← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 312

Sashe 34

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi me nauyi ne ya kufce mata cikin zulumin rashn sanin me zatayi Ta dauke katon single red rose din dake kasa tana kallo ahankli takai hannu ta tura shi kan fuskan ta kamar me shakar daddan qamshin jikin roses din

Wani tsabar sanyi da Farin cikin daya mamaye ta a wannan lokacin jinshi take tamkar babu mahadin shi..

sakin flower tayi akasa da gudu tana dariya ta dauki balloons din dake kasa tana wasa da su.

she looks vry excited harta manta da condition dinta nata na dar dar din zaizo ko bazaizo ba duba da yana fushi da ita,
altho she have a strong feeling in her heart najin cewa hala daga goben rayuwarta ne gabaki daya zai sauya mata for good....
#SURAYYAHMS
NOT A FREE BOOK MAISON KARANTAWA CHAT ME 08060712446

I WISH U ALL A SUCCESSFUL IBADAT.

IN SHA ALLAH DAGA MUN DAWO POSTING ZAI SAUYA IZUWA BIBBIYU ARANA ADAURE ANA COMENTS DAN DA BAZARKU MUKE TAKA RAWA.

MUCH LOVE...AS WE WAIT FOT THE HOTESST LOVE BANGERS🔥🔥🔥🔥🔥🔥 DAT IS COMING FOR US IN NEXT LINE OF THIS STORY... KU GRGIJE KU SHIRYA MASA DAN AKWAI DRAMA DA ABUN DUNIYAN WATO SOYAYYA🙈🙈🙈

AYI HUTUN RAMADAN LAFIYA⭐
08060712446
▶️1️⃣8️⃣.

Bayan kamar awa guda gidan meenal din ya dauka da wani irin shiru tamkar ba ayi wani hayaniya acikinsa da safen ba ayayinda dukansu matayen suke kulle cikin dakunansu kowacce da yanayin data tsinci kanta aciki na hargitsar tunani kala kala kuma mabambamta.

Sam meenal takasa zama waje guda, tsiriyar hannunta mai tsananin laushi dake nan soo fresh yay jazir har ya tara xufa sanadiyar yadda ta damkeshi da karfi tanamai jeka ka dawo atsakiyar fankacecen room dinta da tunanin irin hukuncin da zata dauka akan mijinta khaleel,Da kuma halisa.

Wanda ata dayan fannin Kwance halisan take Dik tinani ya cikata tayi lumi kan gado tana kokarin calming zuciyarta da yau zafi akan zaman dole daya kamata anan gidan da bata kaunar ganin kanta aciki kona scnds wanda duk gani take kamar lefin duka na khaleel ne...

Yanayin yadda ta lumshe idanuwanta ta nitsar da kanta akan gadon zaka rantse babu abunda yake damun zuciyarta saidai ita kadaice tasan me ke mata ciwo arantan sosai.
Dan kuwa jitake kmr ma tsanar datake ma khaleel ya karune aranta dan haryau bataga dalilin da zai ajeta agidansa duk da yasan bason hakan takeyi a wann lkcin ba...

Jin kanta takeyi acikin yanayin matsatsin matsi da kuma takura, dan atmospher din gidan baimata dadi sam.

Duk juyin datay akan gadon sai ya taho mata tare da hoton kyakkwar fuskarsa wanda ahalin ynxu haushinsa takeji har cikin kololuwar xuciyarta irin haushin nan da ita kanta batasan iyakarsa ba.

wata hutacciyar tsaki mai cike da yanayin kufula dayake xuwa mata tun daga cikin kokon zucyarta har izuwa kan makwaronta shine yake kufce mata.

Duk sanda ta bude ido ta rufe sai taji zuciyarta ya harba da haushi, atake kuma sai ranta ya dauka da bambami da mita akansa, aranta cewa take "He is so rude, baida aji Komi dei sai ya nuna ikonsa akai Baida tausayi baida tarbiya sam sam, he cant even respect a woman's decison mtswww but she wll make him.

Ta jima cikin zancen zuci kafin nan wata nannauyar ajiyar xuciya mai hade da tsaki mai hautsinannen sauti ya kufce mata,.lumshe idonta tay ta bude can kasar wuyarta ta furta
"zanyi maganinshi""..
Sann ta juyo ta hannun hagu tareda rungumar kanta tay shiru batare da ta sake kawo tunanin sa aranta ba, tafi awa guda ahaka Har saida tagaji tadan saka kanta baccin dole na yan mintoci snn ta farka takejn haushin Abun ya dan ragu mata aranta.

Gabobin jikinta duk sun mutu, sam bata jin guzari tabi tay mashak bisa kan gadon, ahankli ta bude idanunta da sukayi jaaa tana bibiyar cikin dakin da kallo. Wani irin takaicin ganinta anan din taji yana shirin shakure mata wuya sede darajar Dr Asim din yasaka ta danneshi tahakura kawai zata dan sassauta ta zauna amma ba dan tanason haka aranta ba.

Ahnkali ta Rungumi pillownta tanamai sauke ajiyan zuciya masu nauyi
Cike da ayyana wasu abubuwan aranta.

Bahaushe yay gaskiya dayace fadar dayafi karfinka saika maidashi wasa.

Gefe Ta juya ahnkli ta lalumo wayarta cikin gyara zama ta budeshi ahankli ta fara rubuta sako cikin dakikanin lkci bayan kamr mintina uku ta danna send san ta aje wayar agefe ta yunkura da niyyar miƙewa zaune ahankli jin wani irin jiri mai karfin tsiya na yawo da ita atake ya fixgeta ta dawo baya kan pillow hannunta tabi ta dora bisa kan ta ta rikeshi sosai jin dakin kamar na juyawa da ita tsabar jiri ga wani azaban ciwo dakantan yake mata.

Wanda ko da ba agaya mata ba tasan da akwai na bala'in yunwa datakeji dana tsananin bukatar hutu da sassan jikinta yake bukata a wann lkci.
Shafaffen Cikinta taji yana kugi tare da kuka tabi ta damkeshi shima sosai ta lumshe idanunta sosai..

Kowani dakikanin lkcin data dauka ahakan bakaramin azaba takeji ba dan yanayin datakeji na tsananta mata tsabar yunwa har yawunta ya fara daukewa gabaki daya sede kodede na minti daya bata kawo tunanin jin sha'awar cin abincin gidan meenal ba ...

Hannunta na rawa rawa Ta sake jawo wayarta da kyar ta kara rubuta ma uztaz da sakon Abinci snn ta nemi waje ta dan kwanta jin jikinta ya dauka da wani irin zafi sosai.

30 minutes later
*********

Meenal ce tsaye agaban fankacecen huge italian oval mirror dinta mai nuna mutum daga sama har kasa dake manne da bangon dakin takurewa kanta idanu ayayin da ta kammala shiryawa cikin sabuwar dressing dinta.

fitted gown ce na tetsur turkish material, green colour mai balain laushi da tsantsi wanda basai an gaya maka matarial din me tsadace sabida kyaunshi dake wanxuwa a sarari.

Juyi take hannunta na bisa kugunta dinkin ya kame dirin jikinta damas shape dinta na yan gayu ya fito zak zak duk dama yau tay kkri ta rufe kanta tay rollng dinshi da multi color veil dan karami.

Babu yabo babu fallasa tay murmushi altho she is not satisfied da dressing din sosai koda shikema mum kawai zata gani dan haka zata iya daurewa.

Da kyar ta bar jikin madubin Bayan ta gama yaba kyaun halittar da Allah ya zuba mata a gaban madubin dan kuwa a kullum ta kalli kanta sai taji ta kara burge kanta dan gani take duk wani wanda ya sameta ya taka karshen sa'a duniya da lahira ya samu rabo. Tana ji da kanta makurar ji dakai. Ta kuma yarda da kanta, tanajin duk duniya ita kadaice macen data san metakyi, me kwakwala da kuma wayewa sosai.

Ahnkli ta tako ta iso ta jikin bango inda wani shirgegen wooden structure me kamar wadrob yake ta danna wani Abu ajikinshi tun daga farkon bangon har karshensa ya budu inda sashi shashi na turarruka da takalman designer da jakuna na zamani suke ajiye kowani bangare da irin tasa desgner din.

Yadda taga kayan nata ajerere rass cikin tsafta da tattali Murmushi me sanyi ne ya kufce mata tuna cewa duk wann aikin bana kowa bane face na halisa tun na ranar datazo mata suka kwana agidan tare ta tsaftace mata ko ina ta gyara matashi.

Duk munin zucyarta tanaji aranta kmr Halisa mansa tana daya daga cikin mutane masu matukar muhimmaci acikin rayuwarta wanda bazata taɓa iya hakura dasu ba.

Murmushi ta cigaba da yi tanamai shafa kan kayan ahnkli da dogayen yatsun hannunta dayaji tattalin manicure da zara zaran farcunta na zamani.

As usual Tsabar yawan takalmanta nata takan rasa wannene zata dauka hannu ta zura ta fito da wedges na gucci ta dudduba bai mata ba ta jefar kasa, ta dauki designer heels kala kala yakai biyar duk basu mata ta watsar,ta sake komawa kan flat duk ta jefar kasa. Haka tabar wajen abude ta koma cikin closet dinta, dan madaidaicin dakine shima da reserves na kayayykin sawarta ya ke jere aciki, tana shigowa ciki bata wani bata lokci ba ta jawo wata karamar side bag na fendi me hade da shoes dinsa ta zura akafarta sann ta dawo dakin kallo daya tay ma takalman data watsar akasa ta dauke kanta ta feffetsa turare agugurje snn ta fito.

Tafiya take kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar yawansu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita.

Daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step dede lokcin ranta yake ayyana mata taje ta ta duba halisa hala ta sauko sai kuma wani zucyar ya kaucar mata da tunanin hakan acikin sauri. Gara kawai taje wajen mummy koda ma zata bata wani haske.

Dede ta sauka akan stairs din kenan aka bude kofar main falo, a rigime sosai kamr wata sarauniya ta daga kanta sama domin taga waye yake shigowa.

Aranta Jira take in jasmine ne ta shigo ta sauke mata buhun haushin datakeji akan sabbin halayyar halisa sai kuma akayi rashin sa'a ganin kmar mutane biyune suke tunkarowa.

Take ta dauke wuta ta hade ranta sosai ganin uztaz ne agaba nata sauri sauri dauke da karamin beige trolley box a hannunsa da kuma ledar Abinci daya riko daga fav restaurant din halisa yana sauri. Ganin irin kallon debar albarkn datake masa yasaka ya dan ja yabawa khaleel din hanya ya shige gaba.

Hura hanci take har suka karasota uztaz yana gaisheta ta sharesa dan batace musu uffan ba.

wata sihirtacciyar numfashi khaleel yaja ya kalleta sama da kasa ahnkli snn yace " Madam Where to? Cikin idonsa ta kalla kafin nan Ta dauke kanta batace mai komi dan tasan tafi karfin tagaya masa inda zataje shine kawai baya gajiya da tambayarta kowani lokci.

Agogon hannunta ta kalla sann ta kallesa atakaice, batare da wani kulawa ayaninta ba tace.."Ya bakaje wajen aiki ba?.. Bayabo ba fallasa yace most of my work is here at home now ko kin manta ne??

Wani Abu taji ya tsaya mata a kirji ta juyo ta kalleshi dan sai yanzu ne ma tadada tunawa da cewa shine zai cigaba da kulawa da lfyar kawarta halisa mansa.
Chapter 34 · 0% Book details