← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 312

Sashe 27

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda tun a hanya ta sanar dashi isowartan dan Bakaramin zumudin junansu sukeyi ba shiyasama tana isowa tagansa atsaye yasha manyan kaya na alfarma daga samansa har kan takalminsa me tsadace ga tarin body qurds dinsa agefe sun dan kewayashi wani irin jin kanta takeyi sama sama dan sosai take son taga kanta acikin irin wann rayuwar ta manyan maza masu murza kudi koda kuwa babu wata soyayyar gaskiya aciki.

Wasu kayattucun murmushi take sakarwa ganin shine dakansan yazo ya tareta daga cikin airpot acikin dankararren motarsa da gwamnonin jihane suke shiga kirar landcruser X20 limited edition an mata convoy na motoci har guda hudu..

Tunda ta shiga motar tabi ta hakimce take jefo masa kallo mai nunnuke da salon rigima tareda da jan aji irinna manyan mata wayayyu, shikuwa kallonta kawai yakeyi yanata lashe baki dan kyaunta da siffarta na tsegerun mata yazo dede da irin matan dayake muradin hada hanyarsa dasu, daga nan suka tsaya awani hadaddiyar pub na masu kudi cikin anguwar Maitama suka sha ice coffe da breakfst din turawa marar nauyi sunasha suna hira shaff tabi ta mance da abunda ya kawota Abuja.

Dagata dayan bangaren hajya badiatu da yar uwarta hajya binta basu yi wani hirar kirki ba suka tattara suka fito babban falon gidan suka baje kolinsu, kan kace Wani abu kusan rabin ma'akatan gidansu mahmud din sun kewaye bakuwar tasu da gaisuwa ta bangirma dan takan jima sosai batare da tazo kasar nigeria sede basu iya mancewa da ita sabida ita mace ce mai halin dattako da son kyauta sosai.

Barkan ki da zuwa Hajiya Allah yasa anzo a lpya...kusan kowani ma'aikaci yana Miko gaisuwarsa cikin yanayin girmamawa da nuna farincikin sa da ganinta

Murmushi takeyi me sanyi tana cewa "Sannunku dai"
Sannunku
tana yi tana Dan waving dinsu da hannu, An sameku lpya?duka Sukace lpya lau ranki shi dade..
Nan kuwa ta juya tana kallon Driverta datazo da shi da safen nan tace
"Mallam munnir sai ka babbasu na shan ruwa ko,Da sauri ya rusuna kai yace toh hajiya Allah kare ki angode,..Duka sauran ma'aikatan dake washe baki suma suka bibbita da addua, nan yaje ya dauko jakarta ya bude ya fidda sabbin bunches din dari biyar biyar ya shiga rarrabamusu 5k a hannun su tuni wajen ya kaure da godiya da yabo kowa na washe baki.

Itakam Bata kara ma kallonsu ba ta riko hannun hajya badiatu tanamai cewa nikam nagaji kikaini wajen ɗana mahmud ko ma jikinshin ne ya hanashi fitowa har yanxu oho???

Babu musu suka nufi ciki A hankli suke tafiya sabida yanayin jiki dole sai an bita a hankli musamman ma da bata fiye son zaman waje daya bajirgi suka biyo suka zo Abujan daga turkey amma still saida jikinta yayi tsami da kyar take Jan kafarta take takawarta a hankli.

Suna daf da bude kofar bangarensan sukaci Karo dashi yafito shima fuskarsa dauke da kyakwan murmushi wanda kallo daya zakamai kasan yana tsananin murna da isowartan.

da sauri sauri ya karaso da alamn an riga an sanar dashi labarin isowarta, yau Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin chairman ne a jikinsa wanda a ƙalla zaikai Darrikan kudi ybi ya ɗaura baƙar hular khufya akansa Hakan yasa Fuskarshi ta fito ras sajenshi da gemunsa mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi..

Wajen hajy bintan ya nufa ya rikota ajikinshi ya rungumeta tsam wacce already tana Hade idanun ta da nashi ta fara sauke wasu maqudan hawaye.

Dan Rabuwarta da ganinsa ido da ido tanajin tun lokcin hidimar aurensa da shemau.

cikin muryanta mai aji da bai fitowa sosai "tace' mahmud?"yana murmushi sosai yace naam small mum.
Wani shafa kansa tayi a lalume tace "Alhamdullahi,saita juya ta kalli yar uwantan dake famar Murmushi tace Alhamdull yau gani ga mahmud its been soo long wayyo Allah....

Mahmud dake Murmushi yace nayi matukar farincikin isowarki mumy, Ta juyo cikin muryan jin dadi tace "Ohh mahmud, ashe dai jikin naka da sauqi, toh Allah ya sa maka albarka Allah ya kau da idon maqiya akanka.

Yana murmushi Yace Ameen Kara rungumesa ajikinta tayi Da Murmushi akan fuskarsa har suka gaisa da nahaifyartasa wanda tuni idanunta ya cikko da ruwa itama dan sosai suke kallon mahmud da daraja sabida shi ya yakasance mutum ne mai mugun shiga rai da son kyautatawa nakasa dashi.

Cikin sashen nasa ya musu jagora, hjya binta ta juyo da baya ta amshe jakarta da wayoyinta ta kuma umarce driverta daya sa ma'aikatan gida sutayashi shigo da kayan su da sauran abubuwan tsaraba da tazo musu dashi.

Suna zama bai wani daukesu doguwar lokci ba suka soma hirararrki na yaushe rabo, anata raha ana dariya ,sede duk hanklinsa ba ajikinshi yake ba dan aransa yasan dolene hjya binta ta tambayesa batun shema'u, suna hirar jefa jefa yana latsa wayarsa yana dialling lambarta izuwa yanzu yay mata tex yafi sau ba adadi amma bata amsa ko daya ba.

Ana hirar ne kawai amma gabaki daya hanklinsa baiya wajen face saida wani sassanyar sautin murya mai mugun sanyi da darsa kafafen tarihi acikin zuciya da aka gaishesa dashi ya dan ratsashi tare da dawo dashi cikin hayyacinshi acikin gaggawa ya lumshe idonsa ahankli snn ya kuma budesu.

Sanye da hijabi hafsat ta shigo cikin sashen kanta na kallon kasa tana tafiya ahnkli sosai kusan ince dauriya kawai takeyi amma badon tana da wani cikakken gwarin gwiwa ba.

hannunta dauke da babban serving tray dan dama ta riga ta saba da aikin gida, shiyasa sam batajin wani dar dar aranta intanayinsa dan tun kafin akawosu aiki agidajen masu kudi a legas ake koyar dasu kala kalan girke girke dan a samu a karbesu da wuri dillalan su kuma suyi kasuwa.

Acikin nitsuwa tay musu sallama snn ta fara jera musu Abin karyawan data zage da zucyarta daya ta shirya musushi dakanta batare da tabar mai aikin gidan sunyi komi ba.

Hadadden sinasir ne dayaji wani irin kayan hadi tare da brown spaghetti jolof mai flaky meat balls akai tana baza wani qamshi mai azaban dadi, tabi tay garnishing kan Abincin da hadadden chizzled salads dan ya kara ma duk wanda zaici abincin appetite ta zubashi sama sama bamai yawa sosai ba. Snn ta musu plain tea mai kayan qamshi da zallan madara.

Albarka kawai hajy badiatu take saka mata harta kammala serving dinsu ita da yar uwarta hjya binta.

Dadin Qamshin Abincin yasaka hajya binta ta kasa haquri sai tambayar yar uwarta take ko hafsat dince ta girka abincin dan ganin datay ma yar yarinya da bazata haura sha biyar sosai ba.. ayayinda kunya yasaka hafsat din ta fice taje dauko flask din kunun daka data damashi domin mahmud dake zaune agefe baice musu uffan ba musmmn ma da suka kama hirar yarinyar.

Yanaji mahaifyrsa tana famar bada labarin komi da komi a yadda faru arayuwar hafsa tamkar wacce ta jima da saninta dan kusan koyaushe suka zauna sai tasha cikinta sunyi hira me amfani.

Labari take bawa yar uwantan musammn gameda yadda ake kawo yan mata daga kauyuka snn azo ayi training dinsu a garin lagos akan sana'a iri iri kamar wasu bayi badon komi ba saidan aci riba akansu.

Suna cikin hirar suka dan katse ganin gata nan ta dawo. dago kanshi yy idanunshi suka sauka akanta tsayawa yay yanata kallonta kusan gabansa ta aje flask din direct, gabanta na mugun faduwa sabida haryanxu akwai wann shakka da kuma tsananin girmamawar datake kallonsa dashi, can snn ta juyo ta dan kalleshi ahnkli cikin sauke boyayyar nunfashi tace masa "ummm ina kwana? Ahnkli Yace lfya..tace umm ya jiki..
Can tsakar kansa yakejin sautin muryan nata mai sanyi da shiga jiki tambayarsa take ko dinning zata kai masa nashi abincin. Bata maji amsar daya bata ba sabida yay nisa cikin wata duniyar da shikansa baiyi zato ba..

Imagining yake aranshi inama ace matarsa shemau daya bata dukkan zcyarshi ce take mishi irin wann biyayyar
Da nuna kulawar da shikenan shikam yasan baida wata matsala a rayuwarsa.

Mikewa yay lokci guda ya koma bisa kan table din babu yabo babu fallasa yana zama yaga harta biyoshi da iya kayan karyawansa kusan kominta a nitse take cikin saukar da kanta kasa dan ko kadan bata dauke kanta bakin komi agidan ba bare a wajen sa dan gani take shiba sa'ar aurenta bane na har Abada.

Tunda ta bude wamer din tafara serving dinsa gizon fuskar shemau kawai yake gani akan fuskrta yabi ya kureta da kallo sosai batare da tasan dalilinsa ba.

cikin bude ido da lumshewa yaga wai harta fara zuba mishi abincin acikin plate normally kamar yadda ta saba zuba masa dan dede. Ta zuba kunun a cup ta miƙa mishi cikin ladabi. Tabi ta zuba masa ruwa a glass cup ta aje agefe. Snn ta nemi waje ta zauna har ya kammala cin abincin wanda yake cinsa ahakli kamar bazai kai bakinsa ba har ya koshi dam dam kuwa.

Yanajin hjy binta suna kkrin jawota cikin hira amma kunya da tsoro duk ya cikata yasaka bata iya wani amsasu sosai ba. lura dayay cewa yanayinsa ne yasata kasa iya sake jikinta awajen, cikin dabara ya miƙe yace musu zai canza kaya suje waje.

Babu bata lokci sukayi waje cikin minti kalilan ya shiga dakinsa ya bude closet ya dauƙi wani dogon wandonsa kalar ruwan toka da thick singlet yana murmishi ya sakasu ajikinshi ya fita.

wajen motsa jiki ya nufa direct ya hau machine din gudu Babu abunda ke yawo a mind dinsa sai makoman rayuwar auren sa da shemau, gani yake kamar lefinsa na rashin mata irin romantic suprise da akama hadiza yasaka shemau ta dena daraja auren nasu gabki daya, tsabar tunani har koinanshi sanda ya mimmmiƙe after like 30 gud min ya sauƙo kasa yana dan haki.

karamin wipe din dake jingine da cliff din gym din ya dauƙa ya hau goge zufa zufan dake tsatsafowa a jikinshi snn ya nemi waje ya zauna yay shiru aransa yanamai cigaba da tunani.
Chapter 27 · 0% Book details