasu sam sam.

Maganganun da take mata a fayyace suke babu wani boye boye

Tunda akace mata hafsa marainiyace babu uwa babu uba Hakan yasa tahau gaya mata gaskiyar rayuwar aure a tsirarsa, Babu wani boye boye ko sakayawa straight to point take fayyacewa, in tay mata waazin sai tace toh ga abunda ya dace dake ga abunda bai dace dake ba

Snn tabi ta cusa mata jin cewa sun daukota nan ne donsu tayata yaki da maraicin rayuwarta amma badon su tallafa mata kadai ba sun san hakanne zaisaka ta dena kallon kanta a matsayin banza, kaskantaccya ko raunataccya wanda bata da gata.

da haka ta rinka karfafa mata jin cewa zatafa iya yin rayuwa mai dadi fiye da wanda take tunanin bazata taba samunshi ba

She stressed dat she must try and put her fears behind her back kuma a shirye suke da su riketa anan din kamr yar cikinsu.

Godiya hafsa ta rinka musu har tana sake sheshhekar kuka dum hawayen da suke kan sauko mata sun wanke mata fuska da alaman maganganun sun shige jikinta ta kuma ji dadin yadda inna hjiya ta mata filla filla, kusan zuciyarta a shirye yake data bi wannan salon nasu don itakanta harso take taga ta dawo kamar yadda inna hajiyan taje fada wati cikakkiyar mace data san kanta.

Alokaci kalililan taji xuciyarta ya wani cikke da shaukin hakan .

Suna cikin tattaunawar hjy binta ta umarceta da akan ta karya kafin nan su san me zasuyi acikin satin ukun nan

Bawani sha'awar cin abincin takeji ba yanayin sakewar su da ita yasa ta daure ta ci abincin fiye da na kullum.

Bayan nan hira kadan sukayi snn ta koma room dinta tanata tunani akan abubuwan da inna hjya ta gaggaya mata...

Cikin sassanyar nitsuwa da samun cikakken gamsuwa acikin zuciyarta take sauke nannauyar ajiyan zuciya

She will try and be that great woman, koda ma ace mahmud ba mijnta bane anan gaba, itade zatay kkri dai taga ta cire kanta a cikin salon matan da basu da class wanda tsabar rashin darajars maza ke iya dauke ido akansu cikin gaggawa.

Bayan kwana biyu koyaushe takan fito da safe su gaisa suci abinci yau bayan sunyi sallan ishai hajy binta tay hamdala Alhamdullhi ya kamata hafsa ta soma shiga kitchen dan itama ta koyi Abincin zamani da kyau it wll be better for now sabida babu batun xuwa makarnta ana hutu.

Inna hjiya tana murmushi tace "aiko ban dan haka bama kinsan gidan mijinta zata wuce daga nan, kamata yay in zata koma ta koma mishi da makaman yaki..Ko yaya kikagani hafsatu?

Tsabar kunya kanta ta sunkuyar can can kasa ta gyada ma inna hjya kai a hankli tana murmushi.

Hajya binta ta riko hannun surkuwanta dake tashi dakyar tace mama tashi muje room ki kwanta yau kingaji fa just leave evrything to me..

yadda inna hjy take nishi nishi dakyar tana surutan tsufa yasa dukan su sukahau dariya.

Suna mugun jin dadi aransu sukaga hafsa tana kkrin yin dariyar duk dama alamar dariyar kawai zaka gani ayanayinta bawai takan sake tayishi bane har can can.

Kafin hjy binta ta dawo ta samu har hafsa ta tattara empty dishess din dake dining ta goge wajen yayi fesss da mamaki ta shiga kitchen ta bude kofar a hankli ta shigo bata lura ba.

Samunta tay agaban sink taba wanke wanke.

Da gyaran murya hjy binta ta karaso Cikin jin kunya da tsantsar yanayin girmamata hafsa ta ja baya.

Hjy binta ta amshe aikin kitchen din dakanta tanayi suna magana tana gayamata abubuwan da zasu nayi kowani rana

Washe gari da safe hafsat ta fito dan yau wekends ne tamkar house sanitation sukeyi cikin haka ta soma janta da hirarra ki, tana dan sakata kana nan aiki miko min kaza aje min kaza goge nan share nan har hafsa ta sake jikinta daa gidan da haka da haka taci nasarar jefa kanta cikin aikin kitchen din sosai.

anan ne ma hjya binta tasoma fahimtar me ta iyada dame bata iya ba fannin abincin gayu.

Babu laifi Hafsa ta iya girke girke dayawa musamman wanda ake koya musu sabida aikin su na house girl.

wasu kuma ta iya amma bata taba gwadawa ba.

Haka hjya binta ta sakata agaba sukayi doguwar list na kyafaffun abincin da zata koya masu rai da lafiya, kama daga kan girkin abinci, izuwa grills da small chops, kai harma da drink kala ka hade da few inter continental dishes.

Bayan sun kammala da wann suka fito cikin gidan nan ma hajy binta ta hau gwada mata yadda ake yi in za'a tsaftace manyan faloka da sauran wajaje har suyi kyalli suna Baza qamshi me kama zuciya da jiki irin na isasshun mata.

Sosai hafsa ta bada hanklinta tanamai kallon
Salon da hjy kebi wajen kunna incense dan ya kama waje, suna da special mopping humra da suke zubawa a floor na rooms dinsu har toilet da kitchen wanda daga ka shigo dai zakaji kamar ginin gidan ne akayishi da qamshin turare.

Kokadan hafsa batajin gajiya aranta dan abubuwane da suke mugun burgeta.

Kwana biyu abunda suka dingayi agidan kenan iyaka intan gaji a kunna mata kallon fina finai masu dadi ta dinga kallo wasu sukan sakata taji ta karu da ilimin rayuwar aure wasu su sakata jin tausayi.

Bayan yan kwanaki A gidan kowani rana musamman da safe akeyi ma hafsa kitchen classes na musammn

Hajya dakanta take shiga kitchen tana koyama mata varieties na kalolin abinci na zamani, small chops with evry delicious recipes na daidai da ajinsu na masu shi har a internet takan bibiye shafukan da suke sarrafa abunci just to learn sumtin new...

Inna hjya tay ta basu dariya kenan dan itace me judging din duk wanda aka kammalashi

Kafin sati ukun nan ya cika saiga fuskar hafsa yay bul bul ya ciko ta dadayin wani irin smooth
jikinta na dawowa ahnkli

rayuwarta agidan tamkar mafarki dan bakaramin dadin zama dasu takeji aranta ba, Babu abunda ke burgeta kamar yadda ake koya mata tsafta da girki, Wasu abubuwan girkin ma anan kawai ta soma sanin cewa akwaisu kuma suna existing a duniya..

Wata rana kawai bayani hjy binta take mata na yadda akeyin abu saita kyaleta dashi, to kafin ta leko zata samu hafsa ta dage hartayishi zak koma fiye, sumtimes kuma sai inna hjya taci gyaranta kadan.

intaje gyarawa inna hjiya daki haka zata yi ta bata labarin yadda dacan suke kwalliya ma mazajensu a zamanin dacan, yadda take ganin yawan suman kan hafsa masha Allah babu irin recipe da bata bata na gyaran gashi ba.

Ana daf za'a fara azumi Yau Tun Karfe bakwai na safe hafsa ta fito kitchen din tana famar aikace aikacenta na karshe dan baifi saura kwana uku tafara zuwa schl ba.
Chapter 122 · 0% Book details