← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 312

Sashe 136

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kukan kamar da gaske sai wani bori take masa na sakalci "Khaleel meye haka dan Allah so Ure just going to leave, kafana fa na buga..
Pls dont leave me like this, tun baka ci abincin bakenan za kafara juya min baya, toni nasan ma abincin zai zube ne?

Baice mata komi Ba ya fincike rigarsa data rike har saida taci da baki wani ihu tay tana birgima tana wayyo wayoo ta rike kafarta dama duk zaka dauka karyewa tayi dagske

Yana isowa daf mahaifytsa yace mama kiyi hakuri dan Allah toh muje ciki mana ki zauna

Ran Mahaifyarsan a mugun bace da meenal tace aa, ibrahim. I feel suffocated here ni Zanje gida na kawai. Asha ruwa lfya!

Tana ficewa sai ganan halisa na saukowa dan ihun da meenal din take wane anayankata.

Bayansu khaleel din kawai tagani ayayinda ya sake basket din kasa da gudu yabi bayan mahaifyarsa duk hanklinshi a tashe dantana ficewa ta fara zubda hawayen itama.

Itafa kukan tausayin danta kawai takeji daya kare da wann yar iskan yarinya marar imani da tarbiya, she feel like meenal is just here to ruin her son's life and destroy his family tun kafin ta isa motarta ta fashe da kuka me zafi har tana jan sheshheka.

Har mota yabiyota da gudu kamar ba azumi yake ba, da wani irin speed ya rike murfin motar da karfi jikinsa na ɓari muryansa harna rawa rawa yace mama dan Allah kiyi hakuri karki tafi kina fushi dani. Dan Allaah kizo muje ciki i swear babu wacce ta isa tasaki bar gidan nan kina zubda hawaye I'm so sorry pls pls Maa pls
Dan Allah kiyi hakuri i promise u i wil do wat eva it takes dan ga haka baisake faruwa ba. Pls come lets go in..ya riko hannunta yanajanta kamar zai mata kuka.

ta finceke hannunta anashi dan karfi snn ta rufe motar ta tay winding glass dan dede tana kallonshi da hawaye cikin idonta.

Koda ya kalleta ahakan saida yaji kansa yarasa dan kamar zuciyarsa zatay bindiga ta tarwatse haka ya dingajin zafi asaman kirjinshi.

Yanayinsa na tsantsan kunci da damuwa yasaka ta shanye nata hawayen da kyar snn tace ibrahim listen to me, kasan dai bazan taba yin fushi dakai ba cos i knw who you are, you are my son, very kind and obedient and i trust u with my life.

Kuma Tun kana karami nake adduar Allah ya baka mace ta gari, i just dont knw what went wrong in ur life daka auro mana wann yarinyar.

Nice zata dubi tsakar idona snn ta cemin nasaka maka maganin boka abincin dana kawo maka danna rabaku?
Toh sai kabata abincin ta karasa zubarwa snn ka gaya mata cewa Saidai in uwarta ce mushrika amma bani ba tana kammala fadin haka wani hawayenta ya sauko mata ta share.

Sunkuyar dakansa kasa yay hawaye sun ciko idonshi sosai nunfashin sa har na sama sama.

Dama saida kace min kar naxo gashi nazo inata nadaman zuwa in sha Allah bazan kara zuwa nan gidan ba, da sauri ya dago kai ya kallata hawaye cike taf a idonsa bakinsa na rawa rawa yace haba mama ive begged u dan Allah kiyi hakuri..cikin katse shi tace naji, son, u have to promise me dat zaka kawomin macen data dace dakai nan kusa, not until then bazan sake taka kafata agidanka ba.

Tana fadin hakan ta janye glass din motar ta tajashi a haknli tabarshi tsaye awajen hanklinsa a mugun mugun tashe.

Lumshe ido yay komi daya faru na memetuwa masa a brain nasa dan babu abunda yafi daga mai hankli kamar hawaye nan da mumynsa ta zubar.. wai ita meenal din nan wacece irin baqar ashana ce mai kona gari

Ya tuna twin sis dinsa maryam ko aurensan batazo ba bare tazo gidan sa, all bcos of meenal they have bcom distant hakama Aliyu sai yay shekara yana garin lagos amma baifi su hadu a asibiti ba.

His parents are even worst babansa dama can baiso auren ba infact bashi ya daura masa ba wani acikin yan uwansa ya nada waliyyi ya daura masa auren. Maman nashi dayake ji da ita yau gashi tace bazata sake taka kafarta gidan ba.

Share hawayen daya sauka masa yay ya shiga gidan normally kamar mutumin kirki yana isa yasamu dede halisa tana famar kkrin dagata akasa kenan sai zage zage take cikin kuka tana gayawa halisa karya da gaskiya tana cewa ai mahaifyar khaleel bata kaunar ta itace ta tureta kasa snn ta watsa mata abincin ajiki.

Suna cikin maganan taji an fincikota kamar tsinke
Kafin ta dago ta kalleshi kau kau kau taji sauka maruka uku uku akan fuskanta agigice ta fadi kasa tana ganin stars nan ta rusa ihu me gigitarwa tanamai birgima.

Har ya daga kafa zai ball da ita halisa ta rikeshi a mugun tsorace what is wrong with u zaka kasheta ne. Kwace kansa yay da karfi ya dubeta da bacin rai a muryasa yace stay out of this.

Yace ma meenal ke zanyi maganinki agidan nan mark my words..

A fusace ya dauki basket din mum din nasa ya haura sama yabarta akasa tana rusa ihu tana birgima dan marukan daya matan nan har fuskanta ya kumbura bakinta na fidda jini karshe halisa ne ta riketa takaita room babu kalar labarin karyan da batawa halisa akan rlashp din khaleel da iyayensa ba.

Cewa take sun tsaneta dana kawai so suke su rabasu, sune suke juya masa kansa akanta. Shikuma baya bin na kowa abunda ke ransa kawai shi yakeyi itama aigani yakeyi kamar alfarma ya mata da
ya aureta dan itace ta gansa tace tanasonshi ita tanace mai suyi aure
haka ta dinga kawo ababen tausayi tana fada

Halisa nasha baqar azaba kafin khaleel ya yadda ma zai aureni, sau tara ina kkrin kashe kaina akansa u were der ryt?? thats why he don't even knw my worth kikaga abunda familynsa suke mun ynxu memekon yabi bayana sai yana dukata kamar jaka?? Babana har ya mutu betaba dukana ba wayyo Allah na shiga uku.

Halisa ta gama jinta daga uhm sai uhm har suka rabu.

Bayan dare ya raba haka uwarta ta kara xugata akan taje ta sameshi ai itace da gaskiya akan me uwarsa zatana kawo mai abinci bayan tana nan haka ta zuzzugata.

Da asubahin fari halisa nakan bacci taji kururuwar meenal ya karade gidan.

Babu takalmi akafarta ta fito sa gudu nan ta sameta kasa tana mutsu mutsu wai khaleel ne ya zazzaneta da belt har abun tausayi jikinta duk yay rada rada da bulala aranar ma ko zama bata samu tay me kyau ba

kamar da wasa duka ya fara dawo ma meenal kamar Ruwan sha a hannunsa cos he is frustrated with her tafara ficemai aransa kwata kwata dan kuwa magana kadan zata gayamai inbe gamshe shi ba haka zai kamata ya nada mata shegen duka irinna sojoji haka zai fasa mata baki snn ya zazzageta yay ball da ita waje.

halisa ta rasa wani kalar shedan ne ya shigo musu gidan ya zauna ajikin khaleel. gashi bata isa ta tsoma baki a fadarsu ba nan da nan zai masifeta tass yace mata taje room dinta tay minding business dinta.

he bcom very rude, angry and hot kamar burning iron, Dan acikin kwanaki bakwai da meenal tay tare dasu kwata kwata sau uku ne kawai bata daku agidan ba. zai dake tan kuma Yace mata shi yana son haihuwa inhar tanason su shirya kawai ta dauki cikinshi sai suje gidansu tabawa maman shi hakuri.

tana mutuwar sonshi shiyasa ma har yake dukanta snn takoma masa da dare kobe nemeta ba amma gani take bazata iya yin ciki ma namiji ba koma wayeshi, Tun datagane take takensa akan haka arana na takwas din sai tay booking flight din asubah ana saura kwana biyu ayi sallah sassafe ta aje mai wasikar cewa ita bazata dauki cikinshi ahaka ba,sassafen kuwa ta gudu takoma wajen mummynta a south africa....................
Da sassafe khaleel ya farka bayan yay wanka yaxo gaban mirror yana taje suman kanshi anan ne yaga short wasikar da meenal din ta ajemai akan table yadauka ya karanta.

cikin sauke ajiyar zuciya wata Karamr muskilayar tsaki ta kufce daga ramin bakinsa ayayinda ya yaja drawrsa ya aje aciki yanamai furzan iska softly ta bakinsa alaman dake nuna hakan be ko darashi ba. She can go to end of the world for all he care dama yagaji da jibgarta ji yake aransa kamr ta isheshi agidan.

shide haryau aransa baiji dandanin danasanin dukanta da yay ba cos all he knw is duk macen datace zata saka uwarsa zubda hawaye agabanshi she wll definatly and surely face the animalistic side of him.

Zama yay a bakin gadonsa dat look soo unkept kwana biyu daya saba da yadda halisa take zuwa ta gyaramai gado tadan tsafce mai dakin ynxu ko yayi gyaran dakansa sai abun baya burgeshi.

Yana zama abakin gadon yafara saka wasu soft sneakers me tambarin jordan akafafunsa dede da kalar rigarsa fari me layi layin ja ajiki. Yana gama sawa ya dauki wayarsa da keys dinsa ya miƙe kai tsaye gaban mirror ya dau turarensa ya fetsa snn yabar gidan bashi da dawowa ba sai can dare kusan time din dayasan kowa yay bacci.

Haka gidan ya cigaba da kasancewa kamar wanda akayi musu mutuwa dan tun sadda ya fara jibgar matarsa Halisa ta dena shiga tsabgarsa kwata kwata atsakaninsu ko gaisuwa baya giftawa.

Cikin kwanaki takwas da meenal tay dasu koda tay abincinta ma iya cikinta dana mai gadi kawai takeyi sam bata aje saura bare kuma takai masa dakinsa.

Meenal kuma dama bata fiye kasancewa cikin hayyacinta ba dan duk sanda ta tsokaleshi ta daku a hannunsa toh a daki take kulle kanta dan taci tasha in peace dan tunda tazo gidan batay azumi ko daya ba.

Ranan daya gane hakan ma tasha mari amma ko ajikinta, itade iya abunda mummynta ke gaya mata shitake ayyana duk dama tana jibguwa, wani bin ihun datake yi agidan tanayi ne da gangan dan ta dada sakawa halisa ta tsanesa snn ta dawo tana bin bayanta kmr dacan.
Chapter 136 · 0% Book details