← Book details Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 312

Sashe 22

Cheaters Club Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mtss Ke shemau kibarni haka banason neman tsokanankin nan

Kasa kasa shemau tace "hahaha mrs doctor kenan toh shkn lets be serious now pls, duk wani abunda ake ciki inya gaya maki saiki gaya mana just make sure that halisa is being watched kinji ko??

Tace Toh ki kaita gidanki mana ki zauna tare da ita
Nifa bani da tabbaci akan komi, .Wai ko Baki ganin ko magana ma batamin ne, is asif she is angry with me ni wallh bansan menayi ma halisa ba kode na fadi wani abune daya bata mata rai acikin kwanakin nan da muke zuwa wajenta?.is like she doesnt even want me to come close to her

shema'u tace yeah kamar nima na lura da hakan. Amma ai kinsan batajin dadi maybe kawai batason ta dameki ne

Vicky tace yeah batason hanklinki ya tashi, maybe. Kuma kinsan dama halisa ta tsane allura amma kinga mijinkin nan kullum sai yay mata allura kamr sau uku arana...who knws shine silar haushin ku datakeji.

Shema'u tace probably

Meenal dai bata wani qamsu da zancen nasu ba amma dai tabarshi akan hakan.

ajiyar zuciya ta sauke tana shirin budan baki tay masu vicky sallama kenan wani caraffff idanunwanta ya sauka akan khaleel ayayinda yake kkrin cincibo halisa data riga tay bacci mai nauyi daga kan wheel chair din izuwa hannunsa zai dorata akan bayan seat na motarsa uztaz har ya rike masa kofa yana jiransa ya sakata aciki.

Idanunwanta nakansa harya tattaro halisan duka ajikinshi ya dauketa sama cakkkk kanta dake reto ya wani kwanto bisa kirjinsa

Meenal Batasan sanda ta kifta idanunta kusan sau goma akansu atakeba..

Subcontiously ba acikin hayyacinta ba tayo kansu ahargitse tace.."..excuse me ??? Khaleel what r u doing da wani irin sauri tabar gabansu shema'u ta karaso gabansa...

Da hargitsaten sauri Tace..."Khaleel Ina zaka kaita? Bai amsata ba har saida ya kammala aje halisan a seat din bayan yabi ya ja mata seat belt ya dora mata bisa kirjinta kfin nan yace gida mana meye matsalarki.

Baki bude take kallonsa Tarasa mema zatace fuskrta a kumbure Tace babu...so youre taking her home in ur car now?

Calmy yace yes,.. nagaji
Get into ur car, ko yau kawayenki zakibi...okay kiyi duk abunda kike so no problem ai dama kin saba ko.

Tsaye tay cak tana kallonsa tana huci taciki Haushin shi duk yabi ya cikata ganin duk maganan da yay nan baima juyo ya kalleta ba yana shiga motrsa ya kama hanyar gidansa abunsa uztaz na biye dashi acikin motarsu a baya.

Kallon bayan motocin sun ta dingai har suka bace ma ganinta.

Kafin ta dage idanunta akansun har kwayar idanun nata sun cike da ruwa.

Tana juyowa kuwa taci karo da idanunsu shema dukansu biyu sun kureta da kallo da alama suna jirane suji ma'anar wann borin kishi datake nunawa afili akan mijinta kamar yafi na uban kowa.

Zuwansu asibitin nan sosai yasaka Shema'u ta soma kallon meenal a matsayin makaryaciya

dan ayadda take nuna musu tafi karfin khaleel sai abunda tace sude sam basuga hakan ayananyinsu ba.

Inbanda uban ajin dayake ja mata kamar Lika mashi ita akayi, Da borin kishin hauka da suke ganin yana controlling inta akansa su basuga komi ayanyin meenal da mijinta ba.

Lkci guda dukansu su gane cewa meenal is overly posessive and obsessive akan mijinta sosai amma inta fito fili saita dinga cewa itace mijin shine matan.

Vicky tace meke faruwa meenal Lafya kuwa ???

Lumshe ido tay dan taji dama dama da vickyn ne ta tambayeta ba shemau ba.

Kwayar idanunta ta sauke kasa cikin borin kunya,cikij shan qamshi tace no bakomi, naga yadda ya fincike halisar ne kamar Baisan bata da lafya ba..he is just careless..ni bansan uban waye ma ya dorashi akan case din nan ba knwing well da cewa halisa da khaleel basu shiri da junansu ko kadan.

Cikin kyabe baki Shemau tace shine fa likitar and he is not complaining abt that or is he?

Tace nop. Amma ai..

Cikin katseta shema tace
Meenal u need to control ur self..mude kinsan bazaki mana karya bako, "kowa yasan khaleel din nan mijinki ne. The fact that basu shiri da halisa shud give u enuf peace of mind kidena wann borin kishin da kikeyi akansa haba meenal

Azafafe ta kaalle shemaun murynta kmr wanda zatay kuka tace

"Borin kishi? kishin uban wa...shemau karki bata min rai...dont insult me again ive had enuf of ur nonsense...mtchewww.
Ta kalle vicky tace vicky am out of here naga alaman cewa shemaun nan naki bata da hankli

A fusace tabarsu awajen
Taje ta shiga motar ta tajashi fuuuu ta fice acikin asibitin batare da ta jirasu ba.

Kallon junansu sukayi Suna hade ido da junan suka wani kwashe da dariya sosai suna masu tafawa.

Vicky tace Meenal is sooo dramatic sai kace mijin nata yafi na uban kowa..

Shemau tace abi ooo, ke kuwa kidube shi da kyau yafita kyau da haduwa nesa ba kusa ba ai dolenta dan ubanta tayi kishinsa, nide damuwata da ita shine wann tsinannen karya da jjiji dakai datake mana na cewa she dont care abt him while she surely do...tun zuwan mu asibitin nan wallh ba anitse take ba.

Cikin kyabe baki vicky tace uhmmm manyan mata kenan wanda basu son ace mazajensu suna control nasu...nide na waye na zaga duniya snn nayi karatun nan amma haryau banga wani abun burgewa acikin yin alfahari da cewa kai kafi karfin mijinka ba sabida akarshe kece zaki fadi kasa babu nauyi.

Namiji ai dan baban shi ne, wajensa fari cikin sa baki kirin. Buhun ƙaya, duk wanda ya daukeshi aka dolensa ya saukeshi.

Shemau tace Haka zalika duk macen datace namiji shine ubanta to tabbas zata mutu a marainiya.
Nide kingannin nan vicky inason ace in zamo inada mulki a idon namiji

Vicky tace dama kowacce mace sarauniya ce, but u knw what shema'u.. i stiil prefer ace ina da nawa power amma na zauna akarkashin ikon mijina, snn amemakon na zama abokiyar karawarsa a mulki gara na zama nice mai juya akalar mulkinsa
...dan mace bazata taɓa iya juya kan namiji da duniyarsa ba face harsai ta kasance a karkashin mulkinsa,to respct a man is to control him sede mata dayawa sunanan suna shan wahala sabida basu san ya ake bada irin wnn respect din ba,...
Sann daga zarar kin baude kin zamar dakanki dede dashi agidan toh ina tabbatar miki bazaki taɓa iya cin nasarta akansa ba.

Hmmm Ai babban goro sai magogin karfe.

..a king is just another word of servant of a queen, inhar tacika queen din toh da magananta za'a na juya masauratar rayuwarsa gabaki daya ba gidansa kadai ba .

Shema'u tay shiru tana murmushi tana kallon vicky...ba wani abu take tunawa ba face yadda itadin take juya rayuwar mahmud kamar kwallon tamaula. Ita din tamkar magogin karfen ne sede gani take kuma mahmd din baikai ace masa babbn goro ba bare ta tsaya gogeshi..

Dan ji take Ko ayau ta rabu da mahmud din tasan tay sa'ar namiji me mugun ji da ita arayuwarta amma bamai irin arzikin datake muradin zama aciki ba, dats why she have to leave him to go find a bigger kingdom to rule, inde har namiji kyakkwa me ilimi kmr mahmud zai iya bauta mata kamar hakan to lallaine ta cika cikakkyr sarauniya...

cikin wnn yanayin tabi ta lumshe idanunta ahankli imagining take shinya rayuwarta zai kasance inta samu namiji irin na hadiza anan gaba???

Ahaka hirarsu ya kare sukayi sallama vicky ta dau motarta ta koma gidanta shemau kuma ta kama hotel dake kusa da airport sabida tsoron kar mamynta ta faso gidanta gobe da safe ta kamata agidan tana bacci.

Wajajen karfe sha daya da minti ashirin dede su khaleel suka iso gidansu
Suna kammala parking meenal ta shigo cikin gidan itama ta kammala parking motarta agefen nasu.

tun bata sauko kasa ba taga khaleel ya sauko kasa cikin sauri ya bude kofar ya saka hannu ya dauko halisa ahnkli ayayinda uztaz ya tattaro masa kayan aikinsa snn suka wuce cikin gidan atare..

Dukkan abunda akeyi anan halisa batamasani ba saida har yakaita can sama cikin wani madaidacin daki acan masaukin bakin su na gida ya dorata akan gadon ya kwantar da ita akan lallausar pillow ahankli snn tafara motsawa ahankli ta bude gajiyayyun idanunta snn ta zubashi acikin nasa wani abuke fizgarsu aciki me mugun karfi kamar sihiri tsillin hawayenta ne yabi gangaro, rudani ya cikke kwayar idanuwnta da alaman mamakin ganinsa a cikinsu duk a tunaninta nan din gidantane batasan ma inda sukeba tukuna.

Hawayen nata da suka soma zubowa yabi da kallo tun daga cikin kwayar idanunta ya gangaro bisa kan kuncinta da doguwar hancinta mai tafe da karamin bakinta mai daukar hankli wanda bada wata manufa ba amma ya tsinci zucyarsa cikin wani yanayina tausayi da shaukin son yaga ya cireta acikin wann kuncin datake ciki

But he dont want the feeling to grow higher aransa, kawai bari yay akan aikinsa kawai zaiyi ya rabu da ita..can tsakar kansa ya tsinkayo nakasashen murynta tay maganane ahankli kuma acikin sanyin jiki sosai

saidai baikai da jin metace ba saiga uztaz nan ya karaso wajen da sauri jin kamr sunanshi ta kira....

Shikuma khaleel a tunaninsa duk zach din ne take tunawa msmn ma inyaga tana hawaye irin haka sosai...

kusan atare suka maida idanunsu kanta dan su tabbatar da metace ayayinda ta lumshe idonta wani gajiyayyen bacci mai nauyi ne ya wuce da ita.

Fuska ba yabo ba fallasa ya kalle uztaz saidai kunya yabi ya hanashi furta tambayar dayake son yay masa akan haka sai kawai ya basar

Uztaz dinne yay gyaran murya snn yace Doc are u sure zata amince ta zauna anan har ta warke?....

Daga dede nan meenal ta somajin conversation din nasu tabi ta mannu da kofar ta zuba kunnuwan ta ata waje.

Uztz yace snn kamar zuwa yaushe kake ganin zata zauna anan din dan nasan iya abubuwanda take bukata wanda zan kawo mata gobe.

Ayanayin nitsuwa dr khaleel yace in sha Allah bazata wani jima ba dan inada abubuwan yi but for now she is my primary assignment.

Kayi kkri ka kwantar mata da hanklinta ta amince ta zauna anan ciki kulawa na.
Chapter 22 · 0% Book details