← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 312

Sashe 19

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan Dukkansu sun rasa meyake faruwa da halisa data daukewa kowa wuta taki cewa komi game da halin da take ciki. Harma gara gara jasmine idan tazo tana iya kyaleta ta dan rungumeta suyi kukan su atare.

Bakaramin tausayinta jasmine takeji ba shiyasa a duk sanda suka zauna atare sai tay mata hawaye , Duk sanda suka dan kebe daga hayaniyar meenal sai ta tambayeta halisa kin tabbata zaki iya daurewa acikinsu kowa????

Inhar kinason afasa kwai kisane ina tare dake..cos i cant wait to expose that evil woman..zanso inga me zatacewa sauran kawayenku akan abunda tayi maki da rayuwarki.

Halisa saidai tace mata kibar maganan kawai jasmine tonowa meenal asiri tamkar tonowa kaina asirine aynxu..
Banajin dadin rayuwata bazan iya jure wani tashin hankli yanzu ba
Komi da kika gani yar hakurice da sannu ahnkli zanbi lamarin..kiyi hakuri jasmine Banason na sake memeta tuninin abunda nayi...its wrong i shudnt have tried to kill myself.

Kusan jasmine dinne kawai tasan halin da halisan take ciki sede tun zuwanta da halisan tay mata alaman cewa bata son kowa yasan da akwai wani abunda ya faru a tsakaninta da meenal talba wanda shiyay musabbin jefata acikin wann hali yasaka jasmine din bata nuna musu alaman komi ba.

Duk da shirun da halisa tay bai hana sauran kawayen cigaba da kkri wajen ganin sun bincike zach ba, meenal tay nan tay can, tarasa meke mata dadi, halisa taki sake mata taga kmr ma jasmine ne kawai take sakewa tay magana me tsayi da ita, daga ita sai kuma uztaz .. ganan ma su shemau sunki sam su bata hadinkai ita da vicky bare abar maganan zach ya wuce mata.

Itakanta shemaun ba adede take ba dan kuwa tun jiya wayarta yake akashe sabida bata son ta amsa kirar mahaifyrta data umrceta da akan taje Abuja ta kula da lafyar mijinta mahmud yau kwana biyu kenan amma batavisa Abujan ba.

Itama so take halisa ta tabbatar musu cewa zach ne musabbabi dan koda zata wuce Abujan ta tafi da shirinta akansa sedei shirun halisan ne ya dakatar musu da komi.

Wani binma jasmine ne kawai take iya sakata budan baki tay magana da kowa bayan nan shiru takeyi ko tace thanks ko okay sai uhm mmmm.

A brain dinta kusan kowani dakikanin lokaci lissafi take na yadda zata soma sabuwar zama da su meenal dan gani take dolene ta hakura ta fahimce asalin wacece meenal talba kafin nan ta fara tunanin yanke mata wani hukuncin daya dace inma rabuwa da ita zatayi batason tay mata hukincin acikin fushi ko garaje.

Ayayinda case yay zafi kowa ya zuba ido yana sauraran abunda zatace.

Washe gari sassafe khaleel ya dawo daga masallaci kenan sao ganan wasu mutane sanye da bakaken kaya suna hade ido suka hau bibiyarsa abaya abaya.

Tafiya yake gabansa yana faduwa har saida ya cimma kofar gate din asibitin kafin nan suka ciimmasa dayan gayen ya sha gabansa dayan ya taresa ta baya.

Gabansa na faduwa yace malamai lafya?

Dayan murdadden gayen yace ..."Dr khaleel?

Yace yes .

Ogan mu ne ya aikomu wajenka...

Khaleel yace oganku?
Waye kuma oganku..

Batare da sun amsashi ba dayan ya fidda wata envelope daga aljihunsa ya mikama khaleel snn yace kaduba ciki kagani ko kasan wann yarinyar?

Tun kafin khaleel ya bude gayen ya fidda wata arniyar bindiga daga aljihunsa yanamai nuna masa cikin wata dakakkiyar murya
...hurry we got a message for ur patient doc ..

Khaleel yana bude envelope din yaga hoton halisa tare da zach sunyi matukar kyau they both look so happy and in love dan sabbin hotunan da suka dauka kenan kafin ranan aurensu da meenal ta tarwatsashi.

Kansa yaji yana sarawa daya gansu ahaka dan Bai wani bata lkcin sa wajen kallon halisan ba zach din kawai yaketa kalla dake bai wani sanshi sosai hakannan ba sai a social media da ake ta nuna speech dinsa akan halisa.

Har cikin ransa yaji tsananin kishin ganin hoton duk dama baisan kishi yake ji ba...he just tot he hated this guy.

Ya hade rai I'm sorry i cant take u to her, kuje kucewa ogan naku inhar sako yake son ya isar mata he shud find a way to knw how to do that amma bata hannuna ba...what nonsense ya fada cikin masifa.

Dukansu suka fidda bindigoginsu na gaban yace Doc i am warning you.. i don't have alot of patience.

Dayan gayen yace kana wasa da rayuwarka ko
Sai mu kasheka anan mu kashe banza...

Khaleel yace is my job to protect my patient u can do what ever u wish kodan kun fito da makamaai kuke ganin zanji tsoronku.

Dariya dayan gayen yay
Doctor munsan baka tsoron mutuwa...
Infact, our boss is impressed with u..u save her life ...bazai taɓa sakamu mu kashe wanda ya ceto rayuwar macen dayake matukar kauna ba..shiyasa ma ya aiko mu wajenka..baka sani ba, hala ma tanada bukatar ganin wann sakon..5 mins, and we r out.. hadin kanka kawai muke bukata ..

Khaleel yay tsaki dan shikadai yasan abunda yakeji aransa yace musu is not possible to let u in.
Ina saqon kubani...i will decide intana bukatar gani.
Babu yadda basu so su tsorashi ba amma yaki sam.

Sai cam dayan Gayen ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya danna wata lamba,.snn ya ja gefe yay magana ya dawo yace
"Okay fine...zamu baka sakon. Amma dolene mutim daya acikinmu yabika domin mutabbata ka miƙa mata.

Khaleel baice musu komi ba sukaje suka dauko wani envelope da wasu manya manyan bonquites na flowers shikansa khaleel baisan tarkacen flowers bane saida sukahaura sama
Lkcin halisan tana bacci

Suna shiga cikin room din gayen ya nemi waje agefen gadonta ya aje bonquets din sann ya yaye abunda suka rufe flower dashi, wasu red rosesss ne masu tsananin kyau tare da strands din white roses daddaya ajikinsu bakaramin kyau flowern yay ba kana ganinsa kaga mei tsada sosai.

Kallo daya khaleel yay ma flower ya dauke kansa har gayen ya mika masa wata envelope snn ya fita ya jima awajen yana kallonta aransa harji yake kamar ya bude sakon yaga meyene aciki ya kasa motsi cikin ransa sam babu notsuwa yabi ya kure envolpe din da idanunsa yana lissafin yadda za'ayi ya budeshi

Motsawar da halisan tay acikin bacci yasakashi dawowa cikin hayyacin shi. Da sauri yay gaban flowers din ganin Igiyar canular dinta ya sarkefe jikin flower din yana kkrin rabawa kenan ta dan fixge hannunta cikin bacci dawani irin karfi suka rikota kasa glass din daya rike kasar flower
Ya fashe tasssss saida ta farka kusan a gigice.

Da wani irin kallon bazata suka kalle direction din atare zucyarta na zillo da mamakin ganin khaleel agaban flowers tana kkrin miƙewa zaune da kyar ayayinda hannunta yaci tuntube da envelope din dake gefenta.

Wani irin girman kan ta tambayesa na waye takeji wanda hakan yasaka ta dauka sann ta budeshi kai tsaye.

Akaro na fako dataci karo daa handwriting din zach saida ta lumshe ido kafin nan ta bude nan take tafarajin kamr ma kawai ta rufe sakon ta ƙona ko ta yaga basai ta karanta shi ba, dan bataga dalilin da zai saka ta karanta ba, dacan harta yanke hukuncin aikata hakan aranta sai kuma taga irin kallon da khaleel yake mata wanda sam ta kasa ganeshi, his expression was blank and unreadble...

Irin was he expectiing her not to read it sabida da sakon daga wajen zach ne?....

Duk dama a zahirin gaskiya abunda yake ransn kenan ko kadan baisan halisa ta bude sakon nn barema ta karantashi amma kuma baisan meyasa yakejin hakan aransa ba

Dan kamar yadda yaga su shema'u da vicky tare da hadiza sunata kkrin su rabata da zach din nan kwata kwata shima aransa kusan hakan yafi amincewa dashi...

Dan bisa da kalaman mutane gani yake kamar zach ne babban matsalar dayake cikin rayuwar halisa ayanzu ..

alho meenal is the only one denying it, saidai shi kansa yafi gamssuwa da harsashen dumbin mutane akanta fiyeda na zantukan meenal datake kkrin cusamasa aransa najin cewa kmr child hood trauma ne kawai yke damun halisa babu batun zach din aciki

Yabi ya zuba mata idanu koda zataji nauyinsa aranta taja tsaki ta bude kawai ta ƙure rubutun da idanuwanta yana kallon ta harta kammala karantawa tanamai sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar dayasaka yaji nashi zcyar ta buga.

Ahankli ta lumshe idanuwanta da suka ciko da ruwan hawaye masu tsananin zafi da karsashi.

Dan da alama zaach ya girgiza matukar girgiza dayaji labarin cewa har tay ynkurin kashe kanta.
A tunaninsa lefinsa ne dan saida ya dawo hayycinsa snn yake gane cewa abunda yay matan sam sam ba girmansa bane saidai sharrin shaidan daya zugashi dan ya toxartata da tsananin soyayya tare da kishinta dayakeji aransa dayakasa control nasa.

Dukkan wani abunda ya wakana tsakanin sa da meenal bai boye mata yau ba ya gaya mata iyakar abunda bata sani ba. Wanda already yanxu hakanma ji take kamar tafishi sanin hakan tunda da kunnuwanta taji meenal din ta furta harda dalilinta na aikata mata shi.

For her peace of mind he his willing to leave the country for good, snn ya nemi gafararta, yace mata rayuwarta yana da muhimmaci agaresa fiye da komi dayakeji na ciwon rasata dayayi a duniyarsa gabaki daya.

Hawayenta masu zafi haka suka dinga zuba ayayinda take tunowa da nitsatsuwar kalamansa masu cikke da nadama da neman yafiya aciki.

Saiyau ta fahince zach sosai, ta kumaa gane cewa meenal is really poisonous and she can do much more maybe tunda harta iya dasa masa abubuwa marasa goguwa acikin kokon ransa game da ita.

All the dirtiest part of her life dat he is not willing to accept duk da irin son dayake ikirarin yana mata aransa har yanxu

Altho he was soo late, yau datake aranar daya tona asirin meenal din already ta rigashi jiyowa ata wani sigar da batay tsammanin zataji shi ba.

Yadda ta rungume letter bisa kirjinta yasaka khaleel kangarewa awajen yanamai kallon ta bakinsa kusan abude..

Kusan Babu abunda kwakwalrsa take ayyana masa alkcn face ko hala zach zai dawo gareta ne wanda yasaka ta shiga irin wann tsumamamen yanayi kuma agabansa batare da taji ko dar dar ba.
Chapter 19 · 0% Book details