← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 312

Sashe 90

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tazo asibitin da bacin rai da damuwa amma kfin wani lokci dukkan wann abun yakau dan tanajin dadin magana da dr aseem sosai ganin yana fahimtarta fiyeda kowa

Koda ta tashi zata kira uztaz yakaiya gida shi ya hanaya yace mata kawai ta jira khaaleel suje gidan tare tabar uztaz yay aikinsa..she had no choice haka ta hakura ta zauna a office din dr yanata koya mata sabbin abubuwa harma bata san lokci yaja sosai ba dan har saida khaleel ya gama aikinsa ana daf da kirar asr ya fito, har gaban motarsa dr Aseem ya rakasu, ya bude mata gaba ta shiga ta zauna suka taho gidansan atare batare da sun ce ma junansu uffan ba.

Suna shiga gidan still basu kula juna ba Dakita ta wuce straight ta hau rage kayan jikinta snn tahau kan gadonta tafara bacci dan sosai ta gaji.

Kan Khaleel yadan daure ganin ogansa bece masa komi ba kuma ga halisan ma ta dawo ta kama bacci. Wanka yay shikam yadan huta snn yaje gari neman musu abunda zasu ci, ya tura ma ogansa sako akan hakan amma haryanxu bai amsa shi ba. Haka nan ya dawo gidan ya sameta tanakan bacci abincin ya aje mata akan table yaja mata kofarta ya fita.

Uztaz ya kirata har ya gaji gashi ya kira khaleel bai dauka ba, har yajeshi office ya same dr Aseem shine ya gaya masa cewa sun wuce gida snn yaji hanklinsa ya kwanta.
Dagata dayan bangaren bayan ficewarsa daga office din vicky wajajen 9am kayden ya shigo ajinsu cikin nitsuwa yaja wata kujera ya xauna bema lura da idanun da sukayi cahhh akansa suna binshi da ido ba
Dan shidin kyakkyawan namiji ne kyaun san har ya wuce misali duk dama ba fari bane but the fact that he is too calm da kuma irin exotic cars din dayake zuwa makarntar dasu yasaka kowa yake Allah Allah wani abu ya hadasu dashi...

Tunda aka soma lectures din yake latsa wayarsa hanklinsa kamar baiya wajen ya rike hadden p cap dinsa a hannu hakan ya dadasa ake saurin noticing golden hublot wristwatch da ya dauke hannun sa chif, pochy and classic rich guys awajen are seriously admiring him bare aje ga matan wajen dake jin cewa Kayden din maybe bama dan kasar bane.
Ayayinda lectures din yadanyi nisa ya fito da foldable system dinsa daga wata yar jaka ya ajeta akan table snn ya kunnata yana dannawa sama sama at same time hankalinsa nakan abunda akeyi a ajin.

Boyayyar email din kamfaninsa ya shiga nan da nan yaga sakonnin vicky sun shigo kala kala murmushi me sanyi ya kufce masa..

Tsayawa yay ya dan duba business proposals dinta da kyau sann ya tura mata amsa da cewa he is busy at the moment zuwa anjima zai tura mata da feedback just to keep her anticipating yasaka yace mata hakan batare da ta sani ba.

Wajajen 2:30pm vicky na zaune a office dinta tana duban sakon,duk fargaba ya cikata, a tunaninta hala ma wasu sun rigata turawa ko ma bazai duba sakon nata da kyau ba..

Tunanin hakan ya hanata sakat bata wani tabuka aikin kirki a schl din ba, sai can ta dan dudduba perfomance din sauran yaran dake hannunta taga kusan dukansu sunyi serious har sundanyi nisa kuma karatun ya fara mike musu, cikinsu kowa yakanyi assigment dinsa yay submitting online hasalima kayden ne kawai bai taba yin komi a board dinsa ba sai yau dayaga tazo....

a nitse ta dudduba file nashi taga bai tabuka komi a course dinta ba, mikewa tay tanufi office din other lecturers da suke daukarau ta rokesu suka dan duba mata records na sauran perfomance dinsa taga it was excelent wasu ma tana ambatar sunansa suka fara bata labarin sa suna cewa ai yaron genious ne, The new student is very good"

A matsayinta na wanda suke hannunta sai dai tay murmushi amma aranta gabaki daya ta cirke.Tunani take in har kayden na iya gane koyarwan kowani malami a schl din toh mesa ita baya gane nata.

Is he tryng to foarm familiarity dan yaga shi kanin abokin mijinta ne
Ko yana tunanin kawai zata bashi A ne batare da yay kokari ba..

Da haushin hakan ta nufi ajinsu kai tsaye lokcin lecturer dinsu na kkrin kammalawa. Student gabaki daya idanunsu suka koma kanta dan bata taba shigowa ba sai inhar lokcinta yayi.

Suna gaisawa da malamin tace masa i want to speak to one of ur students.

Daga nan kai tsaye ta nufoshi ta bata rai sosai shikuwa duk sand ya ganta sai zucyarsa ta tsaya cak ya dena motsi.

Harta iso kansa be dena kallonta ba. Tana tsaya tace mashi "Are u done with the assigment???
Ahnkli Yace yes.

Tace send it now.
Ya dau wayarsa ya turo mata a board, take ta bude wayarta tay forwading masa 5 hot home works masu zafi snn tace mai to be sumbmited by 8am tmrw morning unfailingly.

Daga nan ta tafi ta barsa yana murmushi dan yasan bazai taba yi ba..

He prefer to fail her course on and on inde zata dinga bashi special attention evryday..

After few hrs Tana office
Dinta assigment din data karba wajenshi ya dada harzukata ya bata mata rai dan wani shirmen yay aciki..this boy is going to give me headaches. Gashi tanata fargaban ko kamfani zata amsata anjima ko bazata amsata ba. Wajajen karfe hudu na yamma ta fito zata wuce ta duba shops dinta dede ta fito kenan tagansa shima yana fitowa kamar wanda aka sanar dashi dede lokcin fitowarta. She canr deny tue fact that his soft lufe is amazing amma takaicin shi ya riga da ya cikata..tana shiga car dinta shima ya shiga almost d same time suka bar schl din kamr yadda suka shigo atare.

Bangaren halisa sai wajajen yamma lis snn ta farka daga bacci. Tarin miss cals din data gani awayarta yasaka ta kira uztaz sukayi magana, dashi kawai sukayi waya ayau sabida batajin dadi sam sai tace masa ya huta kawai yau karyazo sai gobe..

Ahankli ta dukunkune kanta daga kan gadon acikin cinyoyinta kafafunta na rawa rawa ga wani irin zufa dake keto mata ta koina sabida azaban ciwon kan dake juyata, tun tana mike har saida takai rigingine awajen tana juye juye,Dukkanin abubuwan da suka faru yau su suka shiga dawo mata akanta daya bayan daya musammn ma na tattaunawarsu da dr aseem, She stayed in melancholy for a while tanajin zata iya danne zucyarta ne ko ba zata iya ba???..duk ta rasa wanne yafi kauri aranta

Hakan yasaka ta dauki
Wayarta tafara scrolling number har takai kan lambar jasmine kamar zatay dialing sai kuma ta fasa Ta raya aranta cewa wann karon raayin kanta kawai zata bi, ji take kamr she doesnt hav to obey the rules,rayuwarta ne bana kowa ba, ba lallai ne Tabi dukkanin abunda Dr Aseem ya gaya mata tay but she is willing to stay here and challenge her heart danta fidda wann fushin data keji akansu gabaki daya so that when she is out der to live her life on her own presence dinsu a duniyan nan bazai dameta ba.

tsahon lokacin data dauka ahaka yasa ta jin kamar anyashe mata hanjin cikinta ne,
tuni ta soma harsahen hala ba ciwon kan bane kadai harda yunwa dan rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare,tashi tayi zaune a hankli tana waige waige ganin babu motsin kowa,gashi bata son shiru yayi yawa ba waje yakan tuna mata wasu mugayen abubuwan data riga ta binne akasar zuciyarta

Saida tay tunani me zurfi kafin nan taci abincin da khaleel ya aje mata ta shiga wanka ta fito ta dan kwanta dukkan gabobin jikinta a muce.

A hnkli ta koma ta kwanta ta rufe idanunta gam gam zuciyarta yau sanyi cikin ikon Allah kuwa saiga wani baccin mai mugun dadi ya kwasheta da alaman hakan nada nasaba ne da wahalar datake sha na rashin samun cikakken nitsuwa ta zuciya..

Tun daga nan gidan ya dauka da wani irin shoru khaleel ne kawai acikin gidan amma bazaka taba sanin hakan ba dan tun shigowarsa ya nufi dakinsa ya zauna akan couch dinsa yahau yar danne dannen sa a laptop as usual feeling so helpless and lonely sabida wani irin mugun shiru da koina ya dauka

Yau ko sanin inda matarsa meenal take baiyi ba dan tun safe ta wuce office itama bata dawo ba ,duk dama ya riga da yasaba da irin wannan rayuwartata but he was nearly choke up today sabida abubuwan da suka faffaru.

haka kawai saiya soma jin wani irin mutuwar jiki da kasala na yawan damunsa. ..

tun arond 10pm na daren ya gama komi ya kmmla tsarawa halisa routine dinta ya zauna shiru shikadai a mugun takure dan baisan mema zaiyi ba,gashi inba aikin sa ko wani meeting ba shi bai iya zuwa koina don rage dare arayuwansa ba, he is a chronic home addict, zan iya cewa arayuwar sa shi bai taba daukar kansa da kansa zuwa wani club ko wajen games ko wani wajje na shakatawar rayuwa ba,he neva care for that infact he hate it tunanin hakan ma baiya yawan zuwa masa a duniyar sa.

Tashi zaune yy akan gadonsa ya zauna da fillo rungume a kirjinsa kenan haka zaita zaman kadaici yau agidan?ders is No one to keep him company infact babu mai lekowa ta sashin ya dubasa bare aje ga kawo masa wani abun tabawa abaki..he missed living a normal life ,inbawai shine dakanshi zai fice ya siyo abinci ba to bamai kawo masa

Hours passs by Can dare Yana fitowa daga wanka ya rasa abunyi kuma yasan ba bacci zaiyi nan kusa ba, zama yay abakin gadonsa dan ba ama maganan zuwa wajen matarsa meenal dan yasan yadda yakejin ba dadin nan aransa hala inyaje ma bazasu kare ta dadiba.
Chapter 90 · 0% Book details