← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 298 OF 312

Sashe 298

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayayin da victoria ta samu rayuwar da batay tsamanin samu agidan miji ba, her mother inlaw itake take komi akan cikin dake jikinta suna bata kulawa sosai duk dama bakaramin shan duniyancin soyayyya suke zubawa da kayden dinta ba. Dan tasu salon soyayyar sam baisan kunya ko sanyi ba... Gabaki daya ta lalata yaron da salo salo na rayuwr aure and the most beutiful thing abt thier life is yadda take ganin ya cimma burin rayuwansa komi nashi takan tsaya masa akai kama daga karatu aiki meetings da duk wasu hidima na iyaye wanda yasaka duk masu tunanin danta girmesa cutarshi kawai zatay suka fara sauya tunani

Dan wasu abubuwan ma ita take encouraging dinsa akai kamar harkan karatunsa wanda dama shi ba wani shaawar yin karatu me yawa yakeyi ba duk da Allah ya zuba mai brain da ilimi amma koda vicky ta sakamai ido akai ya zamo yafara maida hankali, they are busy planing to move into United state bayan sun haihu inda zata rakashi su zauna anaan har sai yayi masters tare da phd dinsa duka a masassuchets institute of technology. Her life is complted and perfect amma bata taba manta Allah aciki ba. Each time ta tuna rayuwata da femiy sai ta zuba knee dinta akasa tay addua ta kuma kara gode ma Allah daya sauya mata rayuwatta da mafi alheri daya bata soyayyar kayden da kuma ahalinsa.

Bangaren hadiza kuwa harkan siyasan mijinta suka fara sakowa agaba dan haka ganin da jinta ya sama ba kasafaai ba amma time to time haka they keep in touch kuma haryau suna magana chats privately kowa ya share grp dinsu bamai lekewa tun Lokacin aauren halisa bayan da shema ta sauya ma grp
din suna ya dawo.. "CHEATERS CLUB"
babu wacce tay left amma babu me lekawa
Face meenal da in zaman damuwa ya isheta take scrolling taga chat dinsu, cemata da halisa taay su vicky da hadiza sun san komi ya mugun daga mata hankli
Sumtomes she just scroll down to re read their chats just to make sure of all the subtle banters dan saiyanxu ne take dada fahimtr wasu bakaken magngnn da vicky take yawan watsa mata acikin wasa .

Tunda sukayi musayar yawu da khaleel bata sake fitowa ba she just tot abt how she can make it dan ita batasan me ake kira da rusuna ba

She still belive she can do sumting amma wann karon tunda kowa ya gane salon maybe she need to change her salo to sumtin they dont knw abt her.

Haka kawai ta qudira aranta cewa zata creating makanta daama na biyu ko Allah ya bata ko bai bata ba, ita de kawai dolene ta zauna a matsayin matar khaleel and later make him regret all wat he is doing to her now..kuma in sha Allah tana da yaqinin saka halisa ajikin halin kuncin datakeciki yanxu
Inhar Allah bai bata ikon ta kasheta ba.

Yauma wanka tay ta fito tana dube dube.

Lokacin halisa ta fito sassafe ta shiga kitchen tana dafe noodles ba abunda ke zagaye mind dinta fiye da magnganun fadila akan meenal dan fadila tana kan bincke net babu dare babu rana and by now she have a big lead akan mutanen da meenal tay aikin hatsarin nan dasu jira kawai take a ɗana musu wata babban tarko akamosu dan duk wani karyan meenal din ya kare.

Halisa tana son taga an hukunta meenal kodan abunda tama uztaz amma akasar ranta takanji wani nauyi da tausayinta na damunta arantan sosai cos she knw how it feels to losse sumone u love and to wacht him love another woman agaban idonka is another form of torture

sede Kuma in ta tuna yadda iyalan uztaz suma zasuji aransu sai taji gabaki daya ranta ya hargitse da zafi.

Alot of things are going tru her mind, taki ma ta gaya ma khaleel batun abunda fadila ta samo musu akan wayancn mutanen sabida batason yay wani abu akai tunda suna kan gudanar da wasu binckensu da kawunta atacan duky tarasa mesa khaleel baison ko kadan a sasauta ma lamarin meenal duk irin zafin zamansu da meenal datakeji baikai wanda khaleel yakeji aransa ba kawai dannewa yake dan kotu ta bashi oder kuma mahaifinsa yace masa ya nitsu da bazai taba bari ta zauna masa a gida ba batare da ya saketa ba.

Now dat he is soo Adicted to her and the unborn child ta kowani fanni duk wanda yake kallon rayuwr su dole ne ya fahimce cewa bazai ma iya kallon meenal a matsayin mace a idonsa ba koda bata aikata komi na Dan har Wani tausayin meenal din halisa takeji data dorashi aranta.

Tana kan juya indomie taji an dafata ahnkli ta juyo suna hade ido da meenal ta hade rai ta rufe tukunyar snn ta juyo tana kallonta batace mata uffan ba

Fuska ba yabo babu fallasa meenal tace Halisa i want to talk to u

Halisa tace uhum ure already talking menene

Nannauyar ajiyar zuciya ne ya kufce mata tace
"You knw what i did..
U knw why i did it.. kar mu cutar dakankanmu
Halisa kibarmin mijina
Please i dont need ur money, i dont need anything frm u, just khaleel is enuf kibar min shi.. kimin wann halaccin inde kinason insan kin biyani abunda na miki abaya pls i am asking for my husband in return.

Da tsantsan mamaki halisa ta kalle meenal dale hawaye tana maganan cikin tsumayi da makalkale wuya kamar wata yar marainiya.

cikin kyabe baki Halisa tace Amina kenan aini ban rike miki mijinki ba bare kice in sake miki shi. Ko bakiji bane? ive already told u saida mijin naki yasha jira kafin na amsa batun aurensa and is all bcos i was busy considering ur feelings
Duk wnn jinkirin hallacine dana maki despite ke dakika tashi wargaza tawa soyayyar baki damu da abunda zanji ba...da khaleel yave zai aureni saida nayi tunaninki amina wnn halacci ne namiki wanda kudi bazai iya sayanshi ba. But i still gave u the money cos i knw u need it.

Cikin lumsshe ido da budewa meenal tace
Halisa please, wallh zan iya mutuwa in khaleel ya rabi dani..inason shi kinfi kowa sanin yadda nake son shi..now dat u took him away frm me i donty knw what i am feeling dan Allah kitaimakeni ki rabu dashi.

halisa tace Aa..Amina nazaki sakani agaba kina min kuka ba Shi zakije ki sama ki gaya mai ya rabu dani ya sakeni, ya zauna dake saboda kinasonshi ke kadai..ure not even ashame of how selfish ure..haryanxu kanki kawai kika sani baki tunanin shi ya zaiyi da nashi soyayyar aransa..amina yadda kikeji kinasonshi zaki iya mutuwa akansa haka shima yakeji yanasona koda yau na barki tare dashi babu abunda zai zanca tsakaninku Amina

cikin kuka sosai Tace aa wallh akwai abunda zai canza halisa..nasn baya kaunata ya aureni amma ai yabani hakiina da damata na zamowa mace a gidansa i just need that kind of chance again to make it ryt. I want my husband back and nothing else..

murmushi me tattare da takaici ya kufce ma halisa Ahnkli ta kalle idon meenal din tace so inkin samu 2nd chance wajen khaleel kema kinsanig baisonki amma ace yay hakuri ya baki daman zama matarsa, then what about me and him? shin Zaki iya bashi dama shima ya zauna tare da wacce yake so ko kawai kanki kika sani??

Tana shirin budan baki cikin katseta halisa tace kafin kibada amsar da bazaki iya cikashi ba kisani amina Kowani dan Adam yana da son kansa
..ure fighting for who uY love babu wanda ya hanaki, Amma fa bashine zai saka kowa ma ya xuba ido ya kasa figthing akan abunda ransa ya keso ba..we all selfish wen it come to sumting we love.

Shawara daya zan baki a matsayina na kishiyarki
U want a 2nd chance akan mijinki kiy kkri ki saka gaskiya acikin lamuranki snn ki cire son zuciya kiy adalci makanki
da masoyin naki..inhar kikayi hakan babu Abunda Allah arrahmanu bazai miki ba..dan bani abunda yafi karfin Allah.

dede nan Meenal ta share hawayenta tace
Shikenan dama ni sauki na zo in nema mana a wajenki dan ni nasan inkika tafi kika barmin shi komi zai dawo mana dede tsakanina dashi khaleel was not this hard hearted saida ya gamu dake, yana sona yana kulawa dani kece kika shiga tsakanin mu amma tunda kince haka kowa tashi ta ficce shi...

Halisa tace thats cool with me...as long as we all in agreement.

Cikin jan zuciya me karsashi Meenal tace saura abu daya.

Cikin rolling mata idanu Halisan tace menene kuma wann hajya??

Dan shiru tay kafin nan tace "inda gaske kike akan maganan dakike fada yanxu inason ki masa magana akaina
Ki gaya masa ni matarsa ce haryanzu inada hakki akansa..i need him close to me. I wanna feel him i missed him..hakkina nake so yabani nima ai macece kuma abunda kike takama dashi in nima inadashi pls do tell him dat.

Dariya halisa tay kamar abun bai cakketa aranta ba ahnkli tace why dont u go and tell him by ur self naga ai kece ma uwargidansa ko?

kai tsaye meenal tace eh gara da kika san da haka, nine uwargida sarautar mata, nine na bare shi a leda..na gaya maki ne kawai saboda kin makallaleshi kin nuna masa cewa ke kadaice mace agidan nan...halisa i knw u just want to have him all to urself Wnn fa ba soyayya kike nuna masa ba dan wuta zaki kaisa sabida rashin adalcin dakike saka shi yanamin yau fiye da sati kenan ina gidan nan amma ai ko sau daya baki barsa ya shiga dakina ba.

halisa tay kwafa sigar maidata shashasha snn tace Toh duk dai wann tsakanin ku ne hjya babba inbezo ba ke meya hanaki biyosa dakin nawa ki jawosa da karfin tsiya tunda kin isa kin cika uwargida sarautary mahaukata? Kidena cika min baki banason na gaya maki maganam da harki mutu bazai dena miki ciwo ba..gara ma kije ki tambayesa meyasa bai shiga ba bani zaki gayawa wann maganan ba dan nidake ba abu daya bane..akarkshinsa nake ke kuma a saman sa kikejin kanki dan haka kurata ta chan.
Chapter 298 · 0% Book details