← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 312

Sashe 211

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da sassafe da kyar suka iya tashi abcci musmmn ma da jasmine tasha kayan maye, se kusan 10 am suka fito daga dakin agaggauce akaje sashen da za'a shirya amarya tare da duka sauran kawaye. Kafin kace Wajajen 2 na yamma an gama shirya amarya da kawayenta. Acikin gidan su jasmine din za'ayi waje tun tuni ya cika da esteemed personalities da celebrities, da kyar Mahaifinsu khaleel ya bar Aliyu yazo bikin dake yau yay tsammanin zai wuce lagos sai kuma aka daga musu tafiyan izuwa washe gari da safe.

Da yamma can khaleel da Aliyun suka shirya cikin attire dinsu snn suka zo, lkcin biki yay biki jasmine was the only doter of her billionare father its almost a big privilaged to be der dan dukkanin mutanen da kasan inba a tv ba ma bazaka taba ganinsu ba suna nan yau kaca kaca a wajen ga celebrites kala kala amarya ta saka kayayyki yakai kala biyar kafin yamma. tun zuwan su khaleel halisa take tare da shi saidai yanxu gabaki daya tunda ya furta mata yana sonta ya lura tafara kin hade ido dashi sosai they love chemistry just took a differnt turn, haka kawai ta dawo tanajin mugun nauyin shi da kunyarsa bakamar da can da bai furta mata komi ba.

Wani abin intayi wani abin har dariya take bashi aransa sai yace kamar ba ita tay kissing dinsa jiya ba, all tru the events tana nan makale a gefensa, bata ko yi rawa ko ta shiga rububin biki ba, she bcme calmer and shy, batason surutu bare yawan shigewa jikin shi data saba yi, Basu rabu da juna ba sai can wajajen daf magrib ta rakasu suka fito har bakin gate they took alot of pictures sunata hira anan amarya jasmine take gaya masa cewa ta canza venue na bridal shower inta izuwa hotel din da suke wato hilton dan haka the party is coming up der later at night tana tsokanarsa cewa zata dawo masa da halisan sa kusa dashi

Haka suka yi sallama suka wuce Da tulin expensive souvernies da aka jibga ma Aliyu har da iphone da cash gifts aciki.Tun a hanya suka tsaya awani babban masallaci sukayi sallahn magrib da isha'i, daga nan sunakan hanyar dawowa khaleel ya ke tambayarsa lkcin da zasu koma lagos aliyu yace masa yana jin da sassafe goben zasu tafi.

Suna isa hotel ya tattata Duka souvenies dinsa ya hada ma aliyun yace masa yaje musu gida dashi, yace masa zasu dawo lagos zuwa jibi tare da halisa dan su shirya yasan zasuje white weding din jasmine din a paris By next week.

Suna isa hotel din Aliyu dake a koshe suke Aliyu bai yi wata wata ba ya hau tattara kayansa komi ya saka musu a jaka, bayan nan yay wanka ya shirya da kananan kaya da wurwuri ya fice a dakin tun kafin baban sa ya dawo daga wajen meeting dinsa dayaje ya zo ya hanashi fita wajen shagali, he is actually enjoying the shows bikin manya ne akwai tarin abubuwan nishadi aciki.

He had to follow stairs danma karsu hadu da baban nasa, dagata dayan bangaren halisa gabaki daya ta rasa gane dalilin dayasa jasmine tasaka akai hidiman can hotel duk dama tasan baban nata yaso ne ayi komi na bikin acikin gida..

No one knew her reason but since she is happy sai kawai aka basar aka hau shiryawa, jasmine was on her phone chatting har suka iso hotel din aka saukesu a suite din dake can sama inda babu hayaniya.

Wajajen karfe 9:pm aka fara hidima sun sako kaya masu kyau na fitan hankali kowaccen su tay kyau Halisa tasaka wani strapless blue gown dogo marar hannu amarya jasmine kuma ta saka wani shiny onion bridal gown da grown dinta for the shower.

Anata shagali waje yay waje, lkcin khaleel baizo wajen ba yana can waje yana waya da mamansa

Karfe sha daya dot mahaifinsu ya dawo a mugun gajiye, Ganin Aliyu baiya dakin kawai saiya tube manyan ka yansa ya barsu akan gado snn yaje yay wanka ya sauya kayan sa izuwa wata brown jallabiya da doguwar wando marar nauyi aciki, yau din wata gari sukaje har kusa da niger state tafiyan kusan awa uku sukayi ga tulin fadakarwan da yaje yay mai shiga jiki wajen taro game da mutuncin ya mace, zina da manyan mutane masu lalata da yara kanana a hotels, a very challenging lectures sabida ana ta kishin kishin cewa acikin su malaman akwai masu irin wann rayuwan a boye yaudin dai bakaramin tambayoyi ya amsa akan stage ba ga yunwa da gajiya da ya kwaso duk sai yaji gabobin jikinsa sun mutu murus.

Yana kammala saka kayan kiran matarsa ya shigo suka yi doguwar waya tanamai kwantar masa da hankli anan ma yakece mata shi bacci kawai yakeji tunda Aliyun na tare da khaleel shizai kwanta kawai, haka suka kare wayar cewa gobe da sassafe zai bi jirgi su taho lagos a jirgin safiya. Bayan hakan texts din da suka shishigo wayarsa tun shekaranjiyan ya hau dubawa, tun ranar da akayi hidiman su khaleel din Dr aseem ya tuttura masa sakonni masu cike da nasiha da baqin cikin yadda haryau ya yada dansa khaleel, yanamai tuna masa mutuwa da kuma halin da yasaka khaleel din aciki. Ajiyan zuciya kawai yay bayan ya karanta sakon bai sake dubawa ba. Aransa bawai baison dansa bane but he has dis deep generational trauma daya debo tun daga wajen baban shi. They love hard and break harder..bazai taba manta irin feeling din dayaji aransa da yan jarida suka yanyane shi a india a lkcin ba. He trust his son, but he most make him pay for that mistake sabida irin yadda shima nashi uban yake hukunta shi kenan inyay wani lefi

bai wani jima ahaka ba yunwa ya fara damunsa, ya dau wayarsa once again ya kira wayar Aliyu yana DND ba'a daga ba, shikuwa aliyun lkcin wayarsa na hannun amarya jasmine sunata tiktok video a hall suna shagali just dat nite social media acct dinsa became a hot cake tuni yabi ya mance da dare yayi.

Bacin rai da yunwa suka hadu suka saka mahaifin nasu tashi ya fito waje domin cin Abinci dan har jiri jiri yakeji yasan bazai iya bacci inbaisaka wani abu acikinsa ba. Lokcin ana neman kusan karfe daya na dare, har ya kamo hanya sai ganan wasu yan mata da shigarsu baida maraba da tsirara su ukunsu kyawawa ga hot body suka zuba mai idanu suna kallonsa tare da masa signal.

Da wani irin sauri ya sauke kansa kasa kirjinsa na bugawa take ya murtuke fuska yana furta Subhannallah suhanllah acikin ransa yana kuma korin sheda a bayyane..

Babu kunya suka taho har gabansa suna masu rausaya jikinsu shuimar cikin su Tace mishi hi handsome.. dayan tace "wow he is hot, and old like a fine wine, sauran yan uwanta suka fashe da dariy, gashi basuyi kama da karuwai ba dei irin yaran masu kudin nan ne lalattu..

Zasu karamai magana da wani irin bacin da kuma sauri ya juya ya koma room dinsa tsabar ransa ya baci jikinsa har bari yake ya dau waya ya kira reception kawai yay ordering abinci..tun zamansa anan yake Allah Allah washe gari yay yabar wann wajen koda reception yazo kawo masa abinci mita kawai yakeyi ya amshi abincin ya zauna ya fara ci kenan ko loma biyar baiyi ba yaji ana kncking a kofarsa duk a tunanin sa ko Aliyu ne ya dawo da kyar da mita ya tashi yaje ya bude kofar kallo na farko yaga mata sun kai biyar agabansa yace subhanallah yana kkrin rufe kofarsa suka wani tunkudu kofar suka shigo Ciki suna masu kewaye shi gashi duk cikin su bamai kayan kirki ajikinta wasu ma nite gown ne tun yana masifa yana tsawa har suka fara bashi tsoro tambayar duniyan yay musu akan meya kawosu amma ina saice masa suke ya musu kyaune..

Haka suka turashi akan gado, yana ji yana gani dan Ruwan shansa suka saka wani abu ajiki suka bashi yasha da alama maganin bacci ne dan haka kafin kace wani abu he passed out compltely baya motsi..

kulle kofar sukaayi ta ciki
Kayansa suka cire suka barsa dagashi sai guntun wandonsa snn suka kwanta half naked agefensa atleaast dat was the job they were paid to do shisa aka offing cctv camera da zai bayyanasu.

2:30pm Aliyu ya bar wajen hidima ya dawo dakinsu domin bacci yazo yaji kofar a kulle gam gam haka yajeshi wajen khaleel da tsoro cike aransa ya kwana acan, khaleel kam kusan kwana sukayi suna waya da halisa, sai kusan asubah snn suka hakura ganin lkcin sallah baifi saura minti goma yasaka yay wanka yay alwala snn ya wuce masjid dake can gaba dasu kadan anan yay raka'atunil fajr dinsa yay yan adduoi kafin nan aka tada jam'in sallah subh. Har 6;30 yana masjid din bai fito ba. 6:am Aliyu ya farka ganin lokci ya tafi sai kawai yay wanka anan din yay sallahn asubahin sa kafin nan ya doso kofar room din baban nasu, yana kan tahowa gabansa ya fadi, ganin wasu kattin maza sun tunkarosa da bakaken kayan special ptf na police ajikinsu sun riko manyan guns suka shiga lifter din daya shiga.

Kirjinshi haka ya dinga bugawa dan daga ganin su yasan kame sukazo wajen gabaki daya yaji ya tsorata yana Allah Allah lifter ya kawosu maraba su rabu, ana sauka a floor dinsa aikuwa yaga sun bangajeshi sun doshi daakin babam nasa straight da mugun gudu yabiyo bayansu jikinsa na rawa rawa.

yanaji yana gani suka saka wani key card suka bude kofar suna shiga yabi bayansu, kan matan sukayi suna tattaba su lkcin kirjin aliyu kamar zai faso waje tsaban bugawa for a moment ya dauka yay batan hanya ne bai tashi razana ba saida caraf idonsa ya gano masa babansa kwance malala ga mata sunfi su uku agefe dashi
Chapter 211 · 0% Book details