← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 238 OF 312

Sashe 238

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sumhow dai tana da karfin gwiwa cos tasan mahmud is kind and gentle tasan bazai koreta ko ya Walakntata ba

haka ta shirya kanta tsaf da yamma wajajen karfe hudu snn ta kama hanya taje asibiti inda su vicky suke, she had to borrow a car, dan dama bata nata nakanta duk zaman sun nan Da bazar mahmud take taka rawa haka zai siya mata masu shegen tsada shikuma ya shiga mota dan dede but he was wise enuf yay register komi da sunan sa shiyasa when she leaves she gets nothing frm jer except her cloths
and luxuries duk ya saka an saka maga Amanya manyan jaka mai aikin tsakar gidan ya aje awaje cikin store room izuwa ranan da zata aiko azo a dauka mata su

Asibiti da motar haya tazo, and she pretended like babu abunda ya faru da ita taci ado abunta cikinsu kowa yay murnan ganinta su halisa hadiza
kowa na wajen,sai daf magrib kafin nan meenal tazo tana wani noke noke wai bata da lafiya sai taga daga hadiza bamai bata fuska sosai
awajen..

Halisa tasan kalau meenal take hakama vcky, shemau kuwa tun zuwan meenal suka fara cakka ma juna magana

Saitana satar kallon idon halisa tana nuna musu kmr cikin khaleel take dashi..cos haryau da wnn natural boyayyr kishin halisan aranta akan khaleel msmn ma lkcin da suka garata a gida da frenship dinsu

Halisa taji mugun haushi da bata sako ring din nan ta kuntatta ma meenal dashi ba sai kawai suka zuba mata ido ita da vick duk kinibininta basu ce uffan ba shemaun ce me amsta wuta wuta dariya dariya.

Shema tacewa meenal ciwon karya kikeyi wallh snn babu wani ciki ai anji labari kamfaninki is on the verge of collapses

meenal tace musu sam karyane media stereotypes ne. Ana so ne kawai abata mata suna haka ta dinga masu rantsuwa har idonta na kawo ruwa tana kumfar baki.

she denied everyting har ta nuna musu cewa kwanan nan mijinta zai bata kudi zata siya major share a wani estate company da zaa budeshi kwanan nan a lagos.

Meenal ta zauna tanata Famad zuzuta basirar me kamfanin da irin kudin da akace tana dashi she was seriously hyping arzkin halisa unknwghly

Halisa tay murmushi tasan akan sabon kamfaninta meenal take wann fafar, she knew dat is her new company da fadila tace zata siya musu a nigeria, snn itace wann matar da meenal take zuzutawa batare da tasani ba.

Meenal na cikin hiran kawai sukaji dariya ya subuce ma halisa kowa ya juyo ya kalle halisa sai tace musu bakomi kawai ta tuna wani abu.

Haba mana, tana fadin hakan,vicky ta samu daman sauya musu topic izuwa hirar sabon saurayin halisa. Altho takan y maganan kamr da hadiza da shema kawai takeyi dan meenal bakaraamin haushin take bata ba tatsani munafuki

nan Vicky tace musu ai taga sabon fiance din halisa a paris ya mugun haduwa, kai zach × 200 harma sun gaggaisa kuma weding bell wil soon ring.

nan Hadiza tafara nata itama tace ai taga gayen a mota ya wuce sunyi sabani bataga face nashi amma jikinta ya bata cewa ya hadu. Shema ta fara rawa tana kwaso shoki agaban meenal zaka rantse da Allah she is fine and she is aware of evrything dat is goin on amma kawai tsokana ce

Tay tunanin ko meenal din tana sane da komi batasan meenal sai yau tagane cewa kowa yasan sabon saurayin halisa itace kawai bata sani ba sosai abun yay mata ciwo aranta, sai yake kawai take tana biye ma shemau suna rawan tare.

vicky kuwa sai bakaken magana take cakkawa

Tace ma hadiza gayen yana da mata me tabon hankali amma da alama waje zasuyi da ita kafin su shigo da halisa ciki

shema ce kan gaba wajen ihu suka tattafa da vicky, shema tace ai koma wacece kishiyar halsy din sai sunyi waje da ita.

halisa nata kallon su tana dariya cos evrything is funny har da facial reaction din meenal.

Kaf dinsu daga kan hadiza vicky shema hirar khaleel suke duk da shema da hadiza basu san shi bane amma sai yabashi suke, suna cewa ya iya kiwo tunda har saida sukaga halsy ta sauya kamanni tay kyau ta dawo queen halsy inta..shema tace halsy kina shiga gidansa karki ji hudubar meenal, kedai kiyi ciki kinji, Dis one dat tun awaje soyayyar sa ya huraki kinyi kiba kina shiga gidansa kuma yaya kenan...

Vicky tace musu aima sai sunga irin yadda gayen yake mutuwar haukar son halisa wani irin describing soyayyr khaleel da halsy vicky takeyi zaka rantse labarin film take tsarawa.

Duk saida ta saka tsumin su ya tashi hadiza tafara tunanin shagalin bikin halisa meenal tafarajin zuciyarta na mata zafi, ko ta tsani ace halisa ta samu wani cigaba ne oho itade gatanan hirar na mata ciwo aranta bana kadan ba

She is almost suffocating da wann hirar ji takey kmar kirjinta zai yi aman wuta halisa kuma ta riga tasan da gayya vicky take kara fetur a hirar nan... Dan haka ta katse hirar da cewa she wll introduce him to them all inyadawo yanzu yay tafiya ne.

Daga nan aka bar hirar meenal dake jin zuciyarta na suya ita ce last din zuwa amma ita tafara cewa zata wuce gida

Taso halsy ta rakata sabida ta tuhumeta amma halisa taki zuwa harta gaji tabar asibitin da tashin hankli aranta najin har ace halisa zatay saurayi kyakkwa kuma me kudi amma ita bata san shi ba??..

Tana komawa gida taje ta kira mummynta ta dinga ranting tana zage zage cewa halisa tay sabon saurayi ita duk damuwarta shine ta san waye ne wnn saurayin da kowa yaji labarinsa amma ita bataji labari

kai tsaye Hajiya nadiya tace mata ta bincika koma hala mijinta ne meenal tace sam ai ance mata a paris suka hadu,
Snn ai khaleel ma yan university yake bibiya wanda zai cucesu ba irinsu halisa da suke da wayo ba haka dai ta kukkushe magananan.

Fannin hjya badiatu kuwa ranar tana isowa lagos dataga yadda hafsa take kulawa da kanta da kuma mahmud Abun sai ya kare burgeta sosai tuni tay fatali da baqin cikin shema'u data kwaso dazu.

Cikin zaman lafiya da girmamawa suke zaman su, itade sai yanxu taji ajikinta cewa danta mahmud yay aure.

Tun zuwanta zancen makomar schl dinta sukeyi duba da ciki ya shiga lamarin yanxu nn hajya binta tace musu koda college dinne abarta ta karasa a turkeyn inyaso sai tafara university anan lagos inyaso masters dinta sai suje tayishi a kasar waje zaifi musu sauki tana kusa da shi .

kwananta biyu a lagos ranar da yamma hafsa ta sha wanka ta saka wata Dry leshi peach lace daya mata kyau saboda yadda cikin ya saka ta dan kara cika gidan ya dau qamshi na turaren wuta ko ina neat, hajy badia na falon tana waya ita kuma tana gefenta tana cin apples sai ga sallamar mahmud
hafsat ta mike taje ta tarbeshi, ya gaishe da hajyarsa snn hafsa ta rakashi sama dan ta tayashi kimtsawa dan tun da safe ya fita bai dawo gidan ba sai yanxu.

Basufi minti talatin da haurawa ba hjya nakan kallon tv aka doka sallama ta amsa tare da lekawa taga ashe me gadine, gaishe ta yay snn yace mata wata mata ne tazo nemanta tun daga descrbtion din ta gane cewa mahaifiyar shemau
Ce nan Tace ace mata ta shigo.

After some minutes sai gasu nan, matar ta shigo tana ta kallon gidan ganin ko ina ya sauya mata, ita daya tazo tasha hijabinta, gata nitsuttyar mace da ita, gabaki daya kunya da nauyin zuciya ya hanata sakat.

kanta na kasa tay sallama suna hade ido da hjya badiatu ta danyi murmushi ta karaso ciki jin hjya badiatun ta tarbeta da murna lale marhaba kamar babu abunda yake faruwa.

Akasa ta zauna ita kadai tasan meyake mata ciwo aranta alkcin dan ji take kamar ta furta tace Allah ya tsine ma shemau albarka amma kuma hannunka bazai rube ka yanke ka zubar ba.

Mahaifin shema yay dan bincike har sun dan gaggano wasu abubuwa da shema tayi a kasar waje tun da suka san cewa tay saurayi da auren mahmud akanta jikinsu yay sanyi dan Bakaramin tashin hankli suke ciki yanxu ba.

Cikin mutuntawa da darajawa suka gaisa suka ma junansu jaje..hjy badiatu ta dinga bata hakuri akan tonon asirin shema datayi agabansu ranan acikin fushi.

Banda hawaye me sanyi babu abunda mahaifyar shema take zubarwa dan tama kasa daga idonta sama ta kalle matar

Nan hjya badiatu ta bar maganan ta kira hafsa a waya ta sauko dan su gaisa snn ta mata bayani kaarsuce ma an haince yarsu, hafsa na zuwa kuwa Ta je ta kawo ruwa da abun tabawa ta ajesu agaban mahaifyar shema snn ta mata gaisuwa cike da girmamawa snn ta tashi ta koma ciki.

Har sanda matar tasha ruwa snn hjya badiatu ta gaya mata cewa ai mahmud ma yay aure matarsa kenan wnn ita bata boye mata komi ba tace mata me aikinsu ce ma dacan wato Hafsa ya aura. Mamaki ya cika zucyar mum din shema ta kasa iya kai komi bakinta sabida tasan hafsa amma tsabar hafsa ta wanku taji kudi yasaka bata ko ganeta ba.

Babu irin hakurin da mum din shema bata basu tana magana tana zubda hawaye har sai kaji kamar kayi mata kuka kaima.

Tace ma hjy bdiatu sunyi iya bakin kokarinsu akan shema'u..kuma tun farko da sungane zata cutar da mahmud haka wllh ba basu amince anyi auren ba saboda iyama ta raine mahmud tasan wayeshi inhar ya iya sakar shemau toh tabbas akwai abunda shema tay wanda haryanxu bazai taba gaya musu ba.

Tana kuka tana jan Allah ya isa duk ta bawa hjya labarin abunda sukaji hjya badiatu ta tausaya mata sosai itama saida tay hawaye sosai ta dinga rarrashinta tana ce mata addua zasu hadu suyi mata kawai Allah ya shiryeta dan taso ace shema ta nitsu ta gyara halin ta kodan soyayyar da mahmud ya nuna mata arayuwa.
Chapter 238 · 0% Book details