← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 245 OF 312

Sashe 245

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

take Meenal tay lumui kunya da rudani ya fara kakkarya mata gabobin jiki.

Rai abace halisa tace ko akai ki ciki ne ki binciko shi, daki daki, lungu da sako..or maybe i hide ur husband in my cupboard.

Bakin meenal na rawa rawa tace halisa..

da hannu Halisa ta dakatar da ita..

snn tace hmm Amina kenan dama ance listen to ur friends words wen he is angry, naji kina zargina akan mijinki amma kisani alot of things u did danake dauke kaina akai kamar karyan dakike yadawa akaina dan mijinki ya tsaneni ya cigaba da min kallon rashin mutunci..

ke kin iya boyemin anma ai shi bai iya boyemin, he told me and he insulted me with it. Kuma dama abunda kike so kenan. Amina u call ur self my friend but ure stabbing me at my back, abubuwa dayawa na mugunta dakika yi akaina ke kinfini saninsu duk bance miki komi ba Amma kisani shiru shiru ba tsoro bane, kema kuma akwai ranar da zaizo wanda bazaki taba gane ni ba, u wil wonder weda u knw me or not. Dan haka Get out of my house right now ko nagaya maki maganan da kema har kimutu bazaki mance shi ba..

A jirgice Meenal ta rusuna kasa ta rushe da wani matsancin kuka me kara...

haba halisa Haba halisa dan Allah kiyi hakuri i don't mean to say or do this..wallh wallh sharrin shaidan ne, nasaka rai akan zoben nan ne and he left me last night while he is angry ina tsoron kar yace zai rabu dani,ni bansan ina zanje in nemesa inbashi hakuri ba... Halisa ure like my sister wallh ba har raina nake gaya maki wann maganan ba ni wallh ba zarginki nake akansa ba
Dana shigo gidan nan ne fa nayi kamar naga wata motarsa anan, it maybe my imaginations, halisa dont take this to heart.
I just love my husband, i can't live witout him shiyasa nake behaving hakan bafa bataki nakeyi awajen sa ba.

Tana kukan makircin Halisa naji kamar ta shakureta sanin cewa duk karya take fada ba gaskiya ba.

"Amina U ought to leave

a mugun dake ta fadi hakan. Snn ta kalle Uztaz tace pls escort her out and make sure u lock my gate. Tana fadin hakan ta wuce cikin gidan ranta a bace tabar meenal din awajen akasa tanata kukan makircinta tanata maganganun karya.

halisa na shiga ciki meenal ta mike tsaye ta dada kare ma gidan kallo tanashan mamakin yadda akayi motar khaleel ya bata dan tasan dai tagani.

Jiki babu kwari ta bude motatta ta fita tana maai matsanancin jin haushi da kuma dana sanin yadda tay aproaching din halisa..dama akace in baka iya kama barawo ba barawo saiya kamaka.

Kwata kwata yanxu sai take ganin kamar itace batay ma halisan adalci ba, har tsoro takeji kar halisan takai maganan wajen sauran kawayen su, tasani kusan kowa zai ci mata mutunci akan hakan datay bamai fahintrta. Cikin rasa meke mata dadi ta koma gida taci kukanta bana kadan ba.

bayan damuwar khaleel haka tay shiru tanata tunanin yadda halisa zata na kallonta yanxu musm ma ganin irin bata mata ranta datay.

Haka ta wuni da damuwar rashin sanin inda khaleel yake da kuma jin danasanin zuwa gidan halisa datayi.

bayan tafiyan meenal uztaz yazo falo ya same Halisa hanklinta a tashe dan bata saba gaslighting din mutum ba abun sai yana damunta tace uztaz ina ka kai motar ka boye???

Yace i am sorry boss, key din na wajen fadila ce bansan inda tay da motar ba.

Cikin lumshe ido da budewa tace ohh thank god for fadila nida bansan ya zanyi in cire kaina a wann fitinar ba..

'Keep an eye on meenal kaji..he is very upset with her and i dont think is best they meet here.

Uztaz ya gyada kansa snn ya fita.

Daki ta haura ta samu yanakan bacci bema san me ake ciki ba. Ta gyara masa bargonsa ta dada rufeshi snn ta hadamai ruwan wanka ta aje masa kominsa steady.

lkcin ana neman 10:30 taje kitchen ta hau hado musu kayataccen break fast. Tana dawowa ta samu har ya farka yay wanka ya fito daure da towel akan kugunsa suna hade ido ta dan sunkuyar dakai can kasa snn tace "gud morning champ". yay murmushi yace morning bbygirl thanks for the warm bath..and give me just five minutes yanxu zan shirya kinji ko

Tana murmushi tace "..okay sir, inka gama ka kirani..kallonta ya dingay yana murmushi harta fita. ..

Sama sama ya kintsa kansa ya maida kayan sa snn ya dauko breakfast din ya biyota dashi falon sukaci anan. Bata nuna masa alaman komi ya faru ba, Har saida sukayi nisa kafin nan Fadila ta kawo keys suka gaisa, halisa ta kalleta ahnkli tace thanks, dayaga suna kallon kallo sai ya kalle halisan yace "what happen? tace nothing.

Bai takura musu ba ya fara jan fadila da maganansu da business marketing anan agaban halisan suka tattauna har inda zasuna haduwa da duk wani abunda zasu yi

Yace mata sai yay tafiya ya dawo bazai jima ba zaije ne yay formal report awajen aikinsa a saudi sai abashi official leave
fadila tace masa babu damuwa.

His big plans was idan yaje saudi yay report ya amshi official hutu kafin hutun ya kare zaiso ace sunyi aure da halisa dats just wat he is hoping for
Ace angama komi nan da wata guda. Yasan dai kudi bazai zamo matsala ba, sabuwr gidansa dake nan ikoyi kuma already an gama, furnishing ne kawai bai gamayi ba dakema ba ajima da gama aikinsa gabaki daya ba dan babban gidan sama ne kuma wasu abubuwan ma basu gama bushewa ba.

Bayan sun gama breakfast around 12 pm na rana halisa ta shirya kanta tay kyau a cikin wata green and red multi colour material gown suka kama hanya izuwa ganin gidan nasa.

After few minutes of drive suka iso wani layi acikin ikoyi wanda zallan manyan gidajene na yarubawa ne zaunannun masu kudin gari wanda suka dan manyanta basu fiye zama a nigeria ba dan haka arean yake nan quiet and peaceful banda masu gadi da security babu wasu masu wulgawa. Shararen street na tsakiya suka wuce gida na daya suka wuce na biyu ana ukun suka dan tsaya abakin wani fankacecen Golden gate mai tsayi da girma sosai.

Khaleel yay horn mai gadi ya bude masa kofar agaggauce nan suka shigo ciki motarsa na tafiya ahnkli dan kuwa hanyace mikakkiya an kawata gefe da gefen hanyar tasu da wasu beautiful assemblies of dark green palm trees tareda wasu balaggun bishiyoyin dogon yaro
ga furanni here and there, gabaki daya gidan yay inuwa iska me sanyi yana kadawa aciki.

tun basu sauka daga motar ba Halisa taji she is just falling in love da environment din ta waje, sunan me gadin Shina acikin ladabi yazo ya bude musu kofar mota ya tsuguna har kasa ya gaishesu, duk ya dauka ko ita matarsa ce. Ya amshi jakarta ya rike yana madam welcome
ganinta kyakkyawa ga class jikinshi na bari yay intrducing kansa sharply.

Murmushi kawai ta masa

Khaleel ya amshi jakar yace masa they wll be in d house for a while duk wanda yazo ya kirashi a waya tukuna.

tundaga nan suka fara zagawa Ta cikin harabar gidan khaleel na mata bayanin dalla dalla yana tsokanarta suna dariya.

musmmn da Yace kinga in yan kawo amarya suka ɓata ahanya saikice musu kinsan gidan mijinki abunki.

Bakaramin dadin ganin gidan tay aranta ba, aranta tay ta tunanin mesa meenal taki zama anan dan kuwa gidan yafi natan komi da komi ga fadi ga yelwa ga kayan hutu.

Or maybe she just dont want to feel less inta zauna akasar khaleel shiyasa ta gwammci ya zauna a gidantan kawai.

Suka cikagaba da zagawa ga parking lot manya guda biyu da garage guda daya, ta bayan gidan suna da babban swimming pool mai shape din kwakwa da kuma blue aqua pond in a small conservation garden wasu fararen agwagin ruwa kananu na shawagi akai. ga can baberque spot, dan Filin dake wajen akasa cool down chairs da karamin filin ball ko wani small events na yara aciki..
NA KUDINE CHAT 08060712446 TO PAY

#SURAYYAHMS

Halisa Tana daga tsaye abazata taji khaleel ya dauketa cak suka shiga daga cikin gidan ta main entrance Da akayi shi da wani irin expensive marble tiles dan kusan komi nasu na zamani ne.

babban gidan sama ne me Definate shape irin morden sleek building inn nan mai dauke da babban falo da zai iyacin manyan setin kujeru uku da dan karamin falo next to it wanda zai iyacin set din kujera daya da yan madaitatan Bedrooms self contain guda biyu a kasan, with a big L shape morden kitchen of her dreams me shegen fadi wanda da wani irin smooth opaque glass akayi bangon kitchen din gabaki daya zaka iya kallon duk abunda ke afkuwa ta waje amma na waje bazai kalleka ta ciki ba.

A can sama kuma part ne manya manya guda biyu masu kominsu iri daya, A tunaninta ko nata ne dana meenal sai taji gogan yace mata site din daya nashi ne daya kuma na babygirl dinsa aransa yasan dai meenal will neva try to move in with him saboda jiji dakanta shiyasa har acikin ransa baima sakota a lissafin gidansa ba gashi manya manyan dakuna ne a saman masu world class walk in closet da huge dark oak wood walls da two sided bathrum me shower da manyan bath tubes, sink area da kuma loundry na zamani.

babban dakin dake tsakiyar sashen nasu kuma dakin yara ne dan kuwa tsarinshi kamr na dormetery akayi shi wanda komin yawan yaran da zaku haifa bazai kasa musu ba. Extra room dinsu babban study room ne, da home office da kuma gym. komi yay mata har ranta amma Babu abunda yafi burgeta kamar tsarin kitchen da kuma indoor swimmig pool din dake can bayan dakin ogan nata just behind his glass walls dan tasan romantic spot ne da za'a sha soyayya sosai.
Chapter 245 · 0% Book details