← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 312

Sashe 102

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan Gayen ya fito da wata takarda ya bata yanata mata bayani akai ita kuma tana dubawa
yana tsaye agefenta harta kammala dubawa duka sann ta amshi bironsa ta sakamai hannu akai ta bashi.

Bayan nan ya ciro waya daga aljihunsa yay dialing ya mika mata ta amshi wayar tare da umartansa ya dan bata waje tana murmushi ta kara wayar a kunne

Cikin bude ido da lumshewa khaleel ya ciza labbansa cikin tsananin jin takaici cikin ransa yana cewa this girl is such a bitch...100% duk ya dauka ko da zach din take magana, "waime mata suka dauki kansu ne sabida kudi da son duniya halisa ta kasa rabuwa da mutumin daya tozartata ya walaknta ya kusa yajefata ga halin rasa rayuwarta me gabaki daya...kafin ya bude lumsashun idanunsa har sunyi jaaa jazur zuciyarsa datake harbawa bakaramin zafi take masa ba.

Gabaki daya maganganun meenal saiya soma dawowa kansa, kenan gaskiyar meenal ce halisa bazata iya rabuwa da zach ba dan aganinsa duk me irin wann maitar son duniyan dolene ya zamo yana hadawa da harkan maza.

hakanan ya dinga reflecting akan rayuwarta na baya kishi ya rufe masa ido shaidan ya shiga ingizashi sosai.

to wayasani ma hala sabida tsabar son tay duniyancin yasaka tabar gaban kawunta tafada aikin kazanta da akace tay a club na goge goge dantana biyar makanta kudin makaranta.

Ata bangaren halisan kuwa tana rike da wayar a kunnenta tana shako muryan mahaifyar fadila kusan kiris ne ya rage hawayene bai sauko a cikin idanunta ba dan ta mugun jimawa bata ji ana saka mata albarka kai tsaye kamar nayau ba

tun da suka fara wayan matar tanata kuka tana mata godiya like her life depend on it, domin kuwa agent dinta data tura wajensun har sunje an dedeta da yarta fadila Sun yafe juna an kuma dauko su izuwa birnin lagos an siya musu isashen gida a wani sabuwar anguwa ita da sauran kannen fadilan snn an bata kayan yin sana'a kamarsu engine markade, keken dinki, da tsabar kudi milliyan biyu da zasu ja jari. Duk wann acikin kyautatawa kawai halisan ta musu badan komi ba.

fadila tarasa na cewa saidai aranta ta quduri niyyar sakawa halisa da alheri ta hanyar rike mata dukiyarta da gaskiya tare da amana.

Rana guda komi ya sauya mata, dan da s sukaje kauyensun ta samu wahala ya ladabtar da mahaifyartan sosai nemanta ma takeyii ruwa ajallo.

Duk wani labarin cin mutuncin da hajya nadiya ta musu saida ta bawa yarta labari dan har gidansu na kauyen saida hajy nadiyan ta siyar wai ta fanshe kudinta data kashewa fadila tayi makaranta. Yunwa da baqar azaba yasaka ta tura kannen fadilan almajiranci ita kuma suna kwana da kananan cikinsu a zaurukan mutane bama ajega maganan abincin da zasu saka abkinsu ba

taimakon da halisa ta musu sai ya zamto musu
kamar wani babbaan rahaman Allah ga rayuwarsu..

Yau datay magana da halisan sai taji hanklinta ya dada kwanciya sosai duba da cewa ita me kudice amma bata da nuna musu girman kai da cin mutunci kamar meenal Da kyamarsu ma takeji sosai.

Halisa ta dada kwantar mata da hankli da cewa yarta zata na zuwa akai akai tana dubasu amma yanxu haka zata koma spain ne da zama me gabaki daya.

Ata fannin fadilar tay alkwarin zatana turo musu kudin makarnta dana abinci kowane wata

harta kammala wayar ta share hawayenta tareda mikawa shuaib wayarsa khaleel bai gane komi daya faru awajen ba.

bayan sun tattauna lkcin tafiyarsun nan sukayi Sallama da shuaib ta koma cikin gidan abunta .

Khaleel na tsaye har shuaib ya wuce kafin nan shima ya shigo cikin gida....

Bayan kamar wasu awanni lokcin ana neman karfe 10:30 uztaz ya taho gidan kai tsaye yaje har dakin khaleel ya kwankwasa masa kofa after some min ya bashi izinin shigowa ciki.

da sallama abakinsa ya shigo qamshin turaren jikinshi gauraye dana dakin shiya fara tarbansa

A Zaune ya hangosa akan couch sanye da bakin wandon jean da jan shirt na marks and spencer ya dora system dinsa akan cinyarshi cikin nitsuwa yana latsa kan computer yanamai designing building blocks na project dinsa yana turawa wa ogansa daya bayan daya..

Sai har Idan ogansa yay reviewing report din kafin sai yay aproaving masa wanda babu kuskure aciki snn ya tura can website din larabawan kai tsaye.

Uztaz na shigowa ya dago kai yana murmushi snn ya mikamai hannu sukayi musabaha da sakin fuska suka gaisa

uztaz yace masa yazo yay masa sallama ne yau zai tafiya kuma bazai dawo nan kusa ba, in akwai wani abu da zai yi masa yanason yasani kafin su wuce airpot da team dinsa..

Khaleel ya boye mamakinsa cikin murmushi cos he is alwys amazed da yadda uztaz ya zamto soo loyal with halisa's health and business. Tabbas samun makusanci irinsa zaiyi wuya.

Double smirks ya kufce masa ya zaro wata paper ya mika masa yace masa iya routine din da zasuyi kenan ya duba ya gani snn ya tabbata ya bata a hannunta shine zai gaya mata lokocin dakansa

Uztaz ya daga ya karanta
Duka snn yace ba matsala zan tabbata na mata ahaka sukayi sallama snn ya fice ya dawo ya samu halisan harta fice a motarta tay gaba dan tatsani neman permission din da akeyi na khaleel duk sanda zata fita wani waje.

A airpot yaje ya samesu da fadila suna zaune, fadilan ta dan kwanto ajikinta tay kuka harta gaji ta rungumeta sosai cikin nuna mata tsantsan godiyarta musmn data damka mata wann aikin a hannunta. Da ita da shuiab da monica zasu wuce spain atare. Uztaz shikuma yana da team dinsa daban..

zuwan uztaz wajen ne yasaka su fadilan sukayi sallama dasu duka suka bar wajen izuwa inda jirginsu zai tashi....

Dat feeling of going into a new life shine ya mamaye kirjin fadila tun acikin jirgi awani bangaren zuciyatta kuwa taci alwashin amfani da wann matsayin nata domin ta koyawa meenal talba hankali a duniyan nan. Wann boyayyan qudiri ne wanda ta kullata aranta wanda daga ita sai Allahnta suka sandashi.

Sai karfe 12 na rana jirgin su uztaz zai tashi sunfi minti arbain suna zaune da halisa duk bata jin dadi data kasance ita kadai ynxu, uztaz yanata mata bayani akan wasu abubuwan da zata bukata idan baya kusa.

He is going to spend like 3 months or so sabida abubuwan da zasuyin suna da yawa,da niyyar zaina lekowa nigeria bayan sati bibbiyu dan yana leko famlynsa da ita.

Yanata bayaninsa baisan ita harta riga ta yanke masa hukunci aranta ba cos she feel quilty sumtimes sabida yawancin lkcinsa akanta kawai yake karewa ba akan familynsa ba.

Wann tafiyar itace yakamata ace tayishi Inhar ta barshi ya tafi tamkar hakkin iyalinsa ta shiga hakan yasaka ta yanke shawarar turasa chan din tare da matarsa dansu kasance tare basai ya dawo nigeria akai akai dan ita ba.

Uztaz baisanda wann shawarar ba sai har daf ana shirin jirginsu zai tashi kafin ta gaya masa
snn tace masa kar yace komi tanaso tayi kkri tayi abubuwa dakanta shima yay kkri ya ja mataarsa ajikinshi sosai in sunje can.

Baisan hakan zai faranta masa rai sosai ba saida yaga dayan drivern su ya kawo matar tasa airpot
Godiya sukayi mata cikin girmamawa kafin nan sukayi sallama da juna 12.30 on the dot suka bar kasa.

Ya rage daga ita sai halinta, she drove her self home cikin motarta dayasha bakar tinted tana tukin ahankli tana shan tabarta tana tunanin yadda zamanta da su khaleel zai kaya agidan, tun anan ta dinga bawa zuciyarta hakuri harta iso gida.

Tun data dawo takejin gidan shiru sai juyi take akan gadonta tasha taba harta gaji ta fito taje kitchen dinsu ta dafa sardine noodles taci tay bacci ba ita da fakawa ba har sai wajajen magrib.

ahakan ma Meenal me tazo ta tadata da zancen tafiyar da zatay jibi
Tanata murna wai carlos yace musu suzo south africa su sameshi suyi first meeting da training dinsu acan. Taki sam ta fayyace ma halisa harkan sabida tanada baqinciki sam batason ace halisa ma ta shiga

She just cant wait to be der duk jikinta na rawa rawa.

...hakanan ta jawo halisa na dole sukaje room dinta danta tayata zaban kayan sawar da zatay tafiyar dashi.

After a while halisa ta dawo room dinta tana waya dasu uztaz Tana cin abincinta wanda megadin gidan ne yaje yasiyo mata, calmy take taunawa dik tafara gundura da cin abincin waje gashi haryanzu bata wani sake da zancen yin girki agidan ba.

Around 9 khaleel ya leka computersa yaganta tanacin abinci tanakan wayarta at same time, shikuwa inya ganta tana waya zach ne kawai ke zuwa masa, ahankli ya dauke kansa ya cigaba da aikinsa da zimman inta gama zai je dakin dakansa ya gaya mata lokcin da zasuna fita cognitive exercise dinta
da zasuyi nayi tare harna tsawon sati daya.

Tunanin yadda abun zai kasance masa gobe ya shagaltar dashi cos he no longer have time to tolerate her gara kawai ya fidda abunda ke ransa agoben inyaso koma me zai faru ya faru..

Time time yana daga kai yana duban screen ko ta gama wayar amma baiga ta gama ba. Kuma dik sanda yaganta ahaka sai yaji haushi.

Sosai ya tsara abunda zai furta mata sai can wajajen 12.00 na dare ya farga ya daga kai ya sake duban computern sai yaganta har yanzu tana kan waya tare da shan tabarta dakin duk ya bule da hayaki..

Takaici ya cikashi ya rasa wani irin waya takeyi haka kwana biyun nan kusan kullum kullum kuma me tsayi har acikin dare???

Ya kasa jumrewa haka nan ya fito da routine din ahannunsa direct ya iso kofar dakin ya hau kwankwasawa, sharewa tay dake duk ta dauka meenal ne ta dawo sai taki budewa akan lokci saida yaci kamar minti sha biyar a tsaye snn ta hakura da bude kofar.

tana budewa Suka hade ido irin kallon daya mata yasaka gabanta mummunan faduwa.

Yayi tsamamninn zata dan katse wayar ta bashi attention dinta ta saurareshi amma sai kuma batay hakan ba..

A mind dinta cewa take meye zai wani zo kofar dakinta yana hura mata hanci kamar ya haifeta..
Chapter 102 · 0% Book details