← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 223 OF 312

Sashe 223

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta share hawayenta tace fine..sorry, nice nake ta kiranki da layin mumy dama wayata ce ya dan samu matsala, Atakaice Halisa tace mata okay can you speak up now dan bacci nakeji sosai am so tired..

cikin katseta da sauri tace "tired? Where are u..nazo gida akacemin kinyi tafiya.. are u with khaleel? Muryanta a rararabe tafada..

Cikin sauke ajiyayyen numfashi halisa tace no, i am at home..

hajya nadiya tace karya kike dan ubanki wane home din?..makaryaciya karuwa kawai...ki fada mana inda kuke kawai..

Rai a mugun bace meenal ta juyo snn tace mum wai me haka ne kibari mana tagayamin inda take muji hala ko khaleel nata wajen wai kodan na karbi wayarki ne zaki min walaknci..

Halisa najinsu batace komi ba suka gama haurawa juna anan ne ta fahimce cewa neman khaleel din kawai sukeyi taja tsaki aranta..

meenal tace Halisa dan Allah kiyi hakuri mum is just perannoid. Kikace kina gida? Wani gidan dan jiya agidan muka kwana.

Murya ciki ciki halisa tace well, i am at my house In victoria island Snn kice ma hjyar taki bata ban ajiyar mijinki ba tukuna bare nayita mata yawo dashi. inda nasan abunda yasaka kuka kirani Kenan da bazan dauka ba, uve already ruined my sleep. Tana furta hakan ta katse wayar da guntun tsaki.

..meenal tay tracing call din taga eh lallai halisa tana victoria island din ne. Bata Kuma yanke hukunci ba still saida ta kira sectary na HRM ta mata tambayoyi anan tasan cewa anyi bikin jasmine dan tasan halisa bata da tarkacen kawaye daga su ne sai jasmine din...

jiki a sanyaye Ta kalle mumynta tace haba mumy ke a komi sai kin kwafsa min..yanxu meye na mata ihu da nuna kina zaginta da kin bari munbi abin nan a hankli Gashi toh kinata zargin ko suna tare amma ai ita bikin kawarta taje and she is even in her home right now gashi sectarinta tamin bayanin komi..

Da yanayin borin kunya hjya nadiya tace Aikin banza..ai tambayarta kawai nayi kinaji tana ja min tsaki hartana ban sako yen yen yen ban bata ajiyarsa ba toh uban wa zai bata ajiyar mijin ki dama mtsww yar iskan yarinya kawai..and i hope she is not coming back to ur house again.

Meenal tace "I dont think so..dama ai treatment din nasu a wann watan zai kare. Hala har sun gama harta tafi gidanta kenan.

"Good riddance to bad rubbish... hanklina ya kwanta yanxu, shikuma mijin naki ina ya shiga kenan?.

Da tsananin kishi aran Meenal tace bazai fa wuce Abuja ba..Taja tsaki wallh be isa ba
..mumy ki booking min flight idan naje abujan nakama shi red handed da budurwan tasa he wll have no choice but to play by my rules.

Hajya nadiya tace kina hauka ne. Play by ur rules ko kuma ya sakeki ya walakantaki kinsan yadda kudi ke haukata brain din maza kuwa?

Cikin katseta da ihu meenal tace mummy kawai ki kama min flight bani da lkcin jiran khaleel duk inda yake sainaje na tattaroshi yazo yabani kudi in yi abubuwan dake gabana..or will u prefer yaje yayta kashesu ma karuwai a abuja..u knw he sleep with girls in Abuja..wancan karon daya dawo wallh najijji shi yana wata da wata yarinya he must be der.

A hatsale hajya nadiya tace toh lefin uban waye ne..kina mace amma mijinki sai yay wata da watanni baiji duminki ba mezai hana shi bin yan matan abuja..mtsww
Ki zauna anan bari inje in ga me za'ayi..once the flight is ready i wll come back.. tana fadin hakan taja mayafinta ta fita waje tanata bambami.

Tsaki meenal din taja snn ta koma kan gadon ta kwanta da tsananin kishi aranta kawai dai ta aje cewa tunda basu tare da halisa to tabbasss yawon iskanci da bin mata kawai khaleel yaje.

Hajya nadia kuwa tana ficewa a asibitin ta nemi resturant da suke budewa sasaafe haka taci abinci ta koshi snn ta aiki delivery da take away na chips ykai asibiti ma meenal, daga nan kama hanyarta tay taje gidan wata kawarta ta share waje ta kwanta bacci dan tun shekarn jiya rabonta da samun bacci.

5.am Dot khaleel ya farka daga bacci da Adduar tashi bacin a bakinsa, bai damu ya kunna wayarsa ba dan yasan he wll be tempted to call halisa to hear her voice cike da Danne zuciyarsa ya share wayar ya wuce bathrum yay wanka snn yay alwala yay raka'atnl fajr raka'a biyu snn yay sallahn asbuhinsa a nitse ya sake komawa kan gadonsa ya kwanta a dukunkune kmr me jin sanyi tare da lumshe idonsa yay shiru million of things running tru his mind, he just cant afford to lose halisa, dan har ji yake dama bai aure Meenal din ba kwata kwata its seems like aurentan is bcming a curse to his life.

Yana kwance yana kan tunanin abunda ya faru jiyan har saida karfe shida da rabi yay, ajiyar zuciya me nauyi ya kufce masa ya jawo wayarsa dan yasan dolene halisa zata shiga wani hali in batajishi for this long ba

Baiso bude wayar ba amma wann tunanin kadai yasaka yafarajin kamr bazai iya hkuri baiji muryanta ba. Danna wayar yay ta kunnu kai tsaye har kirjinshi na bugawa cikin sauri sauri ya dudduba logs dinsa yaga call back mesges and calls attempts dinta
Cikin bude ido da lumshewa ya bude sakon data turamai da safen ya karanta ya kuma sake karantawa yakai sau biyar atake yaji ya kuma kara zaucewa da shaukin jin tsoro rasata kirjinshi na wani irin bugu yanajin kansa kamr a kulle cos How can she love him dis much and still ask him to wait bayan sun san wann lamarin cannot be undone yau ko auren meenal nakansa ko ya sake meenal it wll still feel the same to her.

Shide bazai iya kuma hakura da soyayyar halisa akanta ba dan a ganinsa what matters is what they feel for each oda and the blessings of their parents.

Yana cikin wnn tunanin yaji kmr ana buga mai kofa daga inda yake zaunen ya dauki wani abu ya danna kofar yay unlocking kansa maryam tabude ahankli snn ta shigo ciki bakinta dauke da sallama muryansa kasa kasa ya amsata har gabansa ta taho tazauna agefensa ganinsa rike da wayarsa a hannu tariga tasan meyake tunani..

suna gaisawa ya kalleta snn yace mata mimi jiya da yaushe kuka dawo?

tana kallon yanayinsan tace late at night..nazo na samu kana bacci.

Yadan yi shiru kadan
Ahnkli snn yace how was she..? cikin sauke ajiyan zuciya maryam tace i can't tell..Atake ya kalleta yace why, maryam,.. this is not the time for games inason nasan halin da take ciki.

Ta harareshi tace Aida kanason sani da baka kashe wayarka ba.. have u receive her tex this morning?

Yace yeah Tacemin she left...inafatan ba fushi tay ba kuma.

tace ohh bansani ba, dama cewa tayi nazo na duba mata kai.

A Bazata wata ajiyat zuciya ta kufce masa Muryansa kasa kasa yace toh meyasa batazo ta dubanin da kanta ba zata aikoki.

Maryam tace maybe she is scared by the u way u left and off ur phone..

Yace Kema kinsan ba fushi nakeyi da ita ba..i just don't get it..mryam babu abunda halisa bata sani ba, this problms cannot be undone. So why wunt we jus go tru it.

Cikin katseshi maryam tace Khaleel is not easy for Her..u shud have seen how worried she was daka bar wajen, pls ka sassauta mata dan Allah give her some space to be at peace with..

Kamar zaiyi kuka yace ma maryam "no..i cannot give her any space mimi u have no idea how scared i am right now wallh inajin tsoron na rasata bazan iya daujar hakan ba na riga na sakata araina. maryam bakisan yawan taurin kan halisa bane. Idan na yi shiru na nuna na fahince ta karshe dolene zata takura akan muyi haqri da juna kuma wllh bazan iya ba. atleast, Not for the sake of Amina talba akan me?? inhar na rasa halisa toh bazan fa iya zama inuwa daya da Amina ba.

Hannunsa ta kama cikin nata cikin sanyin murya snn tace pls control ur self khaleel..komi zai zo ya wuce inada yaqinin yadda kakejin bazaka iya ba haka itama takeji aranta, i knw she loves u dearly..nide abunda na lura shine tana bukarta lkci ne da zata digesting din abun..khaleel did u think is easy for her to live with that pain of breaking her..friends home?..

yace Maryam dan Allah kudena gaya mata haka for god sake, she is not breaking any ones home, Aminan nan itace ta ganni tace tanasona bani nace inasonta ba bare ace yaudararta nayi,.. kuma kema kinsan yadda akay na aureta,.. haba da Allah maryam shikenan ni bazan yi rayuwata da wadda nake so ba sabida ita, halisa is just giving baseless excuses ai ba ciki daya suka fito ba, and she knws how much i care for this to work out kawai so take taga nashiga damuwa..ita Aminan In halisan Allah ya rubuta min zan aura arayuwata ita kuma ta mutu tabarmu tare me zatayi akai??mtsw..

Dafashi Maryam tay tace toh yanxu dai ka kwantar da hanklinka kaji, and dont say dos words again. Which is zaka aure wata, wata kuma ta mutu.. duk wann abu yar hakuri ce, nide abunda nake so dakain shine karkaji fushi da halisa dan bata amince akan lkci ba, she have all the right to think dis tru..and isnt it enuf to knw she loves u back?..haba khaleel. pls inka huce ka kirata awaya ka dan lallesheta baka ga yadda kawayenta duk suke bin bayanka ba, i am not sure she slept yestanyt.. kuma muna komawa gida try and see her and make sure u let her knw u can wait for her..

jin hakan yasaka yadanji sanyi aransa ahnkli Yace tou "Naji. daga nan ya mike tsaye yana kallonta fuskansa ba asake sosai ba.

tace yo meye kuma na hararata danma kasamu na tsaya na rarrasheka?

aranshi Yace toh ai aikin kine dama..
Chapter 223 · 0% Book details