← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 312

Sashe 224

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da nemansa tsokana tace "when shud we move..ko zaka kaini can eifel tower city of love ne insha shagalina in dauki hotona tunda budurwarkan ma ta tafi.

tsiririn tsaki yaja yace eif..wa? dawa kikeyi, nay miki kama da saurayinki me katon cikin nan ne kome.

baki bude maryam take harararsa ta takuna fuska kamr zata fashe
Karka sake cemasa me katon ciki, wai daga kaji baba yana fadin abu shine kaima dan rainin hankli zaka kama kana gayamin mind urself oo.

yace..To karya aka miki ne? ke ki auri saurayi kinje zaki aure tsoho sai mutum yarasa da wata kalma zai gaisheshi agaban baba..

dariya maryam ta fashe dashi tace eh din,.kuma ai yayin da akeyi kenan, ko bakaga jasmine bane, itama halisar naga wani abokin ango tsoho tun jiya idonsa yake kanta bakagansa bane Ga kudi ga katon timbi..

Cikin katseta yace "uhum ta kulashi ko bata kulashi ba?.. Dariya tafaray yo ina zan sani sarkin kishi bayan kowani lkci kuna waya kuna chting kahana ta shan iska

girarsa na sama a dage yace toh ya akayi da ni ke kuma dariyar ya isa haka muguwa kawai memekon kina kulamin da ita awajen kinzo kinaban labarin masu kallonta toh sunanta ma ya fita abakinki kinji ko..

ta dinga harararsa tana dariya.

jakan kayansa ya jawo "ni wallh daukawa ma nayi harkin gama kwashe tsummokaranki' C'mon get ready mu wuce akwai fa inda zamu. Tace me zamu jira anan din dama
Ni kayana a hade yake kaine dai kake rayuwarka a lalace kome sai halisa tazo tayi...

ahnkli yace zan miki rashin mutunci mimi kefa kin tsani kiga ana kulani..halisa is not like u Kawai she is already use to cleaning up ne amma da bazan barta ta yi min komi ba.

Cikin kyabe baki maryam tace Amma dai in akayi auren nan zaka daukar mata masu aikin gida ko..dan ga hidimar office ga hidimar miji ga gida abun zai mata over.

murmushi yay yana kan kulle zip din troley dinsa cikin kyabe baki yace "albishirinki Aikin miji kawai zatay agidana sauran duk zan san yadda zanyi ana tayata dasu Karki daukeni marar hankli.

Dariya tay tace toh Allah ya kaimu lokacin..Yace Ameen. Daga nan suka fara magana akan inda zasu je next, khaleel ya mata bayanin abunda yake son ta tayashi ya faray da makudan kudadenshi na project participation grant da suka shigo last week wanda ko mahaifyrsa bai fada mata ba bare kuma halisa dan da Akwai personal abubuwan dayake son yay ma iyayensan firstly witout making noise abt it.

bakaramin dadi abun ya ma maryam ba, ..nan ta miƙe taje room dinta ta shirya kanta tsaf snn tazo sukayi breakfast bayan nan suka wuce airport suka booking next available ticket to india.

Sati daya kawai zasuyi anan india, dan he had already been working on it secrtly. Har ma anyi nisa sosai, wasu ma angama dubawa kawai zaiyi.

Tun yana gida yaketa tunanin zagowa ta nan insun zo bikin jasmine domin ya duba yadda abubuwan suke tafiya anan, har cikin ransa yaso ace tare da halisa zasu zo indian domin yakaita har schl dinsu amma Allah baiyi ba.

Frm paris to india flight dinsu ya taho direct aka saukesu a birnin mumbai
Suka kama hanya a jirhin kasa izuwa town din da schl din nasu yake dan baida nisa da babban pharmaceutical store na babanshi,. Sai kusan yamma suka isa basu kai ga zuwa koina ba suka samu masauki washe gari da safe bayan sun shirya sukaje Location na babban pharmacy din
already ya biya kudi an sake renovating dinsa an kwaskwaremeshi da abubuwa na zamani wajen yay kyau yana mai mugun dauke idanun mutane sabida gyaran da aka masa da wall din glasses kamr wani gucci store. Maryam was so excited to see evrything duk basu san yanata aikata wann abun ba a shiru shikade ba, she cudnt hold it, ta yi videos tay hotona ta tura ma mum dinsu a watsap
lkcin Sassafe ne suna cin breakfast da mijinta ta bude ta gani at first bata ma gane wajen ba saida ta karanta sakon maryam taga it was meant to suprise them

rgwababben Murmushi tay me tafe da hawaye tunda ta fara hamdala da kabbara saida mijin nata ya damu ya bar cin abincin dayakey ya dawo kanta ya amshi wayar a hannunta yana saka idonsa akai shima ya tsandare kallon waje yake da mamaki, ita kuma tana masa bayanin abunda maryam tace mata.

Tana murmushi tana hawaye at same time tanacewa Abban ibrahim kagani fa yaron nan baice mana komi ba sai Dai kawai mugani?? ka ga wajen nan kamr ba wajen ba..wayyo Allah na tafadi hakan da tsananin murna dan saida taji abincin dakw gaban tan ya isheta. This place is going to go wild with foreing marketers.

Sunan baban nasu ne akai yanxu bana khaleel ba, haka aka dora katon brass lighining deck an rubuta the Hasheem's pharmeceuticals store india.

Shikuwa tunda ya rike wayar bey motsi ba dan Wani irin sanyi ne ya tsandarar dashi, da can har an fara masa tunanin ya saida wajen but he cudnt do it sabida initially ma dansa ibrahim ya siya bama kansa ba, yasan tunda har khaleel ya gyara wajen hala ya sake registring wajen ne da dual nationality tare da medical licence dinsa yanxu kusan dolene gwamnatin india ta basu full proof right na enjoying duka right din yin business dinsu kamr yan kasa. tun bayan Abunda ya faru dashi a hotel bai sake yin farin ciki da dariya me yawa ba sai yau shikam bai iya hakuri ba atake ya kirasu ya sassaku musu albarka

Khaleel ya gayamai cewa zasuyo sati daya anan din dan sai sun gama da registeration da sauran manyan kamfanin da suke producing original drugs sann zasu fara kawo kayansu phamarcy din..

Babban yaron Dr aseem anan shine zaiyi ma new wokers dinsu inteview cos the store is going to run like a huge medical super market duk wani abu daya kunshi asibiti zasu siyar har surgical equipments da enginan aiki, snn kayansu direct daga kanfani zaina zuwa

Babansa ya saka mai albarka ya masa addoi masu yawa da suka so suka sakashi hawaye.

Wani irin karin kwanciyar haklin da nitsuwa ya dada ji ajikinshi cos there is nothing more fullfilling kamar kaga iyayenka suna cikin halin tsananin farinciki sabida kai ranar har jin kansa yake kamar wani sabon mutum.

Daga nan agidan Dr Aseem suka wuni masa tare da familynsa babu kalar karamcin da basu gani ba, And he just missed halisa more and more Dan tun zuwan su dr aseem da matarsa suketa tambyarsa ita.

maryam tasha mamaki dataga Shima Dr Aseem din bai bi bayan halisa ba
Kusan yanayin tunanin su iri dayane da khaleel yace masa he shud neva give up on her one bit musmn ma akan abunda zai cutar dasu dukansu su biyu.

Haka rayuwa ta fara musu cikin neman nitsuwa da samun albarka da kuma gwagwarmayan rayuwa.

Dr Aseem ya taimaka masa sosai wajen tada darajar pharmacy duk da ma Babansa ya kasa kiranshi suyi magana amma yasani sarai dan baison suyi maganan a wayane cos he had alot to say to him. Shima doc Aseem din bai damu ba yafi koya jin sanyi aransa da khaleel ya samu albarkan mahaifinsa da kuma cikakken nitsuwa.

Zamansu a india gabaki daya aikin tada wajen kawai sukayi ana saura kwana uku su wuce aka kammala interview din workers nan aka jejjera equipments da drugs aka shirya komi da komi duk abunda sukayi sai sun tura ma iyayen nasu sun gani daga can, Ranar da suke kkrin bude wajen da sassafe a abazata sai ga nan iyayen nasu sun diro musu a surprise tare da Aliyu da siyama haka sukayi karamin lunch tare da familyn Dr aseem ya babbashi hakuri ya masa godiya, dr Aseem kuwa ya fahince shi sosai snn yaji dadin irin karramasa dayay da yazo har gidansa ya nemi gafararsa akan maganan khaleel.

bayan nan suka je aka bude waje tare sauran manyan mutanen da baban khaleel din yasani a india musamn ma wanda suka masa mummunan gori akan abunda ya faru da dansa dan su gan susha kunya.

Ranar He was all over his son sounding very proud Of him tun tuni ya maida masa duk abunda ya bashi adacan wani bin Khaleel har gani yake kamr mafarki yakeyi.

kwana biyu bai kira halisa ba saidai suyita exchanging tex message dats funny, emotional and witty, Datace mai ta kwashe kayanta agidan sa ta koma nata gidan har dan karamin ciwon kai saida yayi aranar.

he doenst knw if he cud bear live in dat house witou her anymore har saida yaga Aliyu maryam da mum dinsa suna yawan waya da ita snn yagane sun riga sun gaya mata komi harma ta kira baban nashi ta masa congrats.

karin kwanansu biyu a india kafin nan suka koma gida nigeria da cewar Aliyu zaina zagowa kowani wata yana duba wajen duk dama babban yaron dr Aseem is managing it for now dake shi anan indian yake da aure shima din lecturer ne a university dinsu na dacan.

Ata bangaren meenal in mun koma baya zaka samu Hatta irish din da mumyntan ta aiko mata bata iya sakawa acikinta ba sabida tsabar kishi da tunanin cewa khaleel ma can abuja yana wasa da kudinsa ma yan mata dansu subashi jikinsu ya rage zafi dan Inba haka ba batasan a ina zaina sauke jarabarsa ba.

ranar Haka taci zama a asibitin tana jiran ganin mumynta amma sai bata dawo ba sai can wajen yamma lis haka sukazo suka sake haurawa juna

Jikinta duk babu dadi haka suka koma gida aranar taki cin komi ta daga hanklinta lallai saitaje abuja ta dubo khaleel acan. Gashi ta kashe wayarta tun last week tana tsoron ganin kiran masu binta bashi babu yadda za'ayi tay wani kwararren bincike akansa ko ta kirasa da lambarta.

hjya nadiya Kuwa haka tayi kememe taki sam ta taimaka mata akan hakan ganin ba wani lafya jikinta ke dashi ba.
Chapter 224 · 0% Book details