← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 312

Sashe 112

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Vicky na isa Master bed room dinta aka biyota da tarkacen abubuwan da zata bukata na gudanar da aikin kamfani, Files,
da gadgets kamr su macbook, laptops da sauransu. Wani irin karramawa na musmmn ake mata tamkar matar sarki, duk da ma bata saka komi aranta ba duk a tunanin ta kodan an bata shugabancin wajen ne yasaka kominta ya zamo na alfarma..

Duk wann bashine agabanta ba babban burinta shine tay ido biyu da wanda take chating dashi, ayayin da take hutawar ne ta kira hadiza maitama suka sha hira hadizar ke dada gaya mata tay hankli sbida kala kalan mutanen da zasu halarci taron duk rivals dinta ne kuma babbn burinsu shine su shafe kamfaninta acikin manya ya zamto su kadai ake harkan dasu.

Dagata dayan bangaren kuwa kayden na kwance kan makaken gadon sa na cikakken dan gata agidansu dake banana island na lagos, daga shi sai white throbe na hutu, yau baije schl ba, almost evry now and then ya kan kira james daga kano domin ya tambayeshi lafyar vicky, bai nitsa ba sanda ya tabbata ya sanar musu cewa baison kowa yasan kamaninsa bare asan cewa shine me kamfanin and he made it clear to most expecially vicky. su duk sun dauka gwadata kawai yakeyi akan dukiyarsa daya dorata akai.

awajensa kuma hakan ba gwaji bane face wani babban hanya data budu masa na samun daman dada janye tunaninta akan mijinta femi gabaki daya. Saida vicky ta samu isashen hutu kafin Program din ya fara da opening dinner na dare.

simple black flowinv gown ta saka for the dinner event bata tsaurarawa a komi ba.

Anan ne ta hadu da few of her business rivals mrs toyin,mrs karimat da babban cikinsu very stern and greedy igbo lady wato mrs chimamanda da bata iso Kanon ba tukuna.

Ganin vicky wajen ya basu mamaki sede ko kulata basuyi ba a tunaninsu kawai batawa kanta lokci takeyi anan din babu abunda zata samu cikin harkan da suka sako agaba sanin cewa kamfaninta yaja baya..

Wajen dinner din banda gulmanta babu abunda sukeyi suna yi suna kuma jefa mata habaici musmm akan business dinta daya koma baya.

Aganinsu ko su din da suke fafutukar tashi tsaye bazasuyi risking jawota cikin business dinsu Ba bare kuma babban kamfanin na elmario da suke masa kallon babban Tudun sa'a kuma mabudin hanyar yin suna da arziki.

abubuwan da suke gaya mata masu cin rai amma hakanan ta daure ta nuna bata damu ba, kuma bata bayyana musu sabuwar matsayinta wajen ba, aranta jira take sai gobe in anzo hidima lokcin kowaccensu tana nan kafin gani zai kore ji...
********

ata fannin su halisa sai can Da yamma lis bayan sun gama yawonsu na shakatawa sun ci abinci sun dawo kafin nan jasmine take gayawa halisar cewa zata bi jirgin sassafe ta koma london dama dan ta duba jikin tan kawai tazo.

Halisa bata ji dadi ba at same time kuma taji dadi sabida Tasan bakowane abokiya bace zata iya secrificing kudinta da lokacinta domin ta taho daga wani duniyar dan tazo ta dubata.

abataso ba haka ta raka jasmine har gidanta suka suka sha hira kadan jasmine tanamai dada nutsar da ita akan abubuwanda suka tattauna dazu dik dama ta lura halisa nada taurin kai akan lamarin khaleel duk da haka she make sure to make her understand that bazata ci nasara akan jinyarta ba har sai ta bude ido akan makircin meenal snn tayi hakuri dashi..

10;30 pm na dare suka rabu da jasmine bayan sunyi sallama ta dawo gidan duk ta gaji, ahnkli ta bude kofar falo sanyi Ac me gauraye dana qamshin turarensa ta faracin karo dashi, koina yay shiru wanda inba ka lura ba bazaka ce da mutume rai zaune aciki ba, nan tasameshi a falonsa yana zaune jikin shi sanye da wata white armles shirt da blue colour thr qrtr ya nade kafafunsa innocently

Idanunta daga can masu kama dana mejin bacci ta darsa akansa lkcin hanklinsa rabi da rabi nakan system yana aiki akan project dinsa wani bangaren kuma tunanin sa dika nagakan abubuwan da yaci nasaran samun su a yaune game da ita.

Tun da sukayi magana da gracy bai samu wani cikakken sukuni aransa ba. Duk Ya rasa me zaiyi, dan juyi yay kadan sai halisan ta fado masa cikin ransa ayanayi me kashe masa gabobin jiki.

he is not sure how to contain the feeling dan akaro na goma sha babu adadi kenan yanamai sauke ajiyan zuciya me nauyi hade da karsashi, dan Kusan dk wani abunda ya shige masa duhu akanta They all came in to him at once yau a sigar da bai taba tsammani ba.

tana shigowa suka hade idanun su waje guda, yadda tay saurin dauke nata anashi da dauraren fuska yasaka wata sihirtacryar ajiyan zuciya ya kufce masa..

Wasu abubuwa masu rikita tunani ta dingaji aranta datake kallon kyaywar fusknsa jin tana bukatar duk wani hanya da kuma dalili da zai saka ta dandana masa irin zafin daya dandana mata aranta ata inda zai fahimce rayuwa.

Gabobin jikinta har wani mutuwa sukeyi ayayinda haske da kuma kyan fuskansan yake piercing cikin kwayar idanunta yanamai aika mata sakonni tare da sakar mata kasala da sacewar jiki daga tsaye.

He can't be this cute and dump at same time, hade rai tay za ta wuce shi batare datace masa komi ba harsanda tay dan nisa snn ya dago idanunsa yabi bayanta da mayun idanunshi da suke haskawa ta cikin farar gilashin dake sakale akan idanunsa yana sauke ajiyan zuciya.

irin kallon Kurilla dayabi bayanta mata har Ji tay gabanta na mugun faduwa, take jiyo muryansa cikin sanyin dakewa yace "Halisa"
..batare da ta juyo ba cikin lumshe ido da budewa tace 'what?

Ya kyabe baki, kamar zai ce wani abu sai kuma ya girgiza kai yace 6.am sharp pls. Ahnkli ya fada

itama ahnkiln tace "Anything else?

Ya jinjin akai snn Yace uhum, dan shiru ne ya ratsa wajen tana jiranshi ya furta abunda yake son furtawa amma sai shiru.

Kallonta yake koda zata dan juyo ta kalleshi ita kuma kallon nasa ne bataso, bayan ta bashi while She waited to hear him speak harsaida ta hakura dajuya mai bayan ta juyo zata kallesa sai ta ga shidin ma ita yake kan kallo..

Kusan atare suka sauke wata sihirtacciyar ajiyan zuciya cikin bude ido da lumshewa tace "I am listening. Har cikin kwayar idonta yake kalla
Da muryansa me taushi cikin kyabe baki yace gud nite...

Tay saurin kwace idonta anashi batace mai uffan ba ta juya ta haura sama tana tafiya ahankli.

mamakin ganin kalar sauyi tare da tsananin shaukin tausayinta datake kallo acikin kwayar idonsa da bata kammala fahimtarsu ba takeji har ta isa cikin dakin. Bude kofar tay ahnkli tana shiga ta fada akan gadonta tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya..ta jima a kwance batare ta kawo tunanin komi ba jim kadan ta muke tay wanka ta fito

Yaudin Kamar yadda bai same nitsuwa aransa cikin daren ba itama kusan hakan ne ata fannin ta, dan kusan kwana sukayi cikin juyi da tunanin juna, sama sama baccin yake daukar ta. sai Wajen karfe biyu na dare kafin ya dauketa me gabaki daya.

Tana rufe idanunta bata jima ba taga kanta da bakaken kaya a wani babban makabarta tana durgushe mutane dayawa sun zagayesu tare da mamanta da babanta sun rike hannu suna mata murmushi ita kuma na durkushe agaban wani kabari tana zuba kasa aciki tana binnewa cikin baqin ciki da kuka.

5:am Dot ta farka a mugun razane tana haki sanadiyar wannnn mummunan mafarki datayi wanda ta rasa dalilinsa, tafi minti biyar zaune akan gadon bata iya motsawa ba, Addua tay ma iyayenta, da tunanin ko itace zata mutu tabiyosu suke nuna mata alaman hakan a mafarki, har sai can da tsoron data kwaso a mafarkin ya saketa snn ta sauko kasa ta fada bathrum tay wanka sama sama ta dawo cikin room din sanye da kakkaurar bathrobe duk da haka taji kmr tana barin sanyi kai tsaye ta rage gudun Ac snn ta zaune tsantsane sumanta ta fara bushar dashi ta shafa masa mayukan gyaran kai ta kamashi in a messy bun dede inda face cap dinta zai zauna.

bayan lotion data shafa ma fatar jikinta bata kara komi ba sai body mist da musk oils masu qamshin lavender notes da african oranges which make her to be smelling as fresh as clean air. Banda oil din hana fuska tsufa data mutsika bata shafa komi ba tabar fuskarta ahaka a natural dinshi.

pants kawai ta saka snn ta jawo bakin wandon sport na kamfanin jordan me stripes din Red colour ajiki da rigarsa me kamar t shirt amma sakakke bai mata yawa ba kuma be kamata ba ko breziya bata saka ba ta zurashi

5;45 ta fita taje kitchen tay makanta green tea ta dawo room dinta dashi tanasha tana tura text wanda zata kirasu duk ta kira sun magantu dan yau batason ma taje ko ina da wayarta bare ya zamo mata silar wani hatsaniya tsakaninta da khaleel..

Ta fannin khaleel yana farkawa masallaci ya nufa har saida yay sallah ya dan Zauna yay bitan karatun qur'ani sama sama daga masjid din ya dawo gida ya hau shirya kansa shima, yau all black ya saka ajikinshi bai mixer da wata kala ba ya dauki phone dinsa 5 min to 6 ya taho kofar dakintan ya tsaya tare da kwankwasawa after a while ta fito ta same shi atsaye suka kalle junan su kowa nashan qamshi kusan yauma basucewa junansu uffan ba har suka kama hanyar field diin atarre.

suna isa babu bata lokci suka fara, tasha mamki yadda taga yau yanayi dgske bakamar can baya ba,Babu yanayin fushi ko murmushi ,but he seem to be intrestd now, Bai barta ta huta ba yana ta sakata tana motsawar dayasan zasu saka ta zamo strong and confident woman in the face of adversities.
Chapter 112 · 0% Book details