← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 312

Sashe 120

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kullum in zatai mata wa'azi saita kawo mata zancen meenal Talba acewarta it will be human of her to be herself around him koba dan komi ba saidan zaman tare, takance mata kar tabari makarcin meenal yay tasiri akanta ita kuma halisa rainin wayonsa kawai takejiye makanta tsoro.

Duk zamansu agidan yaki sam ya sanar da ita me ake ciki da batun case din kawunta bare kuma mama g..

Sau daya grace ta kirata awaya da lambarsu ta foundation tagaya mata cewa ana kulawa da ita sosai harma za'a kaita india for cancer theraphy formalities din kawai ake shiryawa.

bakaramin dadi halisa taji ba, kudi me dan yawa tasaka uztaz ya tura a acct din foundation din mahaifyar khaleel din a matsayin contribution nata. Snn ta aika ma grace kudaden kashewa..

Acikin satin banda hidimar thanks giving din vicky da akayishi acikin gidanta with few friends and family halisa bataje koina ba, ahakan ma khaleel din bai kyaleta taje wajen ita daya ba tare sukaje ya jirata awajen har aka gama hidimar suka dawo hakan yasaka bata samu ta jima sosai awajen hidiman vickyn ba.

banda Asad babu wanda ya taba zuwa gidansun, shima dayazo duk tana lura dashi taga yauma basuyoli wani hiran mutunci da khaleel dinba dake har yau yana kawo masa zancen babansa da kwata kwata baison ji.

wayo tay ma Asad din taji labarin halinda Kawunta yake ciki abakinsa, abun sai yadan fara damunta aranta dik da tasan dai zamansa acan a kulle abune me kyau amma toh meyene duniyar, yau kaine gobe ba kai bane, gani take Duk babu amfani, cos at the end der is no amount of purnishment da za'a ma kawuntan da zai kawo ma zuciyarta sauki ko wani salama musmmn ma akan abubuwan da yamata na tozarci da walakanci a rayuwa.

Tanason tay ma khaleel magana akai amma ina duk mood dinsa ya baci akan zancen sa da Asad akan babansa, shide baison ana takura masa akan cewa lallai sai shine zai rusuna kansa kafin su shirya, dan gani yake kamr baban nashi yafi cutar dashi sosai kuma dadin karawar abun haushin da haryau treating dinsa yake kamar baisan abunda ya masa yayi masa zafi ba. His dad care very less abt how he feels komiye ya taso masa na cigaba in zaiyi da rayuwarsa ayanxu sai ya kusheshi.

Kallon khaleel din yake kamar wani baudadde wanda baisan ciwon kansa ba musmmn ma tun akan wani abu da ya faru dashi dacan yana makarntan likitoci, tun anan ya sauke sunansa akan duk wani kaddara da kamfanin sa da kuma manyan business da suke dashi a familynsu ya rike abunsa yanayi shikadai.

gidan nasu bawai babu nera bane akwaishi, kai mahaifyar sa ma kawai zata iya yin dede da meenal a arziki bare kuma dad dinsa dayake da matukar daraja da karama da ilimin sharia law dana bokon me yawa snn yana da manyan businesses awasu kasashen waje.

Khaleel din ne kawai ya ware gefe. Ya cire shi a sahun yayansa dayake jinsu aransa.

shiyasa khaleel din yake rayuwarsa agefe shika dai daga shi sai abunda yake samu na aikinsa da small businesses dinsa na phameceuticals..

Cikin kwana biyun halisa bata gane kansa ba, fushi fushi me aljanu aljanu haka takemai kallo, dadin karawa da meenal ta ga hoton hidimar vicky tagansa acikin guest sai ta fara matsa masa cewa yazo inda take shikuma yace mata sam bazaai bar halisa anan lagos yabita inda taje ba...tun ranar data furta mai maganan suke tashin hankli basu sauko kasa ba kusan Koyaushe ransa a bace yake.

Ana saura kwana biyu afara azumi yau sassafe sukaje wajen motsa jiki daga nan suka je ganin tashin grace a aiport da medical team din da zasu wuce india da ita..

grace nata kuka tana neman gafararta da tunanin hala bazata dawo nigeria a raye ba Haka halisa ta dinga lallashinta tana kara mata karfin gwiwa har suka wuce india jikinta be dawo mata dede ba.

Yanayinda suka rabu da grace was so emotional for her, har abun yazo yana nemn ya hanata bacci itama, tunani me yawa tay cikin dare taga babu amfanin aje kawu a kulle hannun hukuma sabida su, washe gari da safe suna fitarsu na karshe tay deciding ta tare khaleel da maganan kawunta.

Aikuwa tana furta masa suka fara samun sabani sabida tunaninsa daban natama daban.

Shi gani yake shimai iya kareta ne ya kuma rufa mata asirin familynta itakuma sam bata ma yarda dashi ba tukuna..

Haka ta sakashi ya kira nadra tazo aka tattauna snn aka saki kawu aka lafar da case dinsun cewarta koma yaya ne shine mata uba kuma jininta kwalli daya a dik duniya data sani tunda ta girma ne batasan dangin mahaifyta ba.

Asad sosai ya bi bayan halisa akan wann maganan nata data fada na cewa albarkacin alakarsu ta jini kawai yasa zata bari sakeshi yakoma gida duk dan yanason khaleel yaga misali akan ta ya saukar da nashi fushin akan mahaifinsa shima

Haka aka fito da Kawu duk ya jeme yay wani iri baki halinka da mugun mutum still yana kallon halisa matsayin me lefi.

khaleel da bai wani ji dadin sakeshi datace ayin ba har office yabishi ya tsoratashi cikin ruwan sanyi yasakashi yajeshi har garin benue da tunanin cewa zasu iya zuwa duk inda yake snn su kamashi su kulleshi msmn ma in sukaji ya taso da maganan halisa ko ya yyi yunkurin zuwa inda take dan ya bata mata suna..anan ne ma nadra tadan bi bayansa tasaka kawu agaba ya rubuta statements snn suka barsa ya wuce.

Washe garin faruwar hakan Ake tsammanin za'a tashi da azumi meenal nason dawowa ga mijinta dan suyi fito na fito akan kin zuwa wajenta dayayi amma tsoron kartazo ya sakata azumi ya hanata zuwa.

Bayan sun dawo daga agency Asad ne yabiyosu gidan suka sha hira wanda yasaka halisa ta
Dan girka musu abinci

Ta kammala girkin kenan tazo ta samu suna wani irin heated argument a falon a tsakaninsu.

Asad yanamai kafa masa misali da halisa yanamai ce masa ita dama ba kawu ne ya tsuguna ya haifeta amma duk mugun halinsan saida tay hakuri ta bashi darajar jini dana uba snn ta sakeshi amma khaleel yana musulmi za'a kama watan azumi bazai sauka ya dedeta kansa danasa uban ba.

Taurin kai da zuciya yasaka yaki sam ya yarda cewa matsayin sa dana halisa abu dayane

Halisa na tsaye da tray din abincin tanajin yadda yake furta wasu kalamai masu cike da taurin kai da fushi musmmn yadda mahaifin nasa ya ware sa acikin yan uwansa sabida abunda be aikata da son ransa ba.

Kota ina akabi Asad yasan khaleel ne me gaskiya amma gani yake kamar babu riba a irin rayuwar da khaleel di yakeyi shikadai anan familynsa na can gefe tunda shidin ma ya taba dandanawa ya ji abun babu dadi.

halisa batasan menene abun ba amma dagajin yadda ransa yayi mummunan lalacewa zakasan abun yana masa ciwo aransa har yanzu. Asad literally begged him akan shi ya amshi rashin gaskiyar kawai su dedeta amma yace sam dagaskiyarsa kam bazai amshi rashin gaskiya dan ubansa ya soshi ba.

The whole condition is affecting his family amma yace bazai yi hakurin ba. Ita kanta datakejinsu saida taji hanklinta yay mugun tashi da irin fushin nasa.

Motsinta da sukaji yasaka sukayi tsit kowa ya zauna kamar anyi ruwa an dauke..

Agaban asad din ta aje abincin wanda tunkan ta budeshi ya badesu da qamshin dadi nan suka danci tare Suna hira khaleel din be ce musu komi ba ya dauke kai ita kuwa sai satar kallonshi take dan gabaki daya ya sauya mata kamar bashi ba.

Bayan nan Asad yay mata sallama yace mata azumi nakaiwa biyu zasu wuce united states sai bayan sallah zasu dawo
Har ya bata wayarsa sukay sallama da nadra snn ta tahaura sama ta kyalesu su biyun suna zaune.

Bayan tattaunawa da sukayi kadan khaleel ya rakashi har can gidansu inda suka sauka, anan ya dan ja lokc sukayi hira tare da sallama da nadra da yaran asad din snn ya dawo gidan cikin dare a mugun gajiye.

Sauran abincin da suka rage yaci snn ya aje sauran a fridge sabida gobe zai tashi da azumi.

Maganganun Asad sune suka dinga dagulamai yanayinsa bai iyayin komi ba face tsarawa halisa abunda zatanayi
tunda sun je field na karshe kenan yau sai kuma bayan azumi zasu cigaba..

ynxu Suna stage six ne a treatment din nata zasuyi wani abu da ake cemai 'in vivo,".wato deep identification of trauma related events. Haka Ya saka mata rountine din shi sau hudu a sati, daga farkon azumi zuwa karshensa iya abunda zasu nayi agidan kenan.

Fannin halisa dake tasan babu inda zata da safe hakan yasakata ta sake jikinta ta share baccinta me yawa da safe ta farka taje kitchen ta samu gogar yay baki kirin da abincin garin dumawa.

haka ta zubar a bola snn ta wanke abubuwan tay makanta breakfast ta zauna taci da yamma tajecan waje ta same me gadi yana karatun qur'ni abunsa, daga nesa ta tsaya tana kallonsa tana murmushi tuna yadda uztaz da me gadin gidan
ta sukeyi, dan kusan al'adarsu ne karatun qur'ani da asuba ko da yamma ko da ba'a cikin azumi ba.

Sede wnn din warash ne sai sautinsa yay mata daban dake karatun zaure yakeyi cikin kwarewa..

Yana kammalawa tazo ta sameshi tana daga tsaye suka gaisa cikin ladabi sosai yake mutuntata

bataji dar dar aranta ba Tadinga masa questions akan karatun har ya ganar da ita cewa akwai karatun hafs akwai na warash wanda yawancin su da sukayi almajiranci irin shi sukayi. Ganin ta dan sake dashi har yadan tsakura mata labarin rayuwarsa da yanayin yadda ya taso cikin fafutukan nema.

Koda ta koma dakinta tausayin labarin sa daya bata yasaka ta kira ustaz ta umarce shi akan da su kara streching din kayan sadakan azumi na kamfaninta izuwa zaure zauren almajrai dake cikin wasu kauyuka da suke shan wahala da rayuwarsu.
Chapter 120 · 0% Book details