← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 239 OF 312

Sashe 239

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafsa tay dashi ya sauko amma da kyar ya amince sabida yasan duk yadda akayi zancen shemau akazo musu dashi shikuma he dont want to even hear her name in his house.

Amma dan sabida kar hafsa ta bata rai dayai ya wanka yaci abincin sai yace mata suje falon tare
Hafsa ta dauki mayafi ta rufe jikinta ta biyosa

Tun saukowarsu mum din shemau take satar kallonsu jin wani abu ya riketa a kirji aranta tace lallai shemau ta tafka kuskuren da har ta mutu bazai dena haunting dinta ba. Tay asarar miji tay asarar arziki tay asarar duniya da lahira.

Mahmud yay sallama snn ya tsuguna kasa ya gaisheta da sanyin murya batama iya amsawa da kyau sabida kukan daya rike mata kirjinta sosai sama sama ta babbashi hakuri ta masa nasiha, tare da hafsa din ta musu nasiha sosai..hafsa mata mamkin ilimin addinin da matar tale dashi kamar ba ita ta haife shema u ba. Bakaramin tausayi ta basu ba, yamma yay tace zata wuce gida.

Da mamkimta taji Mahmud yace zasu kaita shida matarsan Duk kinta kuwa haka suma rakata har gida a babban motarsa shida matarsa suka shiga har falo suka gaishar da baban shema
Ya nuna masa hafsa shima ya saka musu albarka ya babbashi hakuri ya masa nasiha sosai Kana ganin yanayinsu zaka san bakaramin kunya shema ta jefasu aciki ba. Haka mahmud ya dauki checkque din kudi ya aje musu agabansu snn suka wuce..

ranar kwana mahaifyar shemau tay tana kuka tanakai kukanta wajen Allah akan abunda shema ta jawo musu har ace da aurenta zataje wani kasa tare da saurayi??? Kuma ta saka mijinta ya saketa saki uku akan abun duniya??.

Washe gari haka mahaifin shema yace ace ma shema kar ta sake tafa kafarta cikin gidansa. Inba haka zai tsine mata albarka.

Kowa ya bari akan bacin rai ne ya saka ya fadi haka face saida abun ya dan kwantar da shi shemau tazo gaishesa ya tashi da gudu ya bita da sanda ya rakata har waje.

Bayan kwana hudu masu kyau bayan wucewar hajy badiatu abuja angama magaman schl din hafsa an karkare komi da cewa zata koma turkey ta karasa 2 session dinta wato wata shida sai ta dawo nigeria ma gabki daya daganan kuma har saita haihu.

shirye shiryen hakan sukeyi a kwana na hudun kawai sai ga shema tazo gidan during wekends da hayar mota me gadi yay kamar be santa ba ya saka ta paker motar awaje ya dinga mata tamboyin renin hankli

Daga baya dayaga ya haukatata snn ya kyaleta ta shiga, tun daga kofa brain dinta ya rikice ganin irin level of standard na gyaran da mahmud yay ma gidan wayyo itama datakejin kanta wayayya kenan amma sai da tay kauyanci aciki.

ta sako wani abaya ta ci dark spec Bata iya shiga ciki ba sai data zaga ta dada gane cewa yes da gaske ne mahmud ne ya samu kudin nan fa.

Her heart was seriously pounding tanajin kamar ta rufe ido ta bude ace mata itace mata a gidan nan once again.

ta leka wajen ajiyan motoci sai bataga car dinta take shiga ko daya ba saidai wasu sabbin Mahaukatan jeeps da lexus, benz da porche
Da sport car guda uku
Ja da fari da baki.

rike Zuciyarta tay dan kar ya faso waje ya zube a kasa, kafin ta gama gulmanta ta fito sai ga mahmud ya fito Me gadi ya kirasa awaya dan shikansa me gadin ya tsane shemau da kalar muguntanta.

Sanye da kananan kaya ajikinsa ya fito da waya a hanunsa Tana ganinsa
ta wani sauya fuska da taku tana sauri sauri zata iso tana daf wajen sa sai taji takun mace ta fito ta bayansa da snyin murya tana cewa hubby ka zo kaci abincinka kar ya huce...READ, AND COMENTS.

NA KUDI NE 08060712446Isarta wajen ta samu shema'u da vicky suna zaune a babban falon hadiza an yi decorating dinsa yay masifar kyau suna hira suna wani irin kwashewa da dariya.

riga da skirt vicky tasaka na wani red and golden colour brocade material me shegen tsada tay asalin dinkin inyamurai ajiki ta kama albartaccen sumanta da bakin gel jelarsa ya zubo mata har kafadanta wanda hakan bakaramin fidda kyaunta yay ba duk dama heavy make up tayi.

babban leshi shema ta saka ajikinta tay kyau babu lefi, ita tafara hallarowa, sede duk ba a sake jikinta yake ba dake wasu kadan daga cikin kayanta na gida wasu suna nan bata kyautar dasu ba, jeweries din ne dai saida ta dangana da aro dan kaf ta yi kyauta dasu da zimman in alhaj shafiu ya samu contrct zata saya wasu, kayanta kuma ta siyar agarin zaman jiran alhaj shafiun acan dan bata dawo daga uk da komi ba.

Meenal saida ta gama kare ma kayan jikin sun kallo tsaf sann ta dada gyara zaman bubun ta tay gyaran murya, acikin su kowa ya mata kallo daya daya dake sunsan ta da iya burga.

Cike da neman tsokana Shema tace uhum kaga su manyan mata sun halloro.

wani irin tafiya meenal keyi cike da kasaita har ta iso tace hi girls, hannu ta mika musu, vicky ta basar ta dau drink ta rike tabi ta hade rai muryanta ciki ciki tace "hi. Daga nan bata sake ce mata komi ba.

meenal ta zauna a tsakiyarsu kusa da shema, minti kadan sai ta gyara zaman wuyan rigarta dan aga abun wuyanta na wasu shegun black stones da ta siya dan kaf jeweries na diamond dinta da gold dinta ta saida su, shema ke hura mata kyau kai kawata wnn shaddar ta hadu.

Vicky ta daure tace Amma ai kin kwafsa ya baki saka diamond necklace akai ba.

cike da rigima meenal tace "nagaji dashi ne.

shema tay dariya tace kai kawata kode kin siyar kin biya bashin kamfani?
wallh ko jiya naji ana maganan cewa zaki saida kamfaninki sabida tsinannen bashi Meenal wai me kike da kudi ne, u dint change house, u didnt change cars.. toh ina kudin bashin sukaje?

Cikin rolling ido tare da jin zafin maganan tace
Shema pls, enuf of this sau nawa zan gaya maki cewa batamin suna kawai ake sonyi have u seen my acct balance?
Beside my husband is on top of one big arab contract kwanan zaki sha mamaki...

Shema tay yake batace komi ba, dan ambatar contrct da meenal tay kadai saida atake ya tuna mata gajen hakuri da tayi akan mahmud.

"Ina su hadiza?..

Shema tace suna ciki
Da halsy tana tayata saka kaya.

meenal Ta kyabe baki hmm kuce dai nikadai ce nayi latti anyways thank god i am here. Tana gama rufe bakinta saiga su hadizan sun fito halisa na mata video hadizan tasaka Golden
Lace irin soltis swiss din nan me shegen tsada da ake bugashi originally a kasar switzerland, yau kusan komi da hadiza tasaka is golden in colour dayake nuna yadda dukiya da hutu ya gama rtsa mata fatar jiki gashi tay wani kwalliya me daukar hankli..

Daga ita har halisan baka isa ka iya dauke ido akansu ba. Halisa ta saka tsiririn wittels bach diamonds necklace me tattare da hadadden agogonsa saida zoben su da khaleel to touch up the look. Kalar kayan data saka sky blue ne kuma atamfa sai tay kamr wata amarya.

hadiza kuwa wata mahaukaciyar sarkan Gold ne da warwaronsu suke wani walwali a wuyanta kamar wata sarauniya..

Kusan suman tsaye shema tay tare da jin kanta na juyawa, idonta atake ya ciko da ruwan bakin ciki da kuma zafin hassada me tsanani tanaji a zciyarta cewa itace tay asalin dacewa da tay irin wann luxurios life din, ba simple and kind woman wacce bata damu da abun duniya kmr hadiza ba.

vicky ta mike tsaye tace ohhhhhh my god hadiza u killed it...

Meenal take ta dauke cak wajen kallonsu duka dan duk sai taji ta mugun raina kanta.

Murmushin dole take yi Tuna manya manyan gwalagwalnta data siyar sai atake taji wani abu ya cakketa a kirji haka tay saurin shanyewa tace woooowww..dizo, dizo.. dizo.. tafara hailing din hadiza badan taso ba.

Ko juyawa halisa batay ba bare ta kalle meenal da ta kafeta da idanu kamar ma bata gane ta ba.

She is actualy thinking of how and when halisa ta dinka wnn kayan daya mata mugun kyau dan tasani sarai halisa bata taɓa saka atamfa ba bare harta san ya ake dinkasu. Hmm, Ba wann bane ma babban abun da yafu ci mata tuwo a kwarya face damuwar ta na ganin kamr bata da wani matsayi ko saurqn muhimmci wajen halisa itade tanata tsammanin ko ciwon nan ne ya sauya ta.

Abunka da me fuska biyu halisan bata kulata ba amma haka nan taje ta rungumeta suka hi hi cikin kyabe baki tace " su halsy manya ashe kin iso shine ko ki kirani awaya muzo tare ainima da na tsaya kin shiryani.

Halisa tay murmushi tace u look good Amina
Ke ai babbace basai an shiryaki ba. Daga nan ta wuceta ta nemi waje ta zauna daf da vicky kusan kowa da abunda yakeji aransa tasan meenal bata ga zoben bane har yanzu. kafin Kace wani abu har an shanye na ciki an tsunduma hidima kayan ciye ciye da shaye shaye kowa na hiran shirmensa zaka rantse babu komi aransu.

Hadiza ta fara magana
Me dan tsayi game da abubuwan da suka faffaru snn vicky tay musu godiya ta kuma cakka magana direct ma meenal akan masu fuska biyu, sai Shema tay akan abun duniya,sann akazo kan meenal yar fafa da cika baki tanami nanata musu cewa ita she is fine
Snn Sudena daukar rumors akanta intana da wata matsala sune zasu fara sani. Abun dai ya daure ma hadiza kai sosai sabida bata taba samun kuskure wajen samun labari amma tunda meenal ta dage sai aka basar. Halisa tace she have nothing to say.

Aka kawo photographers ya musu hotona masu kyau na tarihi, sann aka kawo wani katon golden and milk colour cake mai hawa biyar kowacce zata yanka step daya ta saka a plate nata taci.
Chapter 239 · 0% Book details