← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 312

Sashe 86

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kansa sosai ya daure sanin cewa basa wani jituwa da halisa infact kullum acikin kusheta takeyi tome zai kawota room din halisan yanata wondering hakan a mind dinsa, Yanadai kallonta harta ajiye cups din coffe din akan table snn ta ware hannayenta biyu ta hau fidda kwayar daya bayan daya har su hudu da wani irin speed yay capturing kan hannun nata dede kan kwayoyin
Da can yana dga tsayene ahujajan ya ja kujera ya nemi wajen zama, babu bata lokci yaga ta zuba kwayar guda uku acikin cup daya, saita saka daya acikin cup na biyu ta girgizasu sosai sai cup na ukun dake kurkusa da ita bata saka komi aciki ba.

Dannen dannensa yay within some minutes yafara scanning capture din daya dauka yana kammala scanning din ya nuna masa sunan kwayar kai tsaye da wasu relevant information akan aikin sa..

Yana karantawa shikansa baisan sanda ya rike bakinshi ba...

Dan Tsabar karfin kwayar sha'awar kwata kwata rabi ake sawa a drink asha ahakan ma me karamin brain baya shan irin wann,its moslty used by drug addicts who are addicted to maniacal sex sukan sha ne dan su kwana suna cin mace basu gaji ba, ko ire iren professional rapist, ko sex trafficker lords.

marmaza yay unmuting din voice din computer dan yaji metake cewa kuma me zatay da shi..

Yaganta tana murmishi harta dauki book din halisa tana dubawa..

Jim kadan saiga halisan ta dawo cikin dakin ita daya batare da meenal ba, hjy nadia naganin hakan tahau washe mata baki, ita kuwa halisa tunda ta shigo dakin kallonta takeyi dan sosai tsikar jikinta ya tashi duk dama bata kawo komi aranta ba.

Khaleel ya mike tsaye idonsa da hanklinsa nakan su at same time yana kulle butoran rigar sa na ciki, ji yay halisa tana cewa hajy banga AMINA a room dintan ba fa..

wani wuf hjy nadian tay tanamai dafa kafadun halisan da wani irn sigar makirci..its okay halako taje wajen mijinta na

..nan ta jawo hannun halisa tana cewa okay come i made this coffe for us, ga naki nan ta dauki wanda ta zuba one tablets ta mikawa halisan na dole, daga nan khaleel ya bar gaban computer ya fito cikin sauri sauri kirjinshi na bugawa dan ko aron takalmi bai saka akafafunsa ba ya nufo hanyar room din halisan agaggauce..

Meenal ta fito kenan da damin dollar a hannunta sai ta hangeshi yana tikan sauri abun ya daure mata kai musmmn ganin datay yay hanyar dakin halisa, aggauce ta sauko
Ta nufi room dinta da niyyar kai gulma da dumi dumi ma mummynta sai taga wayam babu ita..

Aje kudaden tay akan gado tafara kwalla mata kira mummy mummy can ta duro bayan gida waiko zata ganta ciki....

Daga nan kuma halisa na rike da cup din hjya nadiya sai famar lallabarta takeyi akan takai bakinta ta shanye.

Nasan kina jin yunwa bakici komi ba pls take it quick quick kafin duniya suce bantaba kulawa da ciwonki ba, drink it so that u can go and call her for me kinga aini surkuwace bazan je dakin suruki na ba, tunda suna can kuma ke patient dinsace pls go along with the other cup inkin buga kofarsu sun fito sai ki bashi coffe din ita kuma ki karawota nan kuzo tare..

Cike da rashin aminta da zancen nata halisa tajanye jikinta gefe snn tace hjy ki kirata awaya mana tazo nan se muyi maganan gaskiya nifa bazanje harcan ba am sorry but is not even proper kaje dakin miji da mata kanamai katsesu..

Cikin katseta tace Iyye kaji manyan yan bariki masu sanin laduban zaman aure..toh uban me za'a katse musu ehh ,komame zasuyi ai sun riga sunyishi jiya cikin dare ..ko kin medani bansan menakeyi bane?

Halisa ta turo baki gaba amma hajyaa ya za'ayi kice sai naje har dakin sa na bashi coffe dan kawai na kirata,..cant it wait..?

Da mummunan harde rai tace No it can't, inkuma ban isa na aikeki kije ba ne saiki fito fili ki gayamin mara kunya kawai...dama can nasan baki kallona a matsayin uwarki sam Bansan ma mesa ƴata meenal ta dauki son duniya ta dora akan macen da bata san darajar uwarta ba...

Kafin halisa tace zatace wni abu hjy nadia tay wuf ta wawusho hannunta da karfin tsiya tana cewa Naga alama ciwon nan naki yamaidake karamar yarinya ne sai anmiki dure...

cup din ta kama tana kkrin kai mata baki
Ran halisa ya baci tafara turewa hjy me haka dan Allah ko kyaleni nace bazan sha bako..sai cewa take saikin sha kuma dolene kije aikana ko atunaninki ban raineki bane agabana kika tashi yarinya bazaki fi karfina ba..hawayen bacin rai harya fara cikowa idanun halisa tana kkrin danne zucyarta karta ture hjya nadiya kasa ta karya mata kunkumi, kusan kokqwa suka shigayi ta damke bakinta sam taki budewa. gashi zuciyrta yaki sam ya kwanta da coffe din, kkrin cusa mata da hjya takey ya dada sata jin bata aminta da coffe din ba.

Ganin halisa ta turje taki shan coffe yasaka takai hannunta waists dinta zata mata cakulkuli tana kaiwa halisa ta firgita tay wani irin ihu daf zata juye mata abki kenan kwaf taji anbuge cup din kasa da wani irin karfin da saida mug din ya rabe biu. Noise din ya janyo hanklin meenal agurguje tayo dakin halisa cikin sassarfa.. hjy nadia kuwa na hade ido da khaleel tay saurin sake Halisa ta zube kasa tafara kuka.

Matsancin tsoron ganin idon khaleel Yasa hajya nadiya tsadarewa bakinta na rawa rawa ta kasa cewa komi sai rarrraba idanu data farayi..

Ko tambayarsu meyafaru beiyiba yay sauri zaiyo kan halisa dake tsugune tana kuka Da sauri hjy nadiyar ta turesa ta isa gaban halisa har jikinta na rawa tafara cewa toh yanxu ni menamiki anan kike kuka neman ki tara min mutane? Oh my god Are u seriously crying dan kin gansa? Hmmm khaleel kaga sakarci ko daga cewa tasha coffee dan kar ta zauna da yunwa shine zata kama dambe dani ganin idonka sai ta hau kuka...

Haushi ya kamashi baisan sanda yay mata magana cikin tsawa ba.

Yace bangane me kika mata ba i just saw u trying to force her to take that dirty coffe nida hannuna na bugeshi kasa.

Da wani irin bari barin rashin gaskiya cikin sauri ta mike tsaye ganin yadda ransa ya baci har idanunsa sunyi jaa..

Tafara barin baki subhanallah wani coffe wani coffe..lahaula wa la kuwwata.

Kusa daf da ita ya matso
Dan kar halisa taji ahnkli yana kallon cikin idonta yace coffen da kika zuba kwayar sha'awa aciki inkuma kin musanta i will call ur doyer to give u the oder cup agabana in oder to prove ur innocence

Kusan karkacewa baya tay kamar zata zube kasa matsancin mamakinsa da tsoron abunda yace din shine ya turnuke atake kafafunta suka fara rawa lar lar kar

Tun bata budi baki ba Saiganan meenal talba ta wantsalo cikin dakin a rikice ta kallesu sai taji ta rude gabaki daya ganin ran khaleel ya tafasa ya kone yakai matakin no control dama kuma danyen kaine dashi in ransa yana bace, ga nan kuma alamun Guiltness kaca kaca a yanayin mummynta ta rasa meye mum dinta tayi anan din daka turketa, halisa kuma na zube akasa tana kuka dan ta mugun tsanar amata cakulkuli .

Kusan a rude meenal tace "Mummy meyafaru..
Tun Kafin ta amsa tay wuf zatayo kan halisa
Khaleel yasha gabanta da wani irin miskiliyyar harara, sai cewa take cikin rawan murya halisa halisa Innalillahi halsy halisa..halisa halisa why are u crying? Is evrthing okay?

Fixgota gefe khaleel yay cikin bacin rai yace Dont fucking ask her ask your mum what she is doing here with that poisonous coffe.

Kusan a tsandare meenal ta juya ta kalle hajya nadia lkcin tay lumi lumi da ido kamar baqar munafuka tace mummy poison kuma??? A rude tace wai meyafaru ne.

Hajya nadiya Tana daga ido suka hade idanunsu waje guda da meenal take ta fashe da wani irin Gawurtaccen kukan makirci "yeee yeee yee ohni yau na shiga uku ni nadiya daga abun arziki anzo an maidashi na mugunta...yeee yee yee

Hanklin meenal yay mummunan tashi khaleel sai kallon mamaki dayakebin hjy nadiar dashi ganin yadda take neman sauya salon zancen gaba daya

Meenal ta rikota tana jijjigata tana cewa
"Mummy what now?

Wai dukkanku da halisan naga ƴaya na ne, coffe din nan dana hada miki shine nace bari itama na kawo mata tasha, yeee yee..yee..daga nan fa bansan meyafaru ba saiga nan mijinki ya shigo a fusace ya hau kaina da fada ya fara min tsawa kamar ban hairesa ba har yana cewa na zuba mata wani abu aciki. Inbanda renin wayo ta ina yaganni ina zuba mata abu yeee yeee yee
Allah wadar naka ya lalace..yeee yeee nayi nadaman zuwa na gidan nan tana kukan tana fyace hanci kmar dagaske

...duk son danake miki ya jawomin inbanda rashin sanin darajar uwa har yaushe mijinki zai daka min tsawa, akn wani dalili..tana fadin hakan ta mike a fusace ta fita tana kuka kamar an daketa

Meenal tabi bayanta da sauri suka fita..

Duk dama yana Allah Allah ya bi bayansu amma bai hanashi juyowa ya dube halisan ba. Har gabanta ya karaso ya dan tsuguna tare da mika hannu kamr zai tabaata sai kuma ya fasa, wani irin sanyaya voice nashi yay cikin taushi snn yace are u okay..? Shessheka take ja ahnkli ta dago kai ta kallesa ahnkli ta gyada masa kai hawaye na saika a idanunta, har ransa yakejin saukar hawayen nata dik dama baisan me zaice mata ba nan saiga uztaz ya shigo da bag din kayan da zata saka ahannunshi yanayin su ya bashi mamaki sosai yay musu sallama da sanyin murumya a hankli khaleel ya amsa shi snn ya mike tsaye yace masa pls make sure she get ready within 15 minute we r going to be late.

Yana fadin hakan ya fice a dakin agaggauce yabi bayansu meenal acan dakin meenal din ya same su suna cacar baki meenal ta birkice ta tutsiyeta akan ta gaya mata gaskiyar me taje yi a dakin halisan da har ta bari khaleel ya kamata..
Chapter 86 · 0% Book details