← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 309 OF 312

Sashe 309

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ya mata komi a dakin ya gyarata tsafff tsaff ita da babies din ya mata asalin wankan ruwan zafi ya tabbata tasa ruwan shayi acikinta me kauri ta samu bacci tare da babies dinsu, macen zak zak kamannin khaleel, namijin kuma sosai yake kama da mamansa.

Khaleel almost cudnt take his eyes off her and the kids dan bazai iya misalta farincikin da ke yawo aransa a wann daren ba dan Saida yay nafila yay godiya yay addua ma future din yaran da zuriarsa gabaki daya. Ko baci baijin a idanunsa Haka ya wanke kayan jinin ya kimtsa komi har asubahi tazo ta sameshi. Fitarsa salla duk yana jin kunya sai yake gayawa Aliyu, Aliu ya gaya ma babansa da mamansa...

Da hijabin datay sallah suka dunguma ita da aliyu suka je dakin murna har baki, Kowa na shan mamaki ganin khaleel ya gama komi. mhfyrs ta dau yaran tana hawaye ta rungemesu ajikinta snn ta fito waje ma mahaifinsa dasu dake shi bai shiga room din ba abakin kofa ya tsaya yanata hamdullhi hannun sa harna bari bari ya amshe yaran yanata kallonsu with immense grandfather love and proudess yanata musu addua rana ce garesu da bazasu iya mancewa ba dan krfe shida na safe nayi aka kirasu daga meduguri cewa maryam ma ta haife mace da namiji.

Satin gabaki daya shagalin shirin suna aka dingayi, baki daga ko ina suka zozzo anty jamila kanwar mahaifyar halisa itace ta zo da wuri tun awashe garin haihuwa..

Irin gatan da halisa ta gani a satin bazai misaltu ba Sumtimes ma sai tay dagaske take iya daukar babies dinta sabida kowa yanason ya dauka ya rike.

As usual wann karon hidimar nasu uztax ne dan shine ya dauki jigila akan komi dashi akaje meduguri akayi bidirIn suna bayan suna da kwana biyar duka suka dawo lagos kowa ya kama abunda ke gabansa masu komawa somalia ma suka tafi

Babban acikin causin dinsu halisa na somalia wato nana ai da anty salma sune suka zauna sukay sati biyu har aka gama halisa wankan jego. Anty salma ta sake hadeta tay mata shiri sosai na tarban miji dake ma asalin jegon dacan aka mata ba irinna zamani ba. They make sure she must eat, kuma abinci na musmmn suke mata,dagwalan ppersoup na kajin gida, kunun daka me yaji da hade haden gyaran ruwan nono, tare da ganda daya dahu yaji romo me masifar dadi da sinadari. Banda kana kanan dabaru da ake mata na tari sanyi daga shigewa jikinta da kuma ingantaccen wankan ruwan dumi.

Komi game da kula da yaran ana dora bisa hanya bare ma mahaifyr khaleel bata wani kyaleta tasha wahala da yaran sosai.. bayan wucewar su anty salma, mahaifin khaleel yace musu suma su tattara su koma asalin gidansa dake nan lagos din..LITTAFIN NA NA KUDI NE 08060712446 TO PAY

COMPLETE NOVEL WAIT LIST GROP IS OPEN

*_"MUFTARIQ"_*
BY SURAYYAHMS.
®Edited seriies.

_labarin wata tsaftacciyar Soyayya hade da rayuwar wasu yan mata kyawawa guda biyu da suka kasance yan uwan juna ɗaya ta kasance tamkar "hagu" daya ta kasance 'dama" wajen raayi da yanayin rayuwa, sun ci karo a acikin Duniyar_ _kokonto tare da banbance kiyayyar talauci da soyayyar gaskiya akan namiji guda ko ya abun zai kasance oho??_

*the book is ready* amma Will be out only...on *30th August*
Wanda suka booking dawuri will get discount on the document...

*Buy now sai asaka a wait list group..yana sauka a tura maka documents naka kasha karatu🤧*

Labari ne me cike da darusan rayuwa...

Dont miss it❤️❤️#SURAYYAHMS
#2024
#CHEATERS CLUB
#08060712446
#PAID BOOK
#ENDPAGE

yau ne zasu tare a gidansu dake lagos dan haka mahaifyar khaleel ta shirya jariran tsaf a dakinta takimtsa su tun da kafin yamma ya rufa aka killace tsaf da kya da kuma adduoi, sai can Wajajen bayan isha'i Halisa ta kammala shiryawa wani sssnyr kwalliya nude make up tay akan fuskanta ta fito sanye da wata arniyar tsadaddiyar ceibo lace olive colour me touches din gold ajiki dinkin yay mata cass sophiscated peplum blouse and strait skirt na manyan mata ta bi ta yafa babban golden colour mayafinta jakarta da takalminta na amina muadi to march koinanta na fidda qamshi kanta akasa ta karasa babban falon mahaifin nasu bata iya hade ido da kowa ba dan bakaramin kyau tay ba. Da sanyin murya tai sallama aka amsa,lkcin kusan kowa ya hallara, iyayen khaleel nazaune akan doguwar kujera tare da jikokinsu a hannu, A kusa daf da inda khaleel yake halisa ta dan zauna akasa ganin inda yake satar kallonta shidinma yay kyau dan kuwa farar yadi marar nauyi medan sharara ya saka ajikinshi goggiya kan nan nashi ya sha hula wanda ta masa kyau sosai.

Gyaran murya mahaifin nasa yay yafara magana tare da fadakar dasu akan lamarin jarabawa da kuma rayuwar gabaki daya, dan tun bayan rabuwarsu da meenal bai taba magana akan su saiyau daya tarasu wani sassnyar nasiha me shiga jiki ya musu me nauyi akan tarbiyan yayan su, ya kuma ja kunnensu akan irin soyayyar da zasu nuna musu, cewarsa meenal ma soyayyar uwace ya fara lalata mata rayuwarta gabaki daya ba talauci ko kiyayya ko maraici ba.

Sabida soyayyan iyayen yakan kasu kashi biyu ne, akwai soyayya me tsafta wanda iyaye zasu rufe idonsu subi da yaransu akan daidai koda duniya zata nunasusda yatsa snn akwai soyayya gurbarciya da wasu iyayen zasu bawa yayansu ta hanyar nuna musu duniya a sigar da hajya nadiya ta nuna ma meenal. Ginshikin kowani alumma tagari ingantacen uwa ta gari ce me tarbiya da ilimi dan haka, ya gargadesu da subawa yayansu tarbiya da ilimin addini ingantacen dana bokon shima ingantace sabida musulunci ya bamu dama munemi ilimi komin yawansa komin nisan sa inde me amfani ne kuma me albarka ce. Shawararri game da rayuwa tare da zaman aure duk sun sake nanata musu.

Musammn ma yanayin zaman yau da gobe,yace musu akwai gajiya akwai sabani, akwai jarabawa masu yawa da suke tafe acikin rayuwar aure dan haka su shirya na wann lkcin, suyi imani, su rike Allah snn su yawaita yin wa junansu uzuri tare da tuna alherin junansu aduk lkcin da rai ya baci sutuna cewa su ajizai ne dolene akwai yau da gobe acikin aure...

Game da dukiyarsu da zuriarsu yace musu su kasance masu tafiya da halal da kaucewa haram
Sabida samun albarka snn sukasance masu hidima ma addinninsu da da yan uwansu da kuma marayu domin samun wadata da haske...

Bayan nan kowa yay musu fatan alheri cikin godiya, wasa da dariya aka watse a falon, wajajen karfe 8.30pm aka rakosu har haraban gidan tare da twins dinsu ana ce musu _Azrah da Azaad_ kakansu kamar bazata rabu dasu dan bakaramin ji dasu takeyi ba.

Dake suna da child comforter abayn motar haka aka sankaya jariran ajiki suka kwanta damas, khaleel na tuki da hannu daya,dayan hannun shi na rike dana matarsa yana murzawa stirinng ahnkli Babu abunda ke tashi a motar face kira'ar karatun qur'ani.

Ahnkli ya tukosu har suka kawo gidansa daya gina musu na asali ann ikoyi wanda anan ne aka yi jerenta tun shigowarsu suketa kalle kallen kayan da nata iyayen suka mata dan duk gidajen da suke zama aciki bayan aurensu basuga gida wanda aka xuba naira aka kyafeshi da kayan zamani yakai wann din tsaruwa da kyau ba.

Daki biyu ne a gidan dan haka dakinta ta wuce da yaranta ta shayar dasu sukayi bacci snn ta fada wanka ta fito jikinta na zuba uban qamshi still ta kunna kaskon wuta ta zuba wani shuumar turaren sirace da mummyn khaleel din ta bata ta rufa kanta akai hayakin gamshi ya gama kama mata jiki after like 15 minute ta kashe snn tayi yan shafe shafenta agaban madubi ta bude sabbin kayanta dake shake agidan ta ciro wani pure white riga me spagheti hand duk jikinshi net ne me sharara tana zurawa yabi ya tamtame hadadden shape din dirinta barin ma da shayarwan yasaka nononwarta ya kara cikawa tam tam daga ita sai Wann rigar ta fito daga dakin ta shiga kitchen jim kadan ta fito ta haura sama can inda master bedroom dinsu yake..

Around 9:30 khaleel ya shigo neman matarsa ya shigayi har dakinta babu ita banda qamshinta sai kyawawan yaransu dake famar bacci anan ya zauna agefensu yanata kallonsu suna bacci har karfe goma ya cika, Jin shirun yyi yawa yasa ya shiga kirar wayarta a bugun farko ta dauka.

Sassanyar Muryanta ne ya fara dokan kunnenssa sai da yaji faduwn gaba
Tace champ where are you? yace mata yana tare da yaransa tana murmushi me sanyi tace masa yazo dayan dakin ya sameta yanxu.

Aje wayar yayi cike da mamaki ya haura sama a babban master room din gidan ya sameta ta baje kolinta koda suka hade idanunsu waje guda yaga irin shigar dke jikintan saida yaji wani yarrr na bin jikinshi kirjinsa na bugu kamr nunfashinsa zai dauke....

Tin daga kofa inda yake takawa yafara kallon red flakes of rose flowers din dake zube akasa yana takasu ahankli har ya daga ido ya kalle yadda ta barbaje su akan gadonsu dayasha wata arniyar white bedsheet bakaramin kawata gadon roses din sukayi ba...

The entire atmospher of the room is extremely romantic shikasan baisan yana maseifar son suprises ba sai yanxu daya shigo yaga abunda yake gani..

Wani iri dadi da zumudi ya dinga ji aransa yana taka roses din dake zube a kasa yana karasowa.

Akan lallausar turkish mat yaganta tay xaman diris ajikin wann kayan nata me masifar daukar hankli tana dada dada kawata decorated huge huge flickering candles da sukenan red and white kusan guda hudu a asakiyar wani hadadden flower bonquet.

Agabansa kuma madaidicin driping chokolate cake ne tare da wasu irin foreing chesee,Chokolates da mouth watering milk shakes masu topings din red beries.

har Khaleel ya karaso kusa bai daina kallonta ba dan banda qamshin turare da ababen dadin dake wajen ba abunda ya ke tashi, yana matsowa daf ta daga sexy eyes dinta ta kalleshi in a way that almost melt him down.
Chapter 309 · 0% Book details