← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 267 OF 312

Sashe 267

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya girma ne da tsanar babban yayan nasa dake Robert mansa airforce ne A nigerian airforce commison dake can yankin niger delta state. Jajirtacce ne dan haka mahaifinsu mansa ya dauki son duniya ya dora masa. wata rana sai robert ya dawo gida da wata mata ana ce mata maryam snn yace ma babansu cewa acikin ruwan taku ya sameta sunyi wata biyu acan jejin dayake aiki yana mata jinya snn ya daukota dan tace masa xata biyosa gida.

yace mahaifinsu baiyi wani doguwar bincike da tunani ba ya amshe maryam sabida yarda da dansa roberts dayayi sosai.

Shikuma sai yaji ya tsaneta sabida sallah takei, snn ta samu matsalar mantuwa ta mance daga inda ta fito.

As time goes on shakuwa ta shiga tsakanin robert mansa da maryam, roberts yace lallai xai yi musulunci ya aure maryam, shikuma dayaga hakan sai kishi me tsanani ya kamasa sosai sabida maryam din kyakwar mace ce kuma ya tsani musulunci a rayrsa sosai.

baban su kuwa kai tsaye yace amince ma roberts akan buktansa na yin musulunci snn yace xai musu aure xai basu gida da abunyi dan su ji dadin rayuwarsu. Wnn abun sosai yaci ma michel ransa sabida shi dyake dansan haryanxu baida aikinyi banda shan giya da kwana da mata amma shine har maryam ma saida aka bata aiki duk dama taxo xata musluntar da robert dinsun abanxa.

haka yay dakon bakin ciki me tsanani, sai ranar da roberts ya tafi aiki acn asaman ruwa shine yaje shikuma yasha giya yaxo xai raping din maryam sabida kishi dan ya lalata musu komi.

A daren ranan babansu mansa saiya kamashi, ya daureshi, ya masa dukan mutuwa snn ya koreshi agidan. Ya tafi da tsananin tsana da jin haushin su gabaki daya mama G ce ta basa mafaka.

Robert baiji dadin haka ba duk da yasha wahalar wajen son ya sasantasu da baban nasu amma ina michel kullum hawa yake yana cewa xai dauki fansa wata rana mama g tana xugashu sosai.

Bayan auren roberts da maryam bada jimawa ba sai baban nasu mansa yaxo rasu. Daga nan rikicin rabon gado ya fara. Akwai wani filin babansu da michel din ya saka arai amma sai ya samu an rubuta sunan roberts akai..duk rikici haka alkalai sukace masa yayy hakuri kyauta babansu ya bawa roberts din tun yana raye dan yayy noma wata rana

Yana kuka me tsuma yace musu akan wann filin shi da hannunsa yakai sunan dan uwansa robert wajen matsafa aka tsafeshi, aka rusa masa rayuwa, ya rasa aikinsa, ya rasa mutuncin sa, ya dawo yana shan giya agari babu kakautawa. Duk aganinsa hakan shine kadai xaiyi ma roberts yaga yahuce takaici.

maryam tayi iyabakin kkrinta but it was hard to cope dake tun tana da cikin halisa abun ya fara masa snn duk wanda yaxo ya tanbaye michel cewa yake dan uwansan krista ne.

garin neman ma robert magani kaf kudadensu ya kare itama maryam din bai kyaleta ba saida ya saka aka koreta a aikin datakeyi she had to rely on menial jobs to sustain her husband and her doter...babu wani labarin wahalar da ya basu aryuwa da bai amayoba yau din ba.

Yace tsafin ma kashi kashii yake musu har na gushewar hankli yayi ma roberts yamaida shi tamkar mahaukci amma dake maryam din natare dashi tana masa adduoi yasaka mutane basu gane hakan sosai ba wata rana har ake masa kallon me hankli me nitsuwa ba a san tabon hankli yake fama dashi ba.

yace musu Halisa was his biggest and magical lulluby dan kuwa roberts yanasonta fiye da komi dayaso arayuwrsa duk yanayin dayake ciki baitaba bari yarsa ta gansa aciki ba saidan ta kalleshi a sace.

Yace Duk duhun sihirin da sukeyi akansa karfin adduan da sukei acan yana rage masa wasu abubuwa sosai.

Acikin tabuwar hanklin nasa haka yake kai yar sa halisa schl kowani rana yakuma xauna agte din ya jirata har sai antasheta su dawo gidan tare.

ganin da yayy yayansa roberts na mutuwar son yarsa halissa yasaka shikuma yaji duk duniya babu abunda ya tsana ma kamar ita.

Bayan mutuwar roberts akayi rikici dashi sosai akan gawarsa,yace sam sai an masa biso irinna nasu na arna..haka suka mata fin karfi suka ci mata mutunci dama gashi bata da kowa .bata iya tuna familynta ba
amma lkcin mutuwar roberts ta samu memory flashes dan tayi yaqi da su har kmar xatayi hauka haka ta xamo amma duk dai saida hakan ya faru.

hakama yaxo mata bayan kwana biyu wai xai amshe gadon dan uwansa da babban filin tunda ai halisa mace ce sai akace musu ai da sunan yarsu halisan ma suka saka abunsu.

Sai kuma Allah yasaka maryam din bata jima ba
She was diagonise with cancer, yace alkcin kowa dayasansu na baqin cikin mutuwar ta amma shi murna yay sabida xata mutu ta barshi da Halisa
suci arxiki cos halisa was just seven alkci bata san komi ba..

tun bayan mutuwarsun Ya daukota ya ajeta Yay karyan ta mutu yana mai kaffa kaffa yana boyeta agidansa daga duk wani abunda xai saka masu neman su susan tana raye. Baima iya gaya musu labarin abunda suka ma halisan ba amma daga yanayin yadda yake summarizing cewa shine ma yasata a addinin christan da irin rayuwar talla da wahalan duniya data taso aciki yasaka mutane dayawa yin kuka awajen.

kamr khaleel kam baima karasa jin saura ba ya fita can waje sabida hawayensa dayake dannewa da karfin sunki tsayawa.

Haka kawun halisan ya dinga kuka yana rokon iyayen maryam yana gaya musu yadda abubuwa suka kasance masa shima, tun bayan mutuwar yarsa grace. Baida wajen kwana sai kabarin robert yana rokon ko roberts xai yafe masa yaga haske a arywansa koda sau daya.

Ya kama kafafunsu yayy birgima ya rike halisa yadinga rokonta yana bata hakuri amma duk wajen babu wanda ya tankashi.

Mahaifin khaleel ne ya breaking silence din tare da musu nasiha me cike da iilimi me kuma shiga jiki wa dukansu da suka fusata suke hawaye awajen.

duk da xuciya yy sanyi Amma bashine ya hana leut abkar yasaka aka kama kawu aka tafi dashi aka kaisa gidan sojojin su nacan somalia dan awatayashi na kwana biyu ba.

Labarin Halisa da iyayenta abune daya kusan girgixa kowa ita kanta Halisa batasan iyayenta musulmai bane saiyau, bata kuma san cewa ashe babanta yayi fama da tabun hankli bama, da xaxxabi me yawa tayi bacci akan cinyar mahaifyar khaleel din dan banda rarrashin ta babu abunda suka kwana yi adakin tare da anties dinta haj maimuna da captain jamila, da kayr da wuya tayi bacci suma sukayi bacci...

Tunda kawun halisa yy confessing nashi part din Basu sake yin wata magana ba har sai washe gari da asubahi da mahaifin maryam din ya sake tarasu duka bayan baban khaleeel yajasu sallahn safiya.

Da tsufar sa yafara basu labarin abunda ya faru har suka rasa maryam
Yace kaf cikin yayansa haj maimuna data kasance babban su itace kadai lawyer amma sauran gabaki dayansu military sukayi kama da ga kan abkar, jamila da kuma ita maryam din

Dake tana da basira yasaka ta xabi ta xamo undercover, toh Allah ya riga ya xuba mata tausai da xafin xuciya. Bata iya jimre ganin xalunci musmmn akan yara kanana da mata.

Duk wani aikin sirri dataje saida ya fayyace musu harda wanda basuyi tsammani ba. Yace musu na karshen kenan taje russia snn taje iraq, ta shiga yakin sirri da masu safaran mata da yara tanamai tona musu asiri ana kamasu. Tunda taci nasara sai ya xamo ana hunting inta sosai har da oganta na kud da kud aka hada baki aka bombing din mafakarsu da wani dan karamin nuclear derteminant dayay pieces da wajen ko kasusuwan sauran sojojin da suke aikin tare ba agani ba daga nan aka bari acewa ta mutu

Masu tatattar sharan wajen haka suka turota tare da Duk reminant na gawawakin snn aka watsarsu acikin atlantc ocean dayabi niger state
Nigeria.

anan ma Wasu masu tattaran datti na ruwa musmmn me tattare da sinadaran nucleur suka sameta suka saida ta ma masu siyan mutane

She later escaped and fall into a nigerian river drainage inda roberts ya ganta ya ceto ranta wata biyu yay yana jinyarta ajejein dake cikin delta coast kafin nan ta farfado suka taho gida.

The cancer she died frm was as a result of sever exposure to radio active elements na bomb blast da kuma dadewar datayi acikin sharan dake tattare da shi.

Yana gama basu labarin ya ciro da wani tsohon letter a aljihunsa, yace musu agarin binciken su suka ji kishin kishin cewa wasu sun rayu They spend many years searching for her duk dama basu san tana rayen ko bata rayen ba

Sunyi amfani da duk wata makafa na sirri da kuma dukiyarsu da ikonsu har saida aka kai wani lkci me tsayi snn suka fara tracing findings dinsu duka har ixuwa kasar nigeria snn suka samo wanda yy matching.

ya kara nuna musu lttern yace musu babu abunda maryam bata gaya musu akan raywr roberts da mahaifinsa mansa da kuma halisa ba, yace musu awajen likitan data ma maryam din jinyan cancern suka samu lettern, dan tace ne abawa yarta halisa inta girma ta karanta tasan da cewa suna da yan uwa awani kasa...

dake tun bayan mutuwar roberts ta fara tuna komi ko ince xallan baqin cikin da suka cusa mata ya sakata yin kunci da tunani me yawan da hartaje ta fara tunowa da nata rayuwar, tayi tunanin ta gudu da halisa su koma gida sede ganin cancer ya cinyeta baxata iya komi ba yasaka ta xauna ta rubuta wasika me tsayi wai koda halisan xata girma taje ta nemesu tunda ita Allah bai qaddara xasu gamu da juna ba.

Yace musu Sunsamo wasikar acikin sauki sabida suna da kafafan bincike masu karfi, amma sai aka kawosu wajen kawun halisa shikuma yace musu ai Halisan ma ta rasu.

Ashe Halisa tana raye basu wani jima da fara xuwa bama ashe ta gudu ta koma lagos shiyasa ko sau daya basu taba tunanin karya aka musu ba...
Chapter 267 · 0% Book details