← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 312

Sashe 92

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya badiatu ce ta matsa akan lallai yau din kawai su tafi dan sam batajin dadin yadda hafsat take xama agidan tana kallon mahmudu suna rayuwar aure da matarsa kullum tamkar ita hafsat bata da wann hakkin akansa.

Tun sassafen da suka tashi tasako hafsat din agaba tace mata ta tattara kayanta kawai zuwa karfe biyu na rana jirginsu zai bar kasa.

Harta kammala prking dinta suka shirya kominsu na karyawan safe mahmud yau bai fito ba har sai can wajajen karfe goma sha daya kafin nan saiga nan shema'u tasha kwalliya ta sauko zata wuce ta cikawa rigarta iska hjy binta ta tsareta da tambayar inda yake
Nan take gayamusu cewa tun da asubah aka kirashi site din sabuwar aikinsu na contract ya fita...

hajy taji dama dama aranta, basu mata komi ba harta fice agidan ta shiga gararinta agari..Hajiya batay kasa a gwiwa ba ta tura masa tex ta gaya mai abunda suke ciki snn ta umarce shi akan ya dawo su sallame hafsat din tare..

Shikuma acan wata babban harka ce datafito sabuwa dar agabansa take kkrin buduwa masa, as a top class enginer, yasaka aka dorashi a matsayi babba na wanda zasuyi desining sabuwar project din dake gabansun da wasu yan chine sukai hadin gwiwa dashi..

He is putting his best once again for the sake of shemau, a tunaninsa inhar ya samu wann gurbin aka amshe design dinsa zai iya samun kudi me yawan da zai iya ma shema'u dukkan abunda tayi requesting awajen shi da abubuwan datake so yay mata irinna kawarta hadiza maitama.

Sosai wnn aikin yasha masa kai wanda har baison yaga ya bar wajen batare da ya kammala desing dinsa ba, hakan yasaka ya kashe wayarsa gabaki daya dan ya nitsar da hanklinsa akan aiki duba da yana da yaqinin cewa inhar ya samu kudin da zai bawa shemau irin rayuwar hadiza datake so hala zata dawo hayyacinta tafara nuna masa irin kulawar da zaisaka iyayensa su dena kuka da aurensun kowani lokci.

Dga gidan kuwa anjira dawowarsa har angaji mahaifinsa ya kikkira shi amma shiru harde suka hakura suka kyaleshi

Aranar sosai hafsat tasha nasiha wajen iyayen mahmud wanda kusan shiya kara mata karfin gwiwa akan dukk abunda ke shirin tun karota anan gaba.

Bayan sallahn azhr ta kammala shiri ta sauko cikin black abayar dubai yasha kwalliyar stones ya mata matukar kyau fuskanta ba komai daga powder sai kwalli ta tarar da kowa na falo.

Sunkuyr dakanta kasa tay ganin Fuskan su ba asake yake sosai ba duk rashin dawowar mahmud ya batawa mahaifyar tasa rai harta kusa zubda hawaye aganinta koba komi zaizo yay sallama da hafsa tunda ba waje nan kusa zata je ba.

Ahankli hafst ta dago kanta da yanayin damuwa aranta tanata kallonsu a fakaice batare da sun lura da hakn ba.

tana isowa gabansu ta rusuna har kasa cikin sanyi murya tace mama na gama shiri Da dan kirkiraren murmushin suka amsa ta da cewa "Alhamdullhi..nan ma suka mata nasiha akan ta nitsu tay abunda yakaita can. Har hawaye takanji suna taruwa a idonta musmmn taji yadda hajy badiatu take mata nasiha akan aure.

Itakam ma auren ya fara fice mata aranta amma sabida su zata daure dan har izuwa yau bata ga wani haske ata wajen mahmud ba.

A yar wautarta takanyi tunanin cewa duk sanda baiya nan a gidan ko yake cikin dakinsa yana tare da shemau ce..

Wanda hasali hakan bai fiye faruwa ba sabida shemau tafi spending darenta tana chat din soyayyarta da saurayi da safe kuma ficewa take batason zama a gidan amma dake yakan nuna bai damu da ita kamar yadda yadamu da shemaun ba yasaka hakan yay karfi aran hafsa bana wasa ba..

Driver ya taho ya loda kayayyakinsu a bayan booth sukayi sallama da kowa snn suka kama hanyar airport din Abuja .

Anan intnl airpot din ma sosai hafsat tay ta saka tsammani a zcyarta waiko mahmud zai zo yay musu sallama amma ina har aka soma kirayen suna suka shiga jirgi ya tashi dasu bataga me kama dashi a filin jirgn ba. Frm Abuja izuwa birnin istanbul is a journey of 8hrs 46 minutes. Gani hafsat tay kamr basu kai turkey tafara shimfida sabuwar rayuwanta acan ba tsabar ranta baya mata dadi, Kafin nan su isa birnin garin zazzabi me zafi ya rufeta sosai.

After few hours gidan nasu ya zama so quiet hajiya badiatu ce ita kadai daga ita sai tunaninta. Mahmud bai tashi dawowa ba sai can wajajen karfe goma na dare. Dan saida ya kammala abubuwan da zaiyi tass yay submitting ma federal gorvenmnt supervisors da spr contractors kafin nan
Ya dawo gidan a mugun gajiye...duk da haka bai hanashi leka dakin mahaifyarsan ba, yana lekowa ciki kuwa yaganta akwance akan gadonta tana baccinta peacefully ga karatun qurani nan na playing shikadansa wanda koda bai sani ba yasan ranta abace yake dashi sosai.

Ya jima atsaye awajen da sanyi jiki yana kallon fuskarta dan shikadai yasan irin abunda yakeji aransa inyana tayar mata da hankli musmmn ma akan matarsa shema'u.

Ahankli ya rufe mata kofar ya koma room dinsa ya samu shemaun ma nakan bacci yasha mamaki dayazo yaganta hakan dan yasan ta da son chatting din dare.

Wanka yay ya kwanta agefe da ita sede daga hafsat ta fado masa sai yaji sam bacci ya kasa zuwa idanunsa..

He kept promising himself akan cewa zai gyara komi dake tsakaninsu muddin ya cikawa shema'u burinta dan aganinsa duk wann abunda shemau takeyi masan dan bai biya mata bukatunta bane amma daga zarar yay rayuwarsu dika zai iya zamowa dede.

Ganin baccin ya kasa zuwa masa yasaka yay nafilfi cikin dare, after a while bayan ya gana aduoinsa na neman nasara akan abunda ya sako agaba, ya dauki wayarsa yay tracking time din kasar turkiya
Its almost 2 hrs ne marabanmu dasu dan haka karfe 4am nayi na asubhi ya danna kirawa antynsa dake yasan acan kasar turkeyn ynxun karfe 6am ne.

Kusan sau uku wayar tay ringing ba'a dauka ba sai can daga bisani ta dauka tub basu gaisa ba ya saukar da muryansa kasa yafara bata hakuri sosai harsaida taji tay sanyi. Duk da hakan ba shi yahanata masa fada akan rashin dawowarsa jiyan yay ma matarsa sallama ba. Yace mata aiki ne ya rikeshi shiyasa ma yanzu ya kira dan yaji yaya suke. Luckly enuf lokcin hafsat din tay sallah kenan zazzabin bai wani gama saketa ba tana shirin komawa saiga hajya binta da waya a hannunta ta mika mata ta amsa duk ta dauka hajiy badiatu ne yasaka ta daure ta gyara muryanta dan karta daga mata hankli.

Da sanyin murya tace mishi salam alaikum..
shiru yay bai amsata ba ganin yadda shemau take juye juye gashi baison taji me zaice awayan, dan haka ya mike tsaye ya fice waje da wayar a hannunsa snn ya amsa mata sallamarta babu yabo babu fallasa.

Gabanta sosai yafadi dataji muryansa jin wani abu ya tokareta a kirji muryanta kasa kasa tace
"Mashi ina kwana?.
Cikin sauke ajiyar xucya yace lfya ya hanya
Kun isa can lfya.. tace mishi eh, shirune ya dan ratsa tsakaninsu kafin na yafara mata magana jin muryansa kasa kasa tasan da cewa baison shema'u tanajinsu ne.

Lumshe idanunta tay tanajinshi dan kusan maganan data saba ji yana gayawa iyayensan shine yau itama ya gaya mata. Cewa ynxu lkci ne da zata nitsu tay karatu batay focusing akn auren su ba. A cewarsa komi da lkcinsa, kuma duk abunda ya faru dasu qadadarrre shi bazai ki zama da ita, sede babu abunda ya kashe mata jiki yake kuma krya mata zucya kamar cewa dayay inhar anan gaba taji bazata iya zama dashi ba shi baida matsalan hakan. Tun da ya fadi hakan taji hawaye na sauko mata babu iyaka.

Dan Tasan yafadi hakan ne dan yasan yana da mafita tunda ga matarsa dayake so atare da shi, ita kuma aynxu haka baza ta iya kwace kanta acikin cakwakiyar aurensa ba kodan tausayin iyayensa da halaccin datake ganin suna mata musammn ma hjy badiatu datake nuna kishi akanta banawasa ba...basu wani jima suna maganan ba suka karkare ta kaiwa hajya wayarta dakinta tazo ta kwanta akan gadonta tana hawaye sosai.

sauran abubuwan da ya rage suka tattauna da hjy binta, yay mata alkwari cewa zaina aiko mata dukkan abubuwanda hafsat din take bukata lkcin zuwansa inyay kuma zai sanar da su kafin yazo..nasiha ta masa kafin nan suka katse wayar sai a sann yaji hanklinsa ya dan kwanta kadan, sede Izuwa yanxu Duk damuwarsa fushin mahaifyarsa ce.

Hakan yasaka baiy kasa a gwiwa ba ya nifi dakinta sassafen shiya tasheta da ruwan shayin dayasan tana matukar son shanshi kowani safe. Da kyar ya shawo kanta ta saurareshi ahakan ma dan ya ce mata ya kira hafsa din sunyi magana ne taji dan dama dama.

After few min shemau ta farka a bacci jin wayarta na ringing da video call ta dauka abinta bata damu da gaggayara jikinta kota rufeshi ba dan haryau a matsayin budurwa take a idon saurayin nata ba matar wani ba.

Hira suka tsundumayi na soyayya as usual yana yaba halittar jikinta yana sawa tanajin duk duniya babu mace me kyau data dace dashi kamarta.

Rashin dawowar mahmud room din da wuri ya bada shemaun babban daman yin wayarta hankli kwance.

Anan ne alhaj shafiu yake gaya mata zancen wani babban harkan gina hanyoyi da manyan makarntun gwamnatin tarayya da kowani me kudi yake muradin cafkewa sabida akwai maqudan kudi da zasu fito a harkan bana wasa ba.

As usual atake yay mata alkwarin cewa kamfanin sa ne zai samu aikin sabida yana da kafa a gwamnati yasan muhimman mutane.

Take yasataji cewa kudin na zuwa duk akanta zai kare gashi bakaramin kudi bane, babban aikine da zaiji billioyin kudade sabida yawansa da muhimmancin sa ga siyasar kasa. Tunda ya soma mata hirar aikin jikin Shema'u ya soma rawa rawa tabi ta rasa nitsuwarta gabaki daya jinshi datake yana cewa zai nema mata wani aikin aciki wanda zata yage rabonta itama.

Yace mata yanxu haka yaune engrn kamfaninsa yake shirin tura nasu design din kuma yanada yaqinin cewa nasun ne kawai za'a zaba..
Chapter 92 · 0% Book details