← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 312

Sashe 47

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Halisa data nitsu tana jinshi cike da gamsuwa tace very good. Harka da sabbin fuskoki yana bukatar kulawa sosai sai Ka kiyaye business da boyayyun drug dealers, child/sex traffickers da kuma money lounderers
..bana son kamfanoni na su hada harka ko hanya da masu gurbatattun sana'oi. But Let every company knw dat Halisa is open to new growth. I only want to do business. kawai inka gama binciken ka akansu ka gamsu sai ka dauki dikkan wani matakin daya dace karka damu da sai na saka hannu.

Cike da ladabi yace thank u for trusting me, in sha Allah duk abunda ake ciki zakiji Allah ya baki lafiya.

Tana murmushi tace Ameen...are you not hungry Comn we shud eat together yau. Kayi mana oder din Abinci inason naga kaci abincin agabana.

Yay murmushi yace yes boss.

Toh tayani tashi zanje nayi wanka inka gama sallan ishai saika kawo mana Abincin muci tun kafin wann wawan likitan naka ya xo yace zai bata min mood dina.

Baice komi ba ya gyada mata kai yana murmushi
Ahankli ya amshi hannun ta ya cire mata canula din ya kulle sann ya tayata ta mike tsaye.

Yana ficewa ta shiga bathrum ta cire kayanta tafara wanka acikin cold shower tanajin jikinta da dan karfi karfi bakamar da can ba.

Bayan ta kammala wankan ta yi brush ta daure suman kanta data jikashi da ruwa acikin towel snn ta fito dakin ta samu uztaz harya fita siyo musu Abinci, acikin dan kankanin lokaci tay sauri ta shirya kanta dama bawani kwalliya takeyi ba nan ta nemi waje ta zauna akan cushion tana latsa wayarta acikin nitsuwa.

Dagata dayan bangaren khaleel ya dawo daga masjid kenan jikinshi sanye da brown jallabiya data sha guga kai tsaye ya shiga dakin binciken sa ya tsaya agaban suirvellnce computersa dan ya duba ko halisa ta farka daga baccin ko bata farka ba, cos too much sleep is also part of signs and symptoms na depression shide yana ta iyakar baqin kkrinsa wajen gane dukkan wani halin datake shiga ciki domin yasan menene ya dace yayi.

Ganinta a zaune akan couch tana latsa waya cikin kwancyar hankli ya bashi mamaki, she look very innocent and calm yanata kallonta yadda ta zauna ta nitsu har yarasa mesa yake kallontan Can yay tsaki ya dauke kansa ahankli cikin sauke ajiyar zuciya.

Cikin dakinsa ya koma tare da daukar agogon sa na phatek dake aje a saman drawer gefen gadonsa ya kalli time its almost 7.30pm baiji duriyar meenal ba kuma bata kirashi awaya ba duk dama bai wani damu ba dan yasan Aldartace ficewa a duk sanda ta ga dama takan dawo kuma a duk lkcin datake so inyay korafi sai tace mai bazai taɓa fahimta ba dan kulawa da babban business da kamfani ba abune me sauki kamr aikin likitanci ba.

Meenal bata taɓa rasa wani hanyar da zata gayamai baƙar magana kota masa gori ba musammn ma akan abun duniyar data tara shiyasa wani lkci ya gwammaci ya dauke kansa akan wasu abubuwan datake aikatawa daya tsaya tana gayamai maganan banza.

Cikin sauke ajiyar zuciya ya aje agogon yanamai rayawa aransa cewa yakamata halisa taci abincin dare dan ya bata maganinta da wuri sabida yana da ayyukan da zaiyi acikin daren nan.

Wadrob dinsa ya bude kai tsaye ya ciro wata casual dress ɓakin jean da fitted short sleeve shirt sea green ya saka ajikinshi bakaramin kyau ta masa ba dan kuwa tamkar saurayi dan shekara ashirin hakann dressing ta maidashi.

Yaci akalla minti sha biyar yanakan shirya kansa dan kusan komin sa anitse sosai yakeyin shi sumtimes kamar ba namiji ba.

Bayan ya kimtsa suman kansa mayukan qamshi da brush yabi ya fetsa turarensa masu sanyin qamshi snn ya dauki key din mota ya juya zai dauki wallet dinsa sai bangansa anan ba.

Tunawa yay ya ajeshi acikin room din aikinsa agaban computersa kai tsaye ya koma dakin tun kafin ya miƙa hannu ya dauka idonsa ya sauka akan halisa da uztaz suna zaune a tsakiyar dakinsun suna cin Abinci kamar yan uwan jini suna yi suna dan hira.

Ta sake ranta sosai acting like she is fine dan Babban burinta shine ta cire wa uztaz damuwa a zucyarsa dan sosai takejin tausayinshi.

Hasalima itake take motivating dinsa Yana cin abincin sosai.

Gashi bata wani karya dokar ba, iya Abincin daya gindaya akan tana cinsu da dare din shine agabanta tana ci duk dama tin a fuskarta zakasan na dole ne take durawa.

Shikansa khaleel dake tsaye awajen ya riga ya gane sabida uztaz take cin abinci.

Mamaki ya daskarar dashi awajen cos At times sai yaji aransa kamr halisa tana da personality disoder yau ita mutuniyar kirki ce gobe kuma babu wani marabarta da cikakken mahaukaciya.

Haryanxu jiyake kamr He just cant belive dat she is dis down to earth and easy going person da
ma' aikatan ta har haka.

Ahankli Ya kyabe baki cikin rashin son barin zucyarsa ya yaudauresa akanta dan bazai taɓa mance irin tantarin rashin kunyar data masa abaya ba musamn ranar dataje har wajen aikin sa ta wanka masa mari agaban kowa akan meenal.

Cusa wallet dinsa yay acikin aljihunsa snn ya fice a dakin tunda yaga halisa tana cin Abinci sai baije dakin ba ba ya sauka kasa yafita ya dau motarsa ya jeshi regular wajen cin Abincinsa ya saya Abincin yaci awajen bai wani jima sosai ba ya kama hanyar dawowa gida.

Lokacin Su halisa har sun kammala cin Abinci uztaz ya kunna mata computerta ya saka mata dukkanin files datake bukata yanamai dada mata bayani ita kuma tanamai dada wayar masa kai akan abubuwan daya dace yayi dan Allah ya bata basirar kasuwanci bana wasa ba.

Tun da suka zauna anan babu abunda takeyi face dorashi akan hanyar da zai kaisu ga nasara a kamfanoninsu.

Khaleel na kammala parking ya wuce sama tattaro maganin halisa na dare anan ya xauna ya shiga harhadawa dan yagane kmr tana yawan tsorata inyana hada su agabanta tana gani.

Yana aikinsa a zaune agaban computer yana kallon su ita da uztaz dake yana respecting privacy nata sai bai saka volume ba, yakan iya kallon dikkanin motsinta ammma bayajin me suke cewa, ganin su kawai yay azaune suna tattaba computer halisa tana ma uztaz bayani shikansa khaleel din ya rasa meyene suke tattaunawa da suka nitsu akai sosai.

Shigarsa gidan bada wani jimawa ba meenal ta dawo gidan a mugun gajiye da riki rikin take aways na Abinci data kawo ma halisa.

Iya Jakarta kawai ta aje a dakinta ko wanka batayi tsayayi ba ta dan rage kayan jikinta ta sako wani marar nauyi ta nufo dakin Halisa da bags din chops din.

As usual bata wani knocking kawai ta turo kofar ahankli kusan dukan su saida suka kalleta a lokci guda.

Kafin kace wani Abu har halisa ta yi closing tab ta kashe computer dake gabanta cikin son ta biye komi nata cos she cant risk it anymore with fake friends.

Meenal na murmushin yake tace "Hey babe. Wow U seem okay, Wayyo Allah na naji dadin ganinki ahaka are u working?

Babu yabo babu fallasa halisa tace nop.

Da rawan jiki ta karaso
Tanamai cewa I brout u food..nan ta fara babbaje su tana budewa daya bayan dayan gabaki daya qamshin abincin ya cike dakin.

Kallo daya me kyau halisa bata kara mata ba bare Abinci ahnkli ta kalli uxtaz ta masa alaman yaje gida ya basu waje.

Babu tantama ya miƙe tsaye zai fice.

Meenal tay saurin dakatar dashi a walaknce
"Hey hey you mr worker
Ina zakaje baka serving inta abincin ba ko nine kake tsammanin zan maka aikinka.

Kafin uztaz ya amsa halisa ta kalleta tace let him be Amina, ni nama koshi yanzu nan muka ci abinci thanks.

Baki galala meenal take kallon Halisan batace komi ba har sukayi sallama da uztaz ya fice abunsa.

Acikin abubuwa masu yawa da suke damunta game da halisa ayanzu "AMINAn' da halisa ta dawo tana ce mata shine yake so ya fara daga mata hankali tarasa mesa Halisa ta sauya mata gabaki daya.

Hawayen makircin data saba ta kwkwalo zata fara kwarorowa halisa zantukan ban tausayi

"Na hana kaina cin komi tun safe a tunanina zanzo muci abincin tare dake aminiyata, Halisa meye na miki pls, Abincin nawa ne bazaki ci ba Cos how cud u just say kin koshi? Is very disgusting kina cin abincin da mai aiki haba.

Halisa tana budan baki sai sukaji sallama ata bayansu khaleel ne ya shigo dauke da medical pan tray a hannunsa ya bisu da kallo daya ya dauke kansa.

Daga ita har Halisan babu wanda ya amsa sallamarsa wanda hakan yasakashi ya dada harde ransa sosai..

Meenal na ganinsa tafara karya wuya dan makirci please halisa kici Abinci...

Halisa tay kamar ba da ita takeyi ba

Ta juyo ta kalle khaleel cikin langwabe wuya babe kace mata taci Abincin mana dan Allah tay maganan tanamai kallon khaleel a shagwabe.

Baice mata uffan ba ya cigaba da abunda yakeyi

Ran meenal sosai ya sosu da sharetan dayay

Ahnkli Halisan tace mata na riga na ci Abinci,u see he cant force me to eat again . Kici Abincinki inkuma kin koshi kibawa wani yaci.

Meenal tay rolling idanunta cikin jin haushi tace dont bother i think ive just lost my appetite

"Okay goodnite"
Acikn rashin kulawa Halisa tace mata hakan

tay saurin dagowa ta kalleta da matsanancin mamaki ganin irin ko in kula da rashin nuna damuwa da ita da batay ba.

Aranta tasan Halisar data sani da tausayi da saukin hali koda bazataci abincin ba da zata iya tursasa kanta taci na dole kodanta kwantar mata da hankli..halisan data sani ba wann bace.

Rai a bace ta miƙe tsaye batace musu uffan ba ta fita acikin sauri ta koma sashenta da tunane tunane.

Ko kallon inda tabi halisa batay ba. Hakama tun da khaleel ya shigo dakin basu cewa junansu uffan ba.

Bayan ya zuba mata ruwan magani acikin normal dosage dinta na induction sai kafin nan ya taho ya tsaya a kusa da inda take yanamai kureta da kasaitaccen idanunsa mai cike da kwarjini.

Tunda ya zuba mata ido banda Bugawa babu abunda kirjinta yake amma babu alaman hakan data nuna a fuskarta.
Chapter 47 · 0% Book details