← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 312

Sashe 124

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta kwaso zallan tsokar kaza ta wanke ta masa kaykkwar hadi ta fere patotoes dan dede da kayan lambu tay rich and courful sauce din ta dashi, saida ya kusa nuna daf snn ta juye sardines isasshe aciki ta juyasu tare sunayi ta sauke tay filling dinsu cikin samosa wrap din inda kowani bangare ka gantsa sai ka tabo kayan dadin dake ciki snn ta jejjerasu a wajen gasawa
bayan sun nuna sunyi kyan gani nn ta cire ta jerasu a foil ta rufe half way.

Brown spageti jollof ta shirya da meat balls dan sauran sauce din samosa din daya rage ta yayyafasu akai Sukayi kyau, wani irin qamshi da armshi abincin nata yayi.

Mashi kawai tayiwa ginger juice one cup ta aje masa a frigde sabida condition din sanyi da datake yake shiga ciki.

mint, citta, kanunfari, da cinnamon ta dora wuta ya tafasa Sann ta zuba masa condensed milk aciki ta dan barsu for few mint tabar sa a low sugar yanadan nuna ta juye a mini tea flask.

bayan ta kammala komi Nata kawai ta deba ta deba ma me gadinsu spagh da samosa da tea din sai ta kirashi tazo ya karba.

Dake haryau bata taba bawa khaleel abincinta ba inta gama sede tabar masa anan yazo ya deba makansa a kitchen din kullum, shikuma kamr maye baidamu ba inde zata bar masa toh sai yaci. Tun kafin farkon azumi har sukazo suka saba da hakan yana dawowa daga aiki straight zaije kitchen din ya bude pot ya duba me ta dafa, in ansha ruwa kuma nan zai kwashe abincin yaci.

Wann karon Bakaramin mamaki mahaifyarsa tasha dataga wai har azumi ya raba tsakiya khaleel be nemeta awaya yace mata ta aiko masa abincin shan ruwa ba. dan Sun riga sunsan meenal bata fiye yin axumi a gidanta ba snn babu axumin da khaleel baiya shan baqar wuya da raywrsa gashi be iya juriyar yunwa sosai ba kuma bai taso da son cin abincin waje ba.

Kusan kullum sai ta tambaye kaninshi Aliyu ko zaije gidan ya dubo mata lfyar khaleel amma dake bason walakan cin meenal Aliyun yake ba yasa baiya zuwa aikanta saidai yay mata wala wala.

Halisa na shiga room dinta ta aje abincin akan table snn ta cire kayanta ta fada wanka dake ita qamshin spices na yawan hawa mata kai kusan dolene sai ta dan yi relaxing snn take iya cin abincinta cikin kwancyar hankli.

yaune rana ta karshe da khaleel zaiyi presentation
dinsa saidai wanda aka kawo domin suyi supervising dinsa na yau din bakaramin gigita masa hanklinsa suka so suyi ba.

dan A tashi daya ma zaka dauka ko sun tsaneshi ne dan Tsabar yadda suka tsaurara masa komi, kowa yay nashi cikin sauki amma bandashi wani irin chalengin dinsa sukeyi kamar wanda ya kawo kansa gaban kotu.

Daga shi har ogan nasa basu sani ba ashe Dr khalid da ogansa dr emeka har sunkulla markici sunkai suka dq gulmansa can headqtr na board cewar ai ogansa dr aseem yana bashi satar amsa,wasu ma zargi suke na cewa bashine yake aikin ba masa akeyi dan kawai a dorashi acikin aikin larabawan nan.

Hakan ya saka suka sako khaleel a gaba saida yay defending every bit of what he did in his paper works, gashi sunayi suna recording din komi duk sun dauka zafin da suka sakamai zai tsoratashi ya fadi gaskiya..

Hatta hankln secret agent na larabawan saida aka jawo kan khaleel, duk sun shirya suna jora su kamashi da lefi akwace licence dinsa akoreshi a progrm din sabida yanayin yadda Dr khalid ya fassara musu shi abun yay muni sosai.

Ransa ya baci kam musmn ma daya gane manufarsu akansa sede yadda yaga an taru masa akai ana neman kureshi yasaka ya sake ranshi ya shanye fushin ya hau fayyace musu abunda yayin dalla dalla kamar wanda yake koyarwa yan nursery one pupils karatu sukansu saida suka sha mamakin sa sosai.

Babu wata tambayar da sukamai da bai amsashi corectly ba sabida shi yay kayansa dakansa.

a Badon son ransu ba haka suka sassauto suka kuma aminta dacewa shine yay abunsa kuma zancen da aka kawo musu akansa na cewa yana da zafin kai da girman kai duk karyace ba gaskiya ba duba da yadda ya shanye bacin ransa agabansu Duk uban kure haqrin shi da sukayi.

the recording that was mearnt to embrass him agent na larabawan ya dauka batare da saninsu ba, ana watsewa awajen yaje ya saka a stream din media na larabawa da zasu bada contrct din, cos he was soo impress da bayanin da khaleel yay akan paper works dinsa wanda duk cikin likitocin da sukay nasu presntation din basuyi ba, kusan dukan alkalan masu contract saida suka bata lkcinsu akan video recrding din suna kalla wanda ya zamo masa wani hanya ta mabudin alheri dabaiyi tsammani ba.

shikam ma da matsanancin ciwon kai tare da bacin rai ya nufi gida, sai yaji azumin yau din ya taɓa shi jikinshi duk ya mutu idanunshi sunyi jaaa.

Tun ahanya da yake tuki yafarajin kmr zazzabi na damunsaa taciki, dede an fara ruwa kenan saiga kirar ogansa earpod ya juna yana waya da ogansa duk jiki shi yay sanyi dayaji ran ogan nasa ya matukar baci da jin abunda aka masa awajen, khaleel nata bashi haqr amma shikam saida yace zaiyi bincike akai sosai dan bazai yu ay treating din student dinsa kamar criminal ba.

Yace ma khaleel inta kama har kotu sai ya kai maganan cos this cud be a case of Blackmail and impersonification of character.

Dr aseem baiya wajen amma dayaji labarin abunda ya afkun saida ransa yay mummunan baci dasu. Har ji yay kamr ya cire khaleel a progrm din dan ya kare masa mutuncin sa sai kuma yace suje kawai Allah yafisu.
Yana isowa kofar gidansa lokcin ruwan ya mummunan tsanantawa

yay horn ma amma me gadinsa baijiyo shi akan lokci ba gashi yana kaiwa nan aka fara kirar sallahn magrib.

Computersa da jakarsa duka ya barsu a car din ya fito aguje ya nufi masallaci tsabar kansa na ciwo ruwan sadaqa da aka aje a masallacin ya dauka yay bismillah ya sha snn yay alwala ya jona jam'i akayi magrib ishai da asham din duka atare sabida ruwan da akeyi ya halatta a hada sallolin lkci guda. Da ake sallah ruwan ya dan so ya tsagaita amma suna idarwa ya dawo da wani irin karfi, aggauce kowa ya koma gidansa karshe me gadi ne ya shigo masa da motarsa cikin gida ya kulle gate din dan tsabar jikinda kayansa yay haryana diga ga ciwon kai da yunwa kamar zai kadashi.

Kusan sau biyu halisa na saukowa dubashi ko ya dawo ganin har bakwai da rabi yay amma bata gansa ba Ta koma sama abunta tana mamaki.

Yana shigowa da jikar da komi ya wuce kitchen dan izuwa yanzu duhu duhu kawai yake gani agabansa baijin inya kara minute baici abinci ba bazai fadi kasa ba.

Akan kitchen island ya aje jikakken jacket na suit dinsa, grey colour yabar white din yar ciki, tun yana nannade hannun rigarsa yafara adduarsa har dana cin abinci, tea pot din ya jawo ya zuba kadan ya shanye tas ya bi ya sake karawa saiga zufa ya fetso mai asaman goshi, foil din Samosan ya bude ya gani, qamshinsa da ya bugosa yasaka ya dauki daya ya jefa abakinsa wani lumshe ido yaay tare da bada nannuar sautin uhmmmm kunsan dadin abinci in kanajin tsinannen yunwa daban take, cikin wani irin yanayin santi yake tauna samosan yabi ya bude tukunyar spagh din kamr wani ninja haka ya zaro plate da fork a dish rag bashi minti biyu har ya zuba dede cikinshi akai,

a kitchen din ya jawo seat ya zauna yacinye komi da komi yaci dam dam, snn yake tunawa da baisha rawa ba, yana bude fridge din kitchen din yaga ginger juice daukawa yay yana sakin murmushi kamar dama can shi ya ajiye gashi tay sanyi yaji yajin ciitar tana tashi.

Gogan naku kaiwa daya yay yaji yakai kasar cup din kansa na sarawa kadan kadan ya bude kofar kitchen din da niyar neman halisa dan ya mata iyeyi akan juice din niyyarsa yace mata bai koshi ba. In his heart yasani sarai takan gane meyake nufi inyace mata abunta bai masa dadi ba,

He had a feeling in his heart cewa she do understand his harmless banters. Shide sosai yaji ginger nan ta shiga ransa baidamu ta sake masa ayau ba kodama zata nausheshi ne.

dede ya fito kenan suka cika karo da juna abakin kofar kitchen din Tana ta sauri danta zo ta duba taga ko ya dawo ganin har takwas saura na dare.

kiris ta rage ta bugeshi ya fadi kasa yay wuf ya capko waist dinta ya fizgota jikakken jikinshi jin wani irin kakkarfar feeling yay magneting din su gabadaya da mugun sauri ta tureshi da uwar masifa a voice nata tana cewa "waye wann, Waye wanann 'wayee haka, Baka gani ne zaka wani bangaje ni kai makaho ne kome.

daga kansa ke da wuya suka hade ido ganin irin kallon dayake mata cikin sauke nannauyar ajiyan zuciya mai tattare da kifiyar so da nuna kulawa

Hakan yasaka tabita murguda mai baki ta sauke idonta kasa cikin jin nauyin shi take yay murmushi sai kuma yaji kan nasa na mummunan sarawa.

girarsa na sama a dage yace"aka bangaje ki ko ke kika bangaje ni, wato ma ba kisan ya ake ba babba hakuri bako..

wani rau da ido tay batace komi ba dan dama kawai ta dubashin ne babban damuwarta dan sauran ginger drink dake kasar cup din ta gani a hannunsa ta kwace abunta"give it to me Wayace maka kasha?

Kyabe bakinsa yay yana kallon cute motsin da karamin bakintan yake, ahnkli yace wai ke kikayi?

a dan dake Tace eh

gani tayi ya rike bakinsa kamar me jin amai amai
Ya kuma cewa ke kikayi? ohhh my god,.mungode, amma kar ki sakeyi, pls Dont, dont do it again. Bai mana dadi ba sam.
Chapter 124 · 0% Book details