← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 312

Sashe 37

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin sauke ajiyar zuciya ta nitsa tace "hmmm Amina nifa bansan yaushene zaki soma jin maganata ba.

Meenal ta juyo acikin kasaita ta kalleta suka hade ido ahnkli tace
"Bby Whats this..jibeki??? maganan tay tana dan dafa Kafadunta ahnkli cikin wata boyayyar siga tanamai kare mata wani irin kallon da ita kanta meenal din bata gane shi ba.

ACikin ynyin dauke kai da rashin fahimta Meenal tace "Mum menene?

..hjy nadia zatay magana cikin katseta meenal ta ji tafara hatsala da irin kallon datake mata.

"mum, pls dont start comparing me with oda kids, kuma ai sallaman nan fa ba dole bane pls dont ask me to greet u okay.

Hajya tay murmushi ganin meenal ta haura sama da masifa cikin kyabe baki tace.
'Ni bance kimin sallama ko ki gaisheni ba..and yes, am talking about ur behvrs...

Meenal ta dada harde fuska.

waime ke faruwane Amina duk kinbi kin lalace kina son kizamar dakanki kamar wacce bata waye ba wann swag din yaran hausawan kuma daga ina kika samoshi? Kallonta ta kuma yi snn Ta cire Spec din idanunta Taja karamin tsaki mtsss albasa batay hannun ruwa ba.

Meenal Ta kalli kanta sama da kasa cikin rashin fahimta zucyarta na kuna dan ta tsani a ahadata da kalmr kauyanci. Atakaice ta kalle mahaifyrtan da kyau batare da ta iya furta komi ba musmmn ganin irin cakarewar da hjy nadiya tay, dan banda kayan data saka, tay kwalliya sosai ta shafa su foundations da eye shadow tamaida kanta zubin yan matan zamani.

Meenal taja numfashi ta ciki "Mummy kifito fili kawai kice min i look ugly.

Hajya ta kyabe baki tay murmushi batace mata komi ba.

Sounding frustrated meenal' tace mumy amma ai Kinsan fa khaleel shine private therapist din halisa. Kuma Suicide is such a Big case, ziriya yake min agidana akanta yanxu. If...

Ayanayin rashin kulawa cikin katseta hjya tace ya isa haka Amina nagaji da jin sunan yarinyar nan a kunnena ke kenan badama ayi wata magana dake sai kin furta halisa halisa halisa halisa...so whats the point in khaleel yana gidan.. saime?

Meenal ta hade rai ciki ciki tace. 'Nothing mum. amma kinsan bazai zuba ido yabarni na fito kamar yadda kika fito haka ba .

Cikin katseta tace kamar ya na fito? a Tsirara nake ne..see ive heard enuf of u meenal. Yanzu lkcina ne na in huta ma raina ko ce miki akyi Lkcin da ubanki yake raye a duniya yabarni ina shan iska haka ne?.. shidin ma ai bakauyene kmr mijin naki... banbamcinsu kawai shine ni nawa mijin yana da dukiya ba kamr naki mijin ba. Babu wan babu tan.

Sosai Meenal taji wann maganar ya cakketa aranta amma batace uffan ba tay shiru.

"Anywys, Am not even talking abt ur Dressing. Yadda kika zo min ne turus babu dan kama aji da shan qamshi, ta duba gefe da gefe cikin sauke muryanta kasa kasa "The richest ppl in lagos might be here you knw..ko ce miki akayi dan kin auri wani matsayacin likita sai maza masu kudin gaske bazasu neme aurenki na basu ke ba..

Cikin katseta meenal tace mummy khaleel ba matsiyaci bane, yana da kudinsa iyayensa suna dashi. Kuma duk familyn sa babu matsiyaci.

Hahahaha Ashsha Amina
Kenan. Yarinya man kaza. See, Ders a great margin btwn being rich and being wealthy.
..Rich ppl count millions but wealth count billions
AMINA u alrdy have millions, why are u so proud of sumone that also have millions????

Meenal ta rasa na cewa tanata kallon bakin hjy nadiya dake juyi sabida tsabar mamakin wann furucin nata Wanda take furtashi cikeda nuna yarda da kanta bako dar dar, idanuwanta kuma a bushe.

'Mumy me kike nufine, na riga na aure khaleel, kuma duk duniya kece kadai kikasan sonshi danakeyi yasaka na auresa badan komi ba. da aurena sai na nemi saurayi anan??cmn mum it doesnt make sense baki taba gayamin irin wann maganar ba dan kinsan ba aji na bane bibiyar maza fa..

Tace 'Eh, Amma ajinki ne ki zauna wani soko yana wanka miki mari duk acikin soyayya ne ko?

Meenal tay rau da idanunta Kai mumy kin dau maganan marin nan da zafi ni wallh harna manta.

Amina stop it. Ya zakice min kin manta da domestic voilence. bayan kin dagamin hanklina dazu a waya kinata kuka wai ya mareki, How dare he. if not bcos i control myself wallh yau da khaleel din nan sai yasan da cewa ni cikakkiyar yar barikice.

Cikin sausauto da murya kasa kasa meenal tace Calm down mumy. Chill, "My Revenge is best served when is chilled. Yanxu de abar wann maganan bari na gaya maki damuwata.

Hajya ta gyara zama tanata kallonta da yanayin takaici.

Cikin sauke ajiyar zucya Tace Mumy i need fast money. Harkan nan dole ta budu bana son sanya
Amma nasan bazaki amince kiminba dan haka na Amince din zamuje mu wajen alfah daga nan But on one condition.

Hajy nadiya ta dau drink dinta ta kurba ahnkli cikin jin sanyin cewar hakan da meenal tay snn tace ena jinki..menene condition din naki.

Bawani abu me yawa bane mummy. Idan munje wajen alfa karki tsoma min baki acikin hidimata pleassse let me handle my own problems by myself.

Hajya tace fine..inde har khaleel zaki kai wajenshi ai bawata matsala awaje na har waje zan iya baku keda alfan ku tattauna.

Murmushi Meenal tay snn ta dauki glass tafara juye drink na margarita aciki sanda ta kusan rabi snn ta kurba kadan tace zamu bukace hakan kuwa.

Daga nan shirune ya dan ratsa tsakinsu kafin hjya ta dubeta tace Toh ita kuma kawar taki kenan zaki zauna da ita agidan ki tareda mijinki har sai ciwon haukar tata ya kare???..

Kafin meenal ta amsa ahnkli Ta dafa kafadun ta tace ke Amina,listen to me, "once a soldier is a soldier..shin kin gane me nake nufi???

Meenal tay murmushi mai sanyi tace mumy kenan kina nufin dan halisa ta taba rayuwar kwana da maza shine ya zamto zatay seducing khaleel agidana suyi karuwanci?...

Rayuwar kwana da maza? Amina kice "karuwanci" cos dats the real word! Hjy nadia ta gaya mata hakan bluntly

Dariya me karfi meenal ta tsuntsire mata dashi cikin wata mahaukaciyar siga me ban haushi..
...mumy bansan mesa lamarin halisa ya zamo miki kamr wuta a harshenki. Cmn, Dats not tru, karuwanci ai da son zuciya akeyinshi..i mean..dat will neva happpen.. halisa bazata taba cin Amanata ba inaga bakisan yadda suka tsane junansu bane da khaleel kamar wuta da auduga..pls der is no an ounce of posiblity na cewa hakan zaima faru a tsakaninsu sabida ynxu hakama halisa wakalan ta sa take yi abunta banajin zata barsa ayi jinyar nan lfiya.

Cikin kyabe baki Hajya nadiya talban tace hmmm once a prostitute dai is a prostitute ni dai shawarata shine kisaka musu ido sosai.

Meenal na dariya sosai tace mum sumtimes ure such a delutionist. Na farko..Halisa dai bazata taba bada jikinta ma wani ɗa namiji ba. Ki duba irin makahuwar soyayyar da sukayi da zach amma harsuka rabu dashi wa'lhi baisan kalar pants inta ba bare kuma mijina khaleel da bakomi tsakaninsu face tsanar juna. Kema fa kinsan Tsanani ne yasaka halisa take da waccan tarihin amma aynzu ko mutuwa ne agabanta bazata taba bawa wani namiji jikinta ba.

Toh naji Amina. Amma kisani wann tsanar dai kece kikayi inventing dinsa atsakaninsu..wata rana zasu gane gaskiya what then..mezai faru?

Cikin sauke ajiyar zucya Meenal tace Babu abunda zai faru mumy kidena wann tunanin sabida i have a full proof plan akan haka inada nawa shirin.

Da mamaki hjya ta kalleta ban fahimceki ba

Mumy..bake kadai bace kike da lissafi okay? Tay rolling idanuwanta cikin tsananin ji da kanta Ahnkli cikin sauke ajiyar zuciya tace Aiba khaleel kadai zan mikashi wa alfa ba harda halisan.

Hjy nadiya tace wow.
Badddd girl..yanxu naji magana. Zaki korata gidan ki ko? U shud do that wallh banasonta agngan dake.

Mumy basai na koreta agidana ba. Inna koreta me zance ma su vicky da hadiza da shema?kowa yasan an ajeta agidana ne badon wai treatemt dinta da khaleel shikadai ba kowa gani yake nima yar uwartace dan haka zan kula da ita.. Kawai kibari.. wann maganan tsakani na da alfa ne snn kawarki bayarbiya me saida yajin cameron din nan tana nan kuwa?

Hajya nadia tace Eh tana nan mana amma me zakiyi da cameroon ppr.

Shuumar murmushi meenal din ta saki
Mumy Khaleel ya tsani Abinci me yaji, Halisa kuma ta iya girki. Dats a small angle.

Hajya nadia tace and so, Angle for what??

Tace hmm Mum i need dukkan wasu abubuwan da zasu temake ni wajen karawa zafin gabar dake tsakaninsu kaimi. Sumtin small and mean, abunda bazasu ganeshi da wuri ba, I have to make them hate each oda soo much ata hanyar da bazasu taba tsammani ba. U get?

Bayan dogon lissafi Hjya tace "Yeah i get...amma banda kisan kai meenal kinsan allergies can kill sumties kikaje kika kashe mijinki ke zakiji dashi ahto.

Ahnkli Tace no mum, kisa kuma Kawai dei they wont see me coming ne. Gwara kansu kawai zanyi tay a gidan and am sure its gonnna be fun.

Dariya suka fashe dashi..Cikkn gamsuwa haj nadiya tay murmushi dede nan suka aje hirar suka kama hirar sabuwar business dinsu wanda abun mamakin shine yadda meenal take bukatar samun wasu kudaden ta hanyar gaggawa kuma me yawan gaske duk da arzikin datake dashi.

Badamuwarta aikin bane ita bukatar ta shine ta samu wasu kudaden da ko da ace khaleel yaci sa'a an daukesa a cikin babban contract din larabawan nan ya zamto kafin yay kazamin kudi itadin ma tana da kudin daya doke nashi dan har abada batason ace yafita a komi na duniya so take kawai harsu mutu ya kare rayuwarsa a karkashinta.

Bayan sun gama hirar sirrin su anan private lounge daga bisani suka koma beach side suka zauna da ice creams a hannunsu suna enjoying din skyline view na ocean suna hirarrkin duniya cikin nishadi da jin dadi.

******************

Dagata dayan bangaren hasken ranar daya huda windon dakin ya saka Vicky tabude lumsashun idanunta tana baza sassnyr murmushi mai tsayawa arai da sanin cewa yau wata rana ce.
Chapter 37 · 0% Book details