← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 301 OF 312

Sashe 301

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

This is sumtin she can
Neva tolerate Allah ya kiyaye mata zama da dangin miji kaf a mtsyin munafakai mayu maroka take kallonsu..

sai can Wajajen sallahn magbr snn suka watse Aliyu ya bi yayansa sukaje masallaci ita kuma halisa a kofar gida kawai taraka sauran bakin ta dawo dakinta tay alwala ta shimfida sallahya ta gabatar da sallahn magrib..

bata tashi awajen ba Ta dau qur'ani ta na duba abinda khaleel yake koya mata every morning har aka kira isha'i ta mike tsaye ta gabatar dashi a nitse shima..

Ta yi sallama kenan taji an turo kofar ahankli tana daga kai taga meenal da wani irin mamaki meenal din take kallonta kafin nan ta sake kofar da sauri jikinta harna rawa ta karaso...halisa lallai kin cika babban makira munafuka..hmmm na sara maki...wai dama dagaske kike kin musulunta??? Yanxu tsabar son ki makalkale min mijina ki rabani dashi shine har canza addininki saida kikayi ke wata irin mayaudariyace haka.

A kasale halisa tay murmushi tace thats is a very good way to express ur shock Amina. Koma me zakice ki fada i dont owe u any explanations.

Tana maganan meenal na kallonta da dumbin mamaki harta cire hijabinta ta linke ta nade sallayar ta aje ta daga qur'ninta ta ajeshi kan gadonta ta nufa meenal nakan binta da kallo me cike da baqar kishi dan wata shegiyar abayace me tsada ajikinta purple colour tana zama abakin gadon ta kalle meenal din snn tace Waime ya kawoki dakina ne ko kinxo neman mijinkin ne?

Nannauyar ajiyar zucya ya kwace ma meenal dan har yanxu mamakin ganin halisa tay sallan bai saketa ba...muryanta wani iri iri tace "kinsan ni ba muguwa bace kamr ki nazo ne inga ko kin samu sauki dazu naga kinata suma haqqi na yafara binki muguwa ...

Dariya halisa tay tace thanks jikina da sauki..

...waje ta nema ta xauna abakin gadon halisan snn tace "wai ciki kike dashi???

Halisa tay shiru sai kuma tay murmushi tace Eh.. haka champ ya gaya min..we are going to be parents soon.

take fuskar Meenal yay jaaa da mugun kulli aranta tace hmmmm
Okay.. kin masa magana na ko dama makirci da karyankine??

kai tsaye Halisa tace ive talked to him, amma yace zaiyi tunani akai

Tsaki meenal taja snn ta mike tsaye tana cewa dama abunda ya kawoni kenan inkin ga dama karki warke kimutu ahaka
Znga kuma dan uban da zaki haifa agidan nan wallh baki isa ba..

Dariya kawai Halisay batace mata komi ba harta fice tanajin haushin dariyan halisan aranta bana wasa ba...

Koda taje room dinta kasa zama tay tayi nan tay nan tanata tunanin yadda zatayi itama

washe gari sassafe ta fito ta jira har saida halisa ta fito snn ta tsareta da magana,duk dama ba me dadi take gaya ma halisa ba amma sosai halisan ta bata shawarar akan ta sauya takunta intanason kan mijinta sabida apart frm mugayen abubuwan da meenal tamata wann soyayyar datake ma khaleel din shikadai ne yakesata taji tausayinta aranta duk dama bata fiye nuna mata a fili ba.

Bayan nan Meenal tafara tunanin bin salon halisan koda itama zaa kulata saidai itafa tafison abunda zai mata aiki ne cikin agaggawa, yau kwananta biyu kacal da sanin cewa halisa na da cikin amma tabi ta dora abun aranta cewa itama lallai sai tay wnan cikin sabida khaleel ya juyo da kulawarsa da hanklinsa kanta babban burinta shine ta kore halisa agidan ta mamaye dukiyar mijinta itama taji irin dadin da halisa take ciki yanxu..

Tanason taga sun gwabza akan miji da halisa amma Gashi babu sauran lokci, sati biyu ya tafi already acikin wata gudan da kotu ta basu dan haka she have to take all risk to see her dreams comes tru.

a kwana na ukun Sassaafe ta saka likitarta
tamata gwaje gwaje ta bata maganin da zai dakatar da drug din datasha dan ya katse mata yin period da kuma haihuwa tun da jimawa

ranar da likitan ta bata maganin tasha ko aiki baiyi ba saida aka sake mata allurai snn jini ya barke mata tayta fama da azaban ciwon ciki, kafa, baya, ranar tasha azaban bana wasa ba.

Ana washe garin ranan da khaleel zaiyi deciding yafara zuwa dubata din kamar yadda halisa ta bukaceshi meenal tafara shirin daukar cikinshi saidai Haryanxu jinin da suka ballo yaki tsayawa

Shikuwa koda yazo ya samu halinda take ciki dama baizo da noyyar tabata ba Haka yace lallai saidai a dangana akaita babban asibiti aka fara duba lamarinta..

Ranan bakaramin baqin ciki da haushin hakan taji kawai ta lura dashi neman duk wata hanya yake da bazai hada gado da ita ba..

Atakaice saida tay kwana hudu masu kyau a asibiti akwance tana xubda jini
Ganin abu yaki ci yaki karewa ga lkci ma tafiya tafara ta fara daagawa hajya nadiya hankli akan lallai itadai sai taimaka mata an tsayar da jini dan ta dau cikin khaleel din itama.

Da wuya da wahala Da Taimakon Alfah jinin ya tsaya a akwana na biyar ranar ranar tace ma likita sam akaita gida wajen mijinta ai yau kwanta ne bana halisa ba..

Now dat she have just 12 days with them tanajin kamar bazata iya lalata koda awa guda na rayuwanta wajen sanya akan khaleel ba..

Tunda har halisa tay cikinsa a sati biyu itama tanason within this days taga cikinnan ya shigeta
Kota halin kaka ne

And her medical reports is showing red ga chronic depression ga mugayen ciwukan infection na mahaifa ko binta kan bayanan likitan batay ba tunda alfah ya dakatar da jinin taji karfin gwiwa...

yau tunda suka dawo gidan da likitarta babu wanda yaji sarari miji nata ne a abatajin dadin wai itama sai tay masa girki irinna halisa kiris ya rage gobara ya kama gidan khaleel Allah yaso megadi yana nan shine Ya taimaka ya kashe mata gas akan lokci.

Duk ranta a dagule bata iya komi ba gashi Aliyu ya dauke halisa sunje cikin family house ziyara dan harga Allah bata iya boye kishinta itama wata rana.

Meenal ce kawai take zagaye ita kadai dan abunda ta caccagabar sunyi baki kiri sun kone murus haka ta zuba su a kondon shara.

duk wann be dameta tundaga lagos tasaka mummynta aiko mata sexy nity Tana Allah Allah
dare yay khaleel ya shigo

Bai kuwa tashi shigowar ba sai can wajajen sha daya na dare fuskansa ma ba asake ba yazo ya samu tajirasa tagaji har bacci ya fara daukarta

Abakim gadon ya zauna yagama chat da halisa kenan zai kwanta taji motsinsa daga cikin baccin ta farka a firgit.

Firigtan datay yasa taji mararta ya wani murdata ihun bazata tay saida ya juyo yaganta harta zabura ta mike tsaye a take sai kuma taji dumi me mugun yawa na sauko mata kasarta kafin kace wani abu jini guda guda sun tuttulu sunabin kafarta yarrrrrrr sunbi sun wanke kafafunta ixuwa kasa suna sauka dan ko pants bata saka yau ba ta shanya gindi tana jiran miji yaxo..

kusan rudewa tay dataga jinin na sauka dan a take jikinta yahau karkarwa tafara cewa na shiga uku
Wayyo Allah na karkamin haka mana...na shiga uku na..

Da mugun sauro khaleel ya dira akan gadon bakinsa yanamai furta innalillahi wa inna ilaihi rajiun...

Rushewa tay da kuka ta tsuguna akasa tafara zage zage tana cewa ta shiga uku.

Bai tabata ya kama hanya yafita after a while sai gasu nan sun dawo tare da halisa suka dau wayar meenal din suna kkrin kira mata likitar gwamntin da aka hadosu da ita.

Meenal kuwa tana ganin halisan tafara ihu tana cewa muguwa azzluma algunguma burinki ya cika kin min asiri dan kar mijina ya kwana dani Allah saiya tsine maki halisa ta dinga ihu tana tsine mata..

halisa tay tay da Khaleel ya taimaka yaki sam karshe ma ya barsu a dakin yaje cikin motarsa yashiga ya kwanta abunsa yay banza da su.

Halisa ne tsaye akanta dik uwan ruwan boma boman zagi da sharrin duniyan saida ta mata amma bata damu ba tana tsaye tare da ita har aliyu ya taho da likitan acikin dare aka hau dubata.

She is having a severe uterine infetion side effect na maganin tsaida menstural flow dinta datay tun tana yar shekara sha takwas da zimman cewa ita bazata sha wahala ba, she is boss lady, equal to men,
Shiyasa bazata juri yin al'ada yana katse mata harkokin gabanta ba.

Yau taji babu dadi sosai aranta komi ma ya fara bata haushi tana jin kamar ta musu hauka, dantagama saka rai tay lissafin cikin kwana goma zata dau cikin khaleel ko ana so ko ba aso.

Tunda tafara lamarin zubar jinin nan gidan ya zama ba azaman lafya dan akoyaushe tana cikin tada rikicin cewa halisa ce ta mata asiri dan kar miijnta ya kusanceta.

Khaleel harya yafarajin kamar hakurinsa zai kare akwanakin musammn data fara tarar halisa da mortal combat da dambe, dan tausaya mata da halisan takeyi duk saida tazo ta kwabar dashi sabida she was soo desparate itadai saita sami cikinshi kota halin kaka ne ..

Ana saura sati guda akoma kotu gidan ya dawo kamar wanda ake zamn doya da manja.

Meenal ta sakasu agaba da da fitina da sharri at same time tace ma mummynta lallai kawai ta Amince ta kwana da alfah on her behalf domin ama khaleel wata muguwar asirin mallaka ita tagaji da hakuri kawai gara ta masa asiri me kankat ta mallakeshhi

ganin meenal ta daga hanklinta sosai yasaka hjya nadiya ta aikata hakan snn Alfah ya bata asirin wani abune kamar ruwa akwalba aka bata akan tazo dashi, ya musu list da wasu abubuwa harda buran kare, da jinin al'ada, da danyen placenta aciki yace musu sun tabbata sun nemo wayann abubuwan suyi stew dashi kuma meenal din ce zatay girki tazuba ma khaleel tare da ruwan kwalban abincinsa yaci abincin akalla sau uku sai shikenan bazai sake tuna wata halisa ba sai meenal har mutuwarsa kuwa.
Chapter 301 · 0% Book details